Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-09-18@03:14:21 GMT

An Sami Ambaliyar Ruwa A Gonakin Shinkafa A Jihar Kwara

Published: 26th, January 2025 GMT

An Sami Ambaliyar Ruwa A Gonakin Shinkafa A Jihar Kwara

Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan ambaliyar rowa a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar,  ya ce  Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya  kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar.

A cewarsa ana sa ran kwamitin zai ziyarci yankunan da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike.

Sanarwar ta ce kwamitin zai kai ziyarar jaje ga Sarkin Shonga Dr. Haliru Yahyah da wadanda abin ya shafa a cikin al’umma.

Mambobin kwamitin da mataimakiyar shugaban ma’aikatan jihar, Gimbiya Bukola Babalola za ta jagoranta, sun hada da kwamishinan ayyukan gona, Mrs Oloruntoyosi Thomas, da kwamishinan muhalli, Hajiya Nafisat Musa Buge; da mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman; da  tsaro ga Gwamna,  Alhaji Muhyideen Aliu, da sauransu.

Ali Muhammad Rabi’u

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025

Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.

Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.

Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.

Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa