2025-05-01@13:50:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 346
«barkewar cutar»:
‘Yar takarar shugaban ƙasar Amurka da ta sha kaye a zaɓen da aka yi, ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, Kamala Harris ta zargi shugaba Donald Trump da tunzura abin da ta kira taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar. Ms Harris ta kuma zargi Mr Trump da jefa ƙasar cikin ruɗani da salon mulkin da ke jefa tsoro a zukatan jama’a. Ta ce abin da suka kasa ganewa shi ne, tsoratarwa ba ita ce kaɗai hanyar magance matsala ba, ƙwarin gwiwa ake buƙata. Tattalin arziƙin Amurka ya samu koma baya a rububin farko na wannan shekarar, idan aka kwatanta da bunƙasar shi a shekaru hudu na mulkin shugaba Joe Biden.

Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Darajar cinikayyar ba da hidima ta kasar Sin ta karu sosai, inda ta kai yuan triliyan 1.97 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 270 a rubu’in farko na bana, karuwar kashi 8.7 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Darajar jimillar hidimar fice ta kai yuan biliyan 835.15, karuwar kashi 12.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, yayin da darajar hidimar shige ta kai yuan triliyan 1.139, wanda ta nuna karuwar kashi 6.2 cikin dari. Hidimomin tafiye-tafiye sun nuna karuwa mafi sauri na kashi 21.8 cikin dari. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“ Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman...
An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai. A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita. Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu....
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar. EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan...
Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar. Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.” Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita...
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya. A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance...
Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Sai dai asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto. Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce “abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda.” Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar. Har yanzu dai ba a san abin...
A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Nijeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato. Burin wadannan mata ta karu ne sakamakon yadda farin ciki nau’i uku ya lullube Malama Bela’u Sabo da iyalanta, bayan da ta haifi ’yan uku a garin Kaurar Yabo da ke Karamar Hukumar Yabo ta jihar. Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi A yayin da mai jego da angon karni da ’yan uwa suke tsaka da murna, wannan karuwar haihuwa ta kara jawo musu sha-tara ta arziki, inda matar gwamnan...
Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso...
Jiragen yakin HKI sun kai hari a yankin Hangara dake unguwar “Dhahiya” a cikin birnin Beirut. Yankin da jiragen yakin na ‘yan sahayoniya su ka kai wa harin, yana cike da mutane da kuma makarantu biyu. Jiragen yakin na HKI sun harba makamai masu linzami 3, da hakan ya haddasa tashin gobara. A sanadiyyar wannan harin, an sami shahidi daya,yayin da wasu da dama su ka jikkata. A ranar 1 ga watan Aprilu ma dai sojojin HKI sun kai wani harin a unguwar Dhahiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 4 da kuma jikkata wasu da dama. Tun bayan tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Aprilu 2025, HKI ta keta wutar yakin fiye da 2000.

An Fara Gudanar Da Zaman Taron Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Tsakanin Iran Da Kasashen Nahiyar Afirka
An fara gudanar da zaman taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da kasashen nahiyar Afirka karo na uku A safiyar yau Lahadi ne aka bude zaman taron karo na uku kan harkokin tattalin arziki tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Afirka a birnin Tehran, tare da halartar shugaban kasar Iran da mataimakinsa na farko da wasu tawagar jami’ai da ‘yan kasuwa daga nahiyar Afirka. Kasar Iran tana gudanar da wannan biki ne tare da jami’an kungiyar Tarayyar Afirka, da manyan jami’ai, ministocin tattalin arziki da cinikayya, da shugabannin kungiyoyin kasuwanci, ‘yan kasuwa, masu fafutukar tattalin arziki, shugabannin bankuna, kamfanonin inshora, da na’urorin samar da kayayyaki, da daraktocin manyan kamfanoni da na kasa da kasa daga kasashen Afirka. Taron...
Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki. Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da shakatawa da wuraren raya al’adu da filayen jiragen sama da otel-otel da tashoshin tafiye-tafiye. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana kara samun karin ta’aziyya da kuma tallafa daga kasashen waje bayan fashewar da ta auku a tasahr jiragen ruwa na Dr Rajai a Bandar Abbasa. Tashar talabijin ta Press Tv ta nakalto ministan harkokin cikin gida Eskandar mumunina yana fadar haka, yana kuma cewa ya zuwa yanzu, mutane 14 aka tabbatar da mutuwarsu a yaynda wasu a yayinda wasu tsakanin 700-750 suka ji rauni. Tankar dakon mai ce ta yi binda a cikin tashar jiragen ruwan, a jiya, ammam ba’a san musabbin fashewar ba hanyanzu. Wuta ta kona tankar ta kuma tsallaka zuwa wasu kayaki kusa da wurin. Sannan bindigan da tankar ta tayi ya watsa wutar zuwa wasu wurare daga nesa, ya fasa gilashan mutocin da suke gewaue,...
Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu. A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu. Fashewar ta yi karfi...

Tashin Gobara A Tashar Jirgi Ruwa Na Shahid Raja’i Da Ke Kudancin Iran Ya Lashe Rayukan Mutane A Kudancin Iran
Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu. A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu. Fashewar ta yi karfi...
Iyalan wata dattijuwa da suka nema suka rasa sun shiga fargaba bayan gano gawarta a cikin wani maciji. Lamarin na zuwa ne bayan kumburin ciki ya bayyana sosai a kasurgumin maciji — kafin dangin tsohuwar su gano cewa maciji ya haɗiye kakarsu a cikinsa. Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja Iyalan matar da ta ɓace sun bi sawun macijin zuwa wani mai yawan ciyayi a kudancin Sulawesi na kasar Indonesia. ’Yan yankin sun tsorata matuka lokacin da suka ga maciji mai tsawon kafa 26 ya yi nauyi da wani babban kumburi a cikinsa. A lokacin da suka farka cikin macijin, sun gano gawar matar...
Wani matashi mai shekaru 30 ya kashe kansa bisa rahotanni bayan rasuwar ƙaramar matarsa a ƙauyen Ikumi da ke Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja. Majiyoyi sun bayyana cewa magidancin mai mata biyu ya sha fama da matsalolin tunani da na zuciya tun bayan rasuwar matarsa ta biyu a watan Maris na wannan shekara. Sun ƙara cewa ya kasance yana yawan bayyana cewa ba zai iya samun kwanciyar hankali ba tare da marigayiyar ba. Shaidu sun bayyana cewa ya yi amfani da bindigarsa ta toka wacce yake farauta da ita wajen harbe kansa har lahira a gonarsa. Wata majiya ta ce ya bar matarshi ta farko da manya da kuma yara biyu. Kakakin ’yan sanda a Jihar Nijar, SP Wasiu...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa game da sake haduwa da ƙara ƙarfin mayakan Boko Haram a yankunan Tumbus na Tafkin Chadi da kuma tsaunukan Mandara a cikin dajin Sambisa. Yayin da yake jawabi ga Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, da manyan hafsoshin soji a Maiduguri, Gwamna Zulum ya yaba da ƙoƙarin sojojin Najeriya wajen yaƙi da ta’addancin Boko Haram a Borno da ma yankin Arewa maso Gabas, amma ya nuna wani abin damuwa da ya faru kwanan nan a ayyukansu. Ya bayyana cewa bayan an yi ayyukan soja an gama, sai sojojin su janye, sai kuma ’yan Boko Haram da ISWAP su sake dawowa su karɓe waɗannan yankunan da aka ƙwato a baya. Babban abin da...
“Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho. Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta. Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta. Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen...
Bugu da kari, game da amincewar da gwamnatin shugaba Trump ta yi da aikin hako ma’adinan karkashin teku, Guo Jiakun ya ce ba wata kasa dake da ikon karya dokokin kasa da kasa a wannan fanni, ta yadda za ta iya keta dokokin bincike, da bunkasa ayyukan hako ma’adinan karkashin teku ba bisa ka’ida ba, domin kuwa hakan zai haifar da illa ga moriyar daukacin al’ummun kasa da kasa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar. Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar. A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai. Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu. Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa...

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana. Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati. Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar. Haka kuma, Ministan...
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC “Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi. Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa. Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni a kwanan baya kan aikin inganta hadin gwiwar jama’a da sojan kasar, inda ya ce, nagartacciyar hulda mai karfi tsakanin jama’a da soja fifiko ne da bangaren siyasar Sin ya jima da shi. Ya ce ya kamata a tsaya tsayin daka kan jagorancin ra’ayin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani, kuma a nace ga jagorantar jam’iyyar JKS a dukkanin fannoni, da zurfafa yin kwaskwarima, da kirkire-kirkire, da ma kyautata tsare-tsare da manufofi, har da raya aikin inganta hadin gwiwar jama’a da soja. An kira taron rada sunan birane ko gundumomi dake taka rawar gani a wannan bangare a yau Laraba a nan birnin Beijing. Inda...
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Sanarwar ficewar ta su ta zo ne bayan kammala taron sa’o’i shida da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da Sanata daga jam’iyyar, James Manager, ya bayyana. “Duk wani dan PDP na jihar har da gwamna, da tsohon gwamna Okowa, da shugaban majalisa, da shugaban jam’iyyar, da duk ciyamomin ƙanannan hukumomi...
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.” A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A safiyar jiya Litinin ce Fafaroma Francis mai shekaru 88 ya koma ga mahaliccinsa, bayan da ya yi fama da mutuwar ɓarin jiki da kuma bugun zuciya, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar. Shugaban na mabiya ɗariƙar Katolika ya shafe makonni 5 a asibiti a farkon wannan shekara, sakamakon harbuwa da cutar limoniya, amma ya koma gida a watan da ya wuce, bayan da ya samun sauƙi. An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana Fadar Vatican ta tabbatar da cewar a ranar Asabar ne za a gudanar da jana’izar Fafaroma Francis a majami’ar St. Peter’s Basilica. A safiyar Talatar nan ce dai fadar Vatican ta saki hoton Fafaroma...
An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tube bisa gado a cikin dakinsa a yakin Alo da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi. An tsinci gawara masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata. Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon rashin ganin matashin ya bude kofarsa da safe kamar yadda ya saba. Daga nan ne ya sanar da dan uwan matashin da kuma ’yan sanda, inda suka so aka balla kofar dakin, inda aka samu masoyan sun kwanta dama. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mika ta’aziyya game da rasuwar shugaban ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis. A wani sako da ya aike a jiya Litinin, Pezeshkian ya ce Paparoma Francis a matsayinsa na shugaban darikar Roman Katolika ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yada koyarwar Yesu Almasihu. Shugaban ya ce Paparoma ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya a duniya, da yekuwar samar da adalci, da ‘yanci, da mu’amala da tsaro a tsakanin addinai. Daya daga cikin shi ne bayyanannen matsayinsa na yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kiran da ya yi na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa mata da kananan yara Falasdinawan...
Kwamitin kasa da kasa kan yaki da fari a yankin Sahel (CILSS) ya yi wani gargadi na musamman kan sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin Sahel, wanda ke da hadarin yin illa nan gaba. Shafin yanar gizo na CILSS ya bayar da rahoton cewa, “Kwananan kwararru kan yaki da fari sun fitar da sanarwar sake bullar farar kwarin dango a kasashen Sahel da dama.” CILSS ta yi gargadin cewa “, wannan na iya haddasa matsala sosai a lokacin noma a yankin da ya riga ya kasance mai rauni’’. Yayin da ake fuskantar wannan barazana, CILSS na ganin cewa, ya zama wajibi a ba da goyon baya mai dorewa ga kasashendake sahun gaba wajen fuskantar irin wannan matsala na yankin Sahel,...
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya, FIGC, ta sanar da jingine wasannin gasar gasannin Serie A, B, da C, saboda alhinin rasuwar shugaban ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis. Shugaban hukumar FIGC, Gabriel Gravina ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa ta Italiya tana taya jimami ga miliyoyin al’umma kan rasuwar Mai Alfarma Fafaroma Francis. Ƙungiyoyin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Juventus, Lazio, Parma Calcio, Cagliari, Fiorentina, Genoa, Torino, Udinese. A safiyar Litinin 21 ga Afrilu ne Fadar Cocin Katolika da ke Vatican City ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88, wanda ke shugabantar Cocin, kuma shugaban birnin Vatican City. Miliyoyin mutane a Italiya da kuma faɗin duniya sun shiga alhini saboda rasuwar malamin adinin. Wannan ya sa aka ɗauki matakin...
Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe. A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu. A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin...
Fadan Vatican ta mabiya darikar Katolika ta sanar da mutuwar Paparoma Francis a yau Fadar Vatican ta bayyana a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo a yau Litinin cewa: Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika dan Latin Amurka na farko, ya kawo karshen mulkin da ya yi fama da rikici, rarrabuwar kawuna, da tashin hankali a yayin da yake kokarin kawo sauyi a cibiyoyin majami’u. Cardinal Kevin Farrell ta hanyar gidan talabijin na Fadar Vatican ya shelanta cewa; Ya ku ‘yan uwa maza da mata masu daraja, tare da bakin ciki da alhini, ina sanar da mutuwar Fafaroma Francis”, da karfe 7:35 na safiyar yau (agogon gida), yana mai jaddada cewa: Francis, ya koma gidan mahaifinsa.” Fafaroma Francis yana da shekaru...
Sojojin mamayar HKI sun fara aiwatar da wani sabon kisa ta hanyar amfani da sabon salo akan Falasdinawa. Kai kace tsawon watanni 18 da su ka dauka suna amfani da makamai mabanbanta wajen kashe mutanen Gaza, bai isha sun cimma manufofin da su ka Sanya a gaba. Sabon salon kisa wanda ya yi kama da “Kalankuwar Masu Cin naman mutum” bayan sun soya shi, shi ne abinda yake faruwa. Isra’ila ta kai hari da jirgin yakin maras matuki na kunar bakin wake akan sansanonin ‘yan hijira da su ka yi dandazo a wuri daya. Iyalan Abur-Rus ne wannan jirgin kunar bakin waken ya fada a kansu ya kashe da dama daga cikinsu ta hanyar kona su da ransu. Mutane 20...
Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan ta’addar ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a Ƙaramar Hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno. JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi Majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar. Wannan aikin ta’addanci ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran al’ummomin yankin,...
Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9. Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar...
· Amfani da intanet cikin tsaro: Wayar da kai tana koya maka yadda za ka yi amfani da wayar salula, kwamfuta, da sauran na’urori cikin kwarewa da tsaro. · Sanin sirrinka da darajarsa: Mutum zai fi kulawa da bayanansa na sirri da yadda za su iya amfani da su wajen cutar da shi idan ya samu ilimi. Abubuwan Da Ya Kamata Ka Kula Da Su 1. Kada ka bude kowanne sako ko imel da bai fito daga tushe da ka yarda da shi ba. 2. Kar ka rika danna kowanne link da ba ka tabbatar da amincinsa ba. 3. Rika sabunta (update) wayarka ko kwamfutarka domin gyara kura-kurai na tsaro. 4. Amfani da kalmar sirri (password) mai karfi da bambanta...
Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya. Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen ci gaban kasa. Alhaji Ibrahim Haruna ya ce, masarautun ba wai kawai suna zama uba ga al’umma ba ne, kawai har ila yau suna bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Ya bayyana cewa goyon baya da gudunmawar da Alhaji Aliyu Dauda ke bayarwa ga masarautun gargajiya, musamman a Arewacin Najeriya, ne ya sa aka zabesa domin karbar wannan gagarumar...
Bisa labarin da babban bankin jama’ar kasar Sin ya fitar, ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2025, jimillar cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje 1,160 ne suka shiga kasuwar hada-hadar lamuni ta kasar Sin, wadanda suka hada da cibiyoyin hada-hadar kudi masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasuwanci a kasashe da yankuna fiye da 70, wadanda ke rike da takardun lamuni da yawansu ya kai yuan tiriliyan 4.5, adadin da ya karu da sama da yuan biliyan 270 daga karshen shekarar 2024. Kazalika, jimillar darajar kasuwar lamuni ta kasar Sin ta kai yuan tiriliyan 183, wanda ke matsayi na biyu a duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
An tsinci gawar wani tsoho mai suna Haruna Abdullahi mai shekara 75 daga garin Gumel na Jihar Jigawa a ƙofar babbar kasuwar Kure Ultra Modern Market da ke Minna a Jihar Neja. Babu wanda zai iya cewa ga musabbabin mutuwarsa, amma ’yan kasuwa sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawarsa da safiyar ranar Juma’a a babbar ƙofar shiga kasuwar. Ya kashe masoyin tsohuwar matarsa bayan sakinta a Neja PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Kakakin rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin. Ya ce, “A yau Juma’a 18/4/2025 da sanyin safiya, an tsinci gawar wani wanda aka bayyana sunansa da Haruna Abdullahi mai kimanin shekara 75...
Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar. Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa gidan Buhari sa’o’i kadan bayan tawagar Atiku, wanda ya kara tsananta siyasa. Ya kuma ba da tabbaci ga ra’ayin cewa shugabannin jam’iyyar APC sun damu da siyasar tsohon shugaban kasar. Masu lura da al’amura siyasa sun bayyana cewa kalaman da Ganduje ya yi bayan ganawar, ya tabbatar da cewa APC na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa Buhari ya kasance tare da jam’iyya...
Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura. Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi. PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta....
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za su iya zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin, yana mai jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi wani lamari ne da ake bukata don samun zaman lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ya yi da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman da tawagarsa a birnin Tehran, bayan da ministan na Saudiyya ya isa babban birnin kasar Iran domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin da alakar kasashen biyu. Shugaban na Iran ya jaddada zurfafa dangantakar addini da al’adu da tarihi a tsakanin kasashen musulmi, yana mai jaddada wajabcin karfafa hadin...
Wasu ’yan ta’addan da ake zargin suna da alaƙa da ISWAP sun tayar da wata na’ura mai fashewa a kan gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa da tsakar daren wayewar garin ranar Talata. Kamar yadda majiyar Zagazola Makama ke cewar, wannan harin na bam da waɗannan ‘yan ta’addan suka jefa ya lalata gadar ta Mandafuna gaba ɗayanta. Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna A cewar majiyar, wannan lalacewar gadar a halin da ake ciki ya kai ga katsewar hanyar da ke tsakanin ƙauyen Mandafuma da garin Biu wadda ita ce hanyar da ta haɗa garin Biu da Maiduguri Jihar Borno. Kamar...
Ban da wannan kuma, alkaluman PMI wato masu bayyana yanayin sayayya da ake ciki ta fuskar sana’o’in samar da kayayyaki a watan Maris ya samu karuwa cikin watanni 2 a jere, matakin da ya bayyana bukatun kasuwanni na kara samun kyautatuwa. Har ila yau, Sin ta kafa cikakken tsarin sana’o’i, da ingantattun manufofin dake da nasaba da su bayan kokarin da take yi a shekaru da dama, matakin da ya aza tubali mai inganci ga bunkasuwar tattalin arzikinta. Bayan ga batun dorewa, Sin ta bayyana kuzarinta mai karfi a fannin samun bunkasuwa. A cikin shekarun baya-bayan nan, Sin ta sauya salon tattalin arzikinta daga matakin dogaro da zuba jari, da fitar da kaya waje, zuwa habaka bukatun cikin gida...
Mai Magana da yawun kakakin babban magatakardar MDD Steven Dujarric ya nuna damuwa akan sanar da kafa wata gwamnati ta daban da shugaban rundunar daukin gaggawa Hamidati Duklu ya yi a shekaran jiya Laraba. Shugaban rundunar kai daukin gaggawar ta Sudan wanda yake fada da sojojin kasar ya shelanta kafa sabuwar gwamnati wacce ya ce za ta kasance ta zaman lafiya da hadin kai ce. Hamidati wanda ya gabatar da jawabi a lokacin da ake tunawa da zagayowar cikar shekaru 3 da fara yaki a kasar ta Sudan, ya kuma ce; A halin yanzu suna Shirin buga kudaden Sudan na daban, da kuma samar da wasu muhimman takardu na aikin gwamnati. Wannan sanarwar daga shugaban rundunar kai daukin gaggawar ta...
Wato na farko, dogaro da kai a bangare makamashi, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta kafa wani tsarin tattalin arziki dake amfanar da dukkan kasashen Asiya da Afirka, sun kuma kara karfin kafa tsare-tsaren samar da kayayyaki na mabambantan bangarori a shiyyar ta hanyar kara tuntuba, da dunkulewar manyan ababen more rayuwa, da yin musayar fasahohi, wanda hakan ya sa kasashen ba sa dogaro da sana’ar fitar da makamashi kawai, matakin da ya kara musu kwarin gwiwar samun bunkasuwa da kansu. Na biyu, samun jari da kansu. Sabon bankin raya mambobin BRICS, da bankin zuba jari na Asiya da dai sauran hukumomi, sun baiwa kasashe masu tasowa wata hanyar samun jari na daban ban da kasashen yamma. Ya...
Wadannan shawarwari guda 6 sun samar da makoma mai haske ga zamamintar da al’ummun kasashen biyu da yawansu ya wuce biliyan 1.5, da ma kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya. Hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren ciniki ingantaccen karfi ne na ingiza huldarsu. A cikin shekaru 20 a jere da suka gabata, Sin ta kai matsayin abokiyar ciniki mafi girma ga Vietnam, kuma Vietnam ta zama abokiyar ciniki mafiya girma ga kasar Sin a mambobin kungiyar ASEAN. Yayin ziyarar aikinsa a wannan karo, Xi Jinping da Tô Lâm sun halarci bikin kaddamar da tsarin hadin gwiwar kasashen biyu wajen kafa layin dogo tsakaninsu. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa har 45 tsakaninsu, ciki...
Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar. Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna. Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu...
Kasar Sin ta kuma nuna aniyarta ta lale marhabin ga shigar da karin kayan amfanin gona masu inganci na Malaysiya zuwa katafariyar kasuwarta inda ta kuma nemi kasar ta Malaysiya ta kara bai wa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a kasar. Kasar Malaysiya ta san irin alheran da kamfanonin Sin suke ci gaba da kawo mata wajen raya tattalin arziki da ci gaban masana’antunta. Wannan ya sa Sultan Ibrahim ya bayyana cewa, Malaysiya tana dora fifiko sosai a kan zumuncinta da kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin aiki tare domin samun nasara ga kowane bangare, tare da kara matsa kaimi ga gina al’umma mai makoma ta bai-daya a karkashin ingantattun manyan tsare-tsare kuma a duk wani...
Gwamna Uba Sani ya amince da sabon tsarin biyan diyya ta hanyar amfani da fasahar zamani ga Hukumar Kula da Bayanan Filaye ta Kaduna (KADGIS), da nufin dakile almundahana a harkokin biyan diyya na filaye a fadin jihar. Daraktan Hukumar KADGIS Dr. Bashir Garba Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa (NUJ), rashen Rediyon Najeriya Kaduna, a ofishinsa da ke Kaduna. Dr. Bashir Garba Ibrahim ya bayyana cewa wannan sabuwar manhaja za ta rika adana bayanan masu asalin filayen da za a biya diyya, da suka hada da daukar hoton ‘yan yatsun da lambar katinsu na dan kasa NIN, domin hana masu zamba karbar diyya akan filayen da ba nasu...
Ya jaddada cewa dole ne a gyara jam’iyyar PDP kafin a fara tunanin neman wani muƙami. Ya ƙara da cewa ko da siyasarsa ta tsaya a matsayin gwamna, zai kasance cikin farin ciki da gamsuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jaridar “Yadiot-Ahranot” ta rubuta cewa, jami’an Amurka sun sanar da sojojin Isra’ila a lokacin da za ta janye sojojinta daga kasar Syria. Jaridar ta ce, jami’an tsaron kasar ta Amurka sun fada wa sojojin Isra’ila cewa, janye sojojin nata zai fara ne nan da watanni biyu masu zuwa. Rahoton jaridar ta ‘yan sahayoniya ya ce, Shirin janyewar sojojin na Amurka bai zama abin mamaki ba,domin tun farkon rantsar da Donald Trump ne ya bayyana aniyarsa na janye sojojin kasar daga Syria. HKI tana jin cewa, idan har Amurkan ta janye daga kasar Syria, to Turkiya za ta kara azamarta ta shimfida ikonta a cikin kasar. Tun a Zangon shugabancinsa na farko ne dai Donald Trump ya bayyana cewa Idan kungiyar...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da sharudan sakin dukkan fursunonin Isra’ila da take tsare da su Wani jami’in Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: Kungiyar a shirye take ta sako daukacin fursunonin Isra’ila domin tsagaita bude wuta da ficewa daga Gaza, kamar yadda wani rahoto da tashar talabijin ta Alkahira ta fitar. Jami’in na kungiyar Hamas ya kara da cewa: A ranar litinin din nan ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma yin watsi da alkawurran da ta dauka, yana mai cewa kungiyar Hamas ta tabbatar wa masu shiga tsakani da “bukatar bayar da lamuni don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar.” Yana mai bayyana cewa,...

Firaministan Malaysia: Xi Jinping Babban Jagora Ne Mai Matukar Mayar Da Hankali Kan Abubuwan Dake Shafar Zaman Rayuwar Jama’a
Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu. Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan Sinawa. A ganinsa, Xi Jinping babban jagora ne dake matukar mai da hankali kan abubuwan dake shafar zaman rayuwar jama’a. Ya ce duniya na bukatar musanyar al’adu sosai don kawar da bambancin ra’ayi, ta yadda za a tabbatar da wadata cikin hadin gwiwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...

Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa: Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake farfaɗowar ƙungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16971864-dalilan-farfa-owar-boko-haram-a-jihar-borno.mp3?download=true
Gwamnatin Jihar Jigawa ta siyo tan tan guda 360 domin tallafawa manoma don ci gaba da habbaka harkokin noma a Jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da shirin noman rani na shinkafa a kauyen Jura dake Karamar Hukumar Auyo. Ya yi bayanin cewar, gwamnatin ta kuma siyo injin girbin shinkafa guda 70 da sauran kayayyakin noma domin tallafawa manoman shinkafa. A don haka, Gwamna Umar Namadi ya yi gargadin hukunta duk wanda aka samu ya karkatar da kayayyakin aikin gona da gwamnatin ta samarwa manoman jihar. Yana mai cewar, fiye da manoma dubu hamsin da biyar ne za su amfana da shirin, wanda wani bangare ne na kokarin gwamnati na bunkasa aikin gona da...
Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas. “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20. “Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa. “Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma. “Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta...
Nan da wata biyu Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 za ta cika shekara biyu, rabin wa’adinta, da fara aiki a matsayin ɓangaren da ke kafa dokoki da kuma saita ɓangaren zartarwa domin yin daidai a bisa tsarin dimokuradiyyar Nijeriya. ’Yan kasar da dama na ganin wannan muhimmin ɓangare ya zama dan amshin shata ga ɓangaren zantarwa na Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu. Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri Hakan dai ya ci karo da yadda aka yi hasashe a lokacin da aka kaddamar da ’yan majalisar su sama da 460 domin fara aikinsu na wakilcin ’yan Nijeriya sama da miliyan 230 a...
Rahotanni da suke fitowa daga Nigeria sun ce, a kalla mutane 7 su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama su ka jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa masu karfi akan hanyar Damboa-Zuwa Maiduguri. Rahotannin sun ce abubuwan su fashe ne dai a lokacin da wasu ayarin motoci da suke wucewa ta hanyar tare da rakiyar sojoji a jiya Asabar da hakan ya haddasa asarar rayuka da kuma jikka. Hanyar Damboa zuwa Maiduguri tana zuwa kananan hukumomi da dama a kudancin Jahar ta Borno, a lokaci daya kuma yanki ne da ya yi kaurin suna a matsayin matsugunin ‘yan Bokoharam. An dade da rufe hanyar saboda matsalar tsaro, amma gwamnatin Babagana zulum ta sake bude ta, da kuma dawo da...
Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
Haka zalika, Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa; jami’an tsaro na ci gaba da mayar da hankali wajen cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Bello Turji. Sannan, ya yi watsi da ikrarin da sojoji suka yi na cewa; sun dakile hare-haren makiyaya da ‘yan ta’adda da kuma barayin shanu da sauran makamantansu. Da yake yin jawabi game da kyautata wa sojojin da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin yin watsi da sojojin da suka samu raunuka. Ya ce, “To, a iya sanina dangane da abin da hukumar sojoji ke yi, sojojinmu na samun isasshiyar kulawa, kuma kai dan jarida ne, da ka lura da lokacin hutun Sallah, za ka ga yadda babban hafsan soji da hafsan hafsoshin sojin...
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda wajen kare karfin tattalin arziki da cinikayya. Kwanan baya, manyan jami’an kasar Sin sun yi shawarwari da takwarorinsu na kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) da na kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda suka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga waje. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ba kamar kayayyakin manyan kamfanoni irin su Ajinomoto, Bedan wadanda aka zuba su a cikin kwali, ana sayar da su cikin lafiyayyen mazubi kuma NAFDAC ta amince da su ba, wadannan danyun kaya ne da ba su da wata alama. Babban abin ban tsoro shi ne ba za a iya gano masana’antunsu don bincikar sahihancinsu ba. Da alama a yankin Arewacin Nijeriya din ake yin su amma an gaza gano hakan ko kuma an gano amma wa’alla saboda yawan bukatu an kasa dakilewa. Bincike ya nuna cewa a kasuwar Singer da Abubakar Rimi da ke Kano, ana sayar da buhu mai nauyin kilo giram 25 na wannan sinadari kan Naira 45,000, wanda ke bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da...
Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...
Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar. Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar. Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis...
Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare. Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin....
Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC. Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,...
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta hada gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) a yaki da hako ma’adinai da kuma ayyukan ta’addanci a kasar nan. Mukaddashin Daraktan shiyyar Kaduna mai kula da shiyyar Kaduna, Mista Bawa Usman Kaltungo ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar ofishin shiyya ta Kaduna na EFCC zuwa NUJ a jihar Neja a Minna. Mista Bawa Usman wanda ya shaida wa manema labarai cewa an kama masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba amma ya ci gaba da cewa “yaki da wadannan laifuffuka ba na EFCC kadai ba ne domin yana da girma da yawa a gare mu don haka yana bukatar hadin...
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Buhari ya gode wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gyaran da aka yi masa a gidansa na Kaduna. Ya gode wa gwamnonin APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah, inda ya ce wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuwa sabbi ne. Shugaban gwamnonin kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna godiya da girmamawa da gudunmawar Buhari wajen gina demokradiyya da ƙarfafa jam’iyyar APC. Uzodinma ya yaba wa Buhari saboda salon shugabancinsa, da yadda ya miƙa mulki cikin natsuwa ga wani shugaban APC, tare da aiwatar da shirye-shirye a fannonin tsaro, noma, ilimi da ababen more rayuwa. Ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,...
Manajan daraktan cibiyar CGIAR Ismahane Elouafi, ta jaddada cewa idan ana son rage tsadar shigar da abinci nahiyar, wanda a yanzu ya kai kimanin dala biliyan 100 a kowacce shekara, zuba jari wajen inganta kyawun kasa da samar da ruwa da rainon ingantattun irrai masu samar da kyakkyawar yabanya, na da matukar amfani. Ta ce nahiyar Afrika za ta iya cin gajiyar fasahohin aikin gona na kasar Sin, da wanda ya dace da hadin gwiwar kasashe masu tasowa, domin bunkasa noma a cikin gida da ma fitar da amfanin gonar. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da shirin don kula da lafiyar al’ummar jihar musamman masu karamin karfi. Dr Abdullahi Kainuwa yana mai cewar a yanzu haka gwamnatin jihar tana gudanar da aikin Dandamalin sabon asibitin kashi na garin Gumel kan naira miliyan 380. A cewar sa, za a bada kwangilar sayen kayayyakin asibitin Kashi na naira miliyan dari shida. Kwamishinan ya kara da cewar gwamnatin jihar ta kammala aikin gina dakunan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba. Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin...
Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar da ayyukan gwagwarmayar Yeman na goyon bayan al’ummar Gaza ko kuma kare jiragen Isra’ila a tekun Bahar Rum. A wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a, Abdul-Malik al-Houthi ya ce Amurka ta zafafa kai hare-hare a kan kasar Yemen, inda wasu lokutan ta kai hare-hare sama da 90 a kowace rana, a wani bangare na goyon bayan da take baiwa kasar Isra’ila a yakin kisan kare dangin da ta ke yi a zirin Gaza. Duk da haka, ya jaddada cewa, hare-haren na Amurka “sun kasa dakatar da ayyukan soji da ke tallafawa al’ummar Falasdinu,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...