Aminiya:
2025-09-18@00:57:36 GMT

Shugaban Ƙungiyar Afenifere, Adebanjo ya rasu

Published: 14th, February 2025 GMT

Shugaban Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Pa Ayodele Adebanjo ya rasu yana da shekara 96.

Rahotanni sun ce dattijon ya rasu ne da safiyar Juma’a a gidansa da ke Lekki a Jihar Legas. An tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da iyalansa suka fitar.

Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano Ta kacame tsakanin mahaifiyar 2Face da budurwarsa

“Ya rasu a safiyar yau Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, a Legas Nijeriya yana da shekara 96.

Za mu ci gaba da riƙe alƙawarinsa na fafutukar tabbatar da gaskiya da adalci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya yi ta bayyana halayansa da gwagwarmayar na tabbatar da samun ’yanci da ci gaban Najeriya gaba ɗaya.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannu a madadin iyalan Madam Ayotunde Atteh (nee Ayo-Adebanjo), Madam Adeola Azeez (nee Ayo-Adebanjo), da Mista Obafemi Ayo-Adebanjo.

Shahararren Lauya, tsohon sakataren Ƙungiyar Action Group kuma shugaban Ƙungiyar Afenifere na Ƙasa, Adebanjo ya rasu ya bar matarsa, Cif Christy Ayo-Adebanjo da ’ya’ya, jikoki da ’ya’yan jikoki.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?

Duk da cewar an yi yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, rikici ya sake ɓarkewa bayan NUPENG ta ce Dangote bai cika alƙawari ba.

Amma matatar ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ma’aikatanta na da damar shiga ƙungiya idan sun so, amma ba dole ba ne.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Chadi:  Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa  damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • Jigilar Mai: Me Ya Haddasa Rikicin Dangote Da Ƙungiyar NUPENG?
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta