Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba
Published: 5th, February 2025 GMT
Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta sanar da naɗa sabon shugabanta, Farfesa Adamu Ahmed.
Majalisar Gudanarwar jami’ar ce ta zaɓi Farfesa Adamu Ahmed a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Kabir Bala.
An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zaboAn sanar da zaɓen Farfesa Adamu da misalin ƙarfe 6:15 na safiyar wannan Larabar a yayin zaman Majalisar Gudanarwar jami’ar wanda Mahmud Yayale Ahmed CFR ya jagoranta.
Farfesa Adamu Ahmed dai malami ne a sashen nazarin tsara birane na jami’ar ta ABU.
Ya taɓa riƙe muƙamin Darektan Cibiyar Bunƙasa Jami’ar kuma a yanzu shi ne Uban Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Adamu Ahmed Jami ar ABU Farfesa Adamu
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA