2025-09-18@20:52:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9060

«hare hare ta»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka  na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi tir da wadannan ayyuka na  ta’addanci, tare da jaddada bukatar  daukar matakin gaggawa daga kasashen duniya don dakile aniyar yahudawan sahyuniya ta kawo hargiti a gabas ta tsakiya, wanda kai tsaye yake shafar tsaro na kasashen duniya. Ta bayyana wannan munanan aiki da cewa, ba wai kawai laifukan yaki da laifin cin zarafin bil’adama ba ne, har ma  yana a matsayin ramuwar gayya...
    Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata. Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa, wasu ministoci da dama sun samu raunuka sakamakon wannan ta’asa, kuma a halin yanzu suna samun kulawar lafiya. Duk da haka, fadar shugaban kasar ta ba da tabbacin cewa cibiyoyi za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ga jama’a ba tare da wani tsaiko ba, duk kuwa da girman Rashin da aka yi. Dangane da matsayar kasar Yemen kan batun yakin  Gaza, fadar shugaban kasar da ke  birnin San’a ta jaddada wa...
    Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran  Reuters ya kasa tabbatar da inda yake. Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo. A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF  ya...
    A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a birnin tashar ruwa na Tianjin dake arewacin kasar Sin. Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Masar na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, ya kuma yi kira da a yi amfani da damar bikin cika shekaru 70 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekara mai zuwa, wajen cimma nasarar gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai daya a sabon zamani, da kara bayar da gudummawa don wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, da bunkasa ci gaba da walwalar sassan kasa da kasa. A dai yau din, shugaba Xi ya gana da firaministan Cambodia Hun...
    Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in. An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana. Abin da nake nufi...
    Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba. Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum. A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin. Don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon Gwamnatin Tarayya da hukumar NEDC domin...
    Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce har kullum kasar Sin za ta kasance amintacciyar abokiyar huldar MDD, kuma a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da majalisar, da tallafa mata, ta yadda MDDr za ta taka muhimmiyar rawar jagoranci a harkokin kasa da kasa, da hada karfi da karfe wajen sauke nauyin dake wuyanta na kare yanayin zaman lafiyar duniya, da ingiza ci gaba da walwalar dukkanin sassa. Shugaba Xi, ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin da yake ganawa da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a birnin tashar ruwa na Tianjin. Ya ce tarihi ya nuna yadda cudanyar mabambantan sassa, da goyon baya da hadin gwiwa, suka kasance amsa ga tarin kalubalen dake addabar duniya. Mista...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da zai iya wargaza dangantakar abokantaka tsakanin Iran da Armeniya. Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa, damuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin Caucasus na baya-bayan nan, musamman kasancewar dakarun kasashen waje a wannan yanki mai matukar muhimmanci, an kawar da su sosai bisa la’akari da fayyace da kuma tabbacin da jami’an kasar Armeniya suka bayar. Ya ce, “Dole ne su...
    Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya gana tare da tattaunawa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya a safiyar yau. A cikin wannan taro, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana gamsuwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi kan matakin tattalin arziki, siyasa, tsaro da kasar Armeniya, tare da jaddada hadin gwiwa da...
    Watan Mayu 1956,aka gabatar da kudurin niyyar yin doka a majalisar Kudu maso gabashin Nijeriya, suka gabatar da kudurin zai bada dama ta a amince da Sarakunan gargajiya, wanda ta haka ne aka samu damar kafa majalisar Sarakunan Kudu maso gabashin Nijeriya, duk kuwa a lokacin da akwai turjiyar da aka samu daga masu fafutukar tafiyar da lamurra yadda suka dace, saboda sun ki goyon bayan a sa su masu Sarautun gargajiya a harkokin yadda ake tafiyar da gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Kungiyar Hamas ta yi maraba da Allah wadai da kasashen Turai 6 suka yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi marhabin da matakin da wasu kasashen Turai shida suka dauka na yin Allah wadai da wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka yi a kan birnin Gaza, tare da la’akari da shi a matsayin wani muhimmin mataki da ke kara habaka matsayar kasashen duniya na neman kawo karshen wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu. Kasashen da ake magana a kai su ne: Iceland, Ireland, Luxembourg, Norway, Slovenia, da Spain. Ministocin harkokin wajensu sun bayyana rashin amincewarsu da hare-haren wuce gona da iri kan...
    Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza ya wuce kare kai, don haka dole ne a matsa lamba kanta don kawo karshen yakin da kuma bala’in jin kai. Ya ci gaba da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila na ruguza tsarin samar da kasashe biyu. A nata bangaren, jami’ar kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai, Kaja Kallas ta bayyana cewa: Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun dauki...
    Zanga-zangar adawa da kakaba yunwa da gudanar da kisan kare dangi da sojojiin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza a biranen kasar Morocco Dubban al’ummar Moroko ne suka gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama na masarautar kasar a cikin jerin gwanon dare, domin neman kawo karshen yunwa da kisan kiyashin ga Falasdinawa a zirin Gaza. Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka tsananta kai hare-hare ta sama, da kasa da kuma ta ruwa a wasu unguwanni a cikin birnin Gaza, inda Falasdinawa kusan miliyan daya suke, tun da sanyin safiyar Juma’a. Wannan dai na daga cikin shirinta na mamaye birnin da kuma kammala kisan gillar da ta shafe watanni 23 tana yi wa Falasdinawa....
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, ta kama wani direban mota ɗauke da jabun kuɗi har Naira miliyan ɗaya. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar cewa jami’an sintiri na Gwamnatin Tarayya ne suka tsayar da direban a kusa da gidan Guru Maharaji, kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara  Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Direban mai suna Akande, ya fito daga Legas ne, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Osogbo, babban birnin Jihar Osun, kafin shiga hannu a ranar Juma’a. A cewar Osifeso, lokacin da aka tsayar da motar, direban ya fara rawar jiki abin da ya sa jami’an suka...
    Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan.   Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye.   Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu...
    Wakilin kasar Sin a fannin cinikayyar kasa da kasa, wanda kuma shi ne mataimakin ministan cinikayya na kasar, Li Chenggang, ya yi musayar ra’ayoyi da jami’an gwamnatin Amurka, dangane da alakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu. Li, ya jagoranci tawagar kasar Sin yayin zantawa da jami’an ofishin baitulmalin Amurka, da na ma’aikatar cinikayya, da na ofishin wakilin cinikayyar kasar, tsakanin ranakun Laraba da jiya Jumma’a a birnin Washington. Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayyar Sin ta fitar bayan ganawar, ta ce sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi dangane da yadda za a aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin zantawarsu ta wayar tarho a ranar biyar ga watan Yunin bana, da ingiza alakar tattalin arziki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki. A tasu gabatarwar ta hadin gwiwa, Dakta Goni Shetima,wanda shi horarwa ne ta bangaren tsarin TaRL,da Malam Abdulrahman Ibrahim Ado, kwararre jami’in ilimi na UNICEF, sun bayyana cewa tsarin an fara gudanar da shi a karamar hukumar Alkaleri. Kamar yadda suka ce, an fara tsarin ne da makarantu 190, ‘yan makaranta 10,865, sai kuma Malaman makarantar gwamnati 290. Shi ma darektan shiyya na hukumar (UBEC), wanda Abdulsalam Abubakar ya...
    Tsohon babban jami’in hukumar tsaro ta Marshall a Jihar Gombe, Alhaji Haruna Jonga, ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya koma APC. An yi bikin karɓarsa a ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gombe. Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Shugaban ALGON na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya ce wannan sauya sheƙa na Jonga alama ce cewa jama’a suna yaba wa ayyukan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya. Shugaban APC na ƙaramar hukumar Gombe, Alhaji Abubakar Danladi, ya ce Jonga babban mutum ne da zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi, musamman kafin zaɓen 2027. Da yake jawabi, Jonga, ya bayyana cewa ayyukan raya ƙasa na...
    ‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi. Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma, kuma dole doka kullum ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babbar manufarta. Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan taro wajen tattauna muhimman batutuwan da suke tsara makomar Nijeriya.” “Ya ce, ‘Ina fatan wannan taro zai ba ku damar tattauna batutuwan da suka shafi makomar al’ummarmu. Abubuwa uku ne manya: Ci gaba da kokari wajen gyaran dokoki domin a hankali...
    Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar. Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi. Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar...
    Yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tura manyan ayyukan ci gaba zuwa Legas, tambaya a nan shi ne: shin za a ji daɗin “Renewed Hope” daidai da yadda ake ji a bakin tekun Legas a ƙauyukan Arewa maso Gabas? Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar. A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor. Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata. Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya...
    Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka haɗa da jihohi 18. Rahoton binciken da wakilanmu suka gudanar ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 3.9 a jihar Legas. A cewar rahoton, cikin lokaci guda, FEC, wadda Shugaban Ƙasar ke jagoranta, ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma,...
    A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwarya na kasar ya bayyana cewa tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin kasar zai gudana ne a tarurruka da kuma kafafen yana labarai na gwamnati. Wannan dai ya sami suka daga yan jarida wadanda suke ganin kundin tsarin mulkin kasar na kowa da kowa don haka hana kafafen yada labarai masu zaman kansu gudanar da tattaunawar bai dace ba. Hakama hana jamiyyun adawa, wadanda basa dasawa da gwamnati shima bai kamata ba. Sékou Jamal Pendessa na kungiyar yan jaridu a kasar ya...
    Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar. An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu daga kungiyoyin gargajiya na Taraba da sauran jihohin yankin. A jawabinsa, Gwamna Kefas ya bayyana cewa haɗin kan Arewa maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ingantattun ababen more rayuwa. Ya kafa da cewa taron gwamnonin na bayar da dama ta musamman don tsara manufofi da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin. Editan BBC Hausa ya magantu...
    Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI wucewa ta sararin samaniyar kasar. Banda haka ta bukaci a kore daga Majalisar dinkin duniya. Majalisar ta bukaci a kula da hakkin Falasdinawa a fagen kasashen a kuma kawo karshen yakin da ke faruwa a gaza, a ranar jumma’a ce majalisar dojojin kasar ta Turkiyya ta amince da wadannan matakan, wadanda suka dakatar da harkokin kasuwanci kwata-kwata da HKI da hana sararin samaniyar kasar ga jiragen HKI. Ya bukaci dukkan shugabannin bangariri na majalisar su sanyawa dokar hannu don ya samu matsayin gwamnatin da mutanen turkiyya gaba daya. Kudurin ya bukaci a kafa kasar Falasdinu...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kama ma’aikatan Mosad na HKI a lardin Khorasan Razavi  da ke arewa maso gabacin kasar, wadanda suka taimakawa HKI a kan hare-haren da ta kaiwa kasar na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto sanarwan da dakarun suka bayar a jiya Jumma;a na cewa, bangaren leken asiri na su ya sami nasarar kama wasu mutane 8 a cikin lardin wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kuma suna aiki kai tsaye da HKI a cikin yakin. Labarin ya kara da cewa gungun mutanen guda 8 suna aiki...
    Jakadan kasar Iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeed Iravani yayi watsi da shirin kasashen turai 3 na sake farfado da takunkuman MDD kan Iran.. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa  Iran tana kan bakanta na tattauna da wadan nan kasashen Turai, wato Burtaniya, farana da kuma Jamus. Amma ba zata shiga tattaunawa da su tare da takura mata ba. Iravani ya bayyana cewa kasashen turai ne suka fara sabawa yarjeniyar JCPOA, inda suka ki aiwatar da alkawulan da suka dauka a cikinta. A halin yanzun dai kasashen turan sun bawa Jumhuriyar Musulunci ta Iran dama har zuwa wani lokaci don cika wasu sharudda kafin...
    “A yayin aikin ceto, wanda aka sace din ya sami raunin harbin bindiga a kafarsa ta hagu bayan ‘yan ta’addan sun bude wuta lokacin da suke kokarin tserewa,” in ji sanarwar.   An garzaya da wanda aka ceto zuwa asibiti, kuma a halin yanzu yana samun sauki.   Kwamishinan ‘Yansanda, Bello M. Sani, ya yaba wa jarumtar jami’an da ‘yan sa-kai bisa saurin daukar mataki, tare da sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Kebbi.   “Wannan aikin ceto ya nuna jajircewarmu wajen kawar da miyagun laifuka a jihar. Ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron kowace al’umma,” in ji Sani.  ...
    Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ce zargin cin zarafi a wurin aiki da ake yi masa ba su da tushe. Lamarin ya samo asali ne bayan wata tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Halima Umar Saleh, a yayin wata tattaunawa da tashar Arewa24 ta bayyana cewa ta fuskanci musgunawa a lokacin aikin ta, kodayake ba ta ambaci sunan editan da ya yi mata hakan ba. A cikin bidiyon, Halima ta ce ta sha wahala a lokacin da take aiki a sashen, tana mai cewa wani babban jami’i ya nuna mata ƙiyayya ba tare da wani dalili ba, abin da ya sa ta shiga damuwa ta kan yi kuka akai-akai. Ta bayyana cewa ta sha barazanar korar aiki duk...
    A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da kwarewa wajen gano yadda aka boye kwayoyin. “Wannan lamari ya nuna jajircewar hukumar wajen katse hanyar rarraba miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaron al’umma.” Ya rawaito kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da himma wajen gudanar da aikin. Idris-Ahmad ya kuma yaba wa shugaban hukumar NDLEA na kasa, Tsohon Birgediya-Janar mai ritaya, Mohamed Buba-Marwa, bisa goyon baya da jagoranci da yake bayarwa. “NDLEA a Jihar Kano ta dage wajen aiwatar da manufarta ta kawar da miyagun kwayoyi a jihar, tare da gode wa hadin kai da goyon bayan jama’a wajen cimma wannan buri,” in ji shi. A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa...
    A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas. Hotuna: Bassey Willie            
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci. Wasu sun rasa matsugunansu saboda rashin tsaro. Wasu kuma suna asibiti ba tare da kulawa ta gari ba—ko kuma ba za su iya zuwa ba saboda babu kuɗi a hannunsu. “Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba...
    Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021.   Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin dala biliyan 1.46 zuwa yau daga dala biliyan 39.54 a ranar daya 19 ga watan Agustar shekarar 2025, suka karu zuwa i dala biliyan 41.00.   Wannan ya nuna yadda karuwar Asusun ta kai zuwa kaso 3.69 a kasa da makwanni uku, da suka gabata.   Bugu da karu, Asusun ya samu wannan karuwar ce, saboda yawan shigowar kudaden musaya na waje cikin kasar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi.   Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta. “Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare,...
    Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu.   Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba.   Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka. A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya...
    Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja. Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar. Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro. Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi Ya ruwaito...
    A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a  cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD. Kasashen uku da aka fi sani da E3  sun ce a shirye suke su dage mayar da takunkumin har na tsawon watanni shida idan Tehran ta amince da sake baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga cibiyoyinta na nukiliya, tare da  magance abin da suka kira damuwar da suke da ita game da yawan tataccen sinadarin uranium da ta ke da shi, da kuma shiga tattaunawa da Amurka. Sabanin haka, jakadan...
    Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Juma’a cewa, sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya yanke shawarar  soke takardar izinin shiga kasar ga wasu mambobin kungiyar ‘yantar da ‘yancin Falasdinu (PLO) da hukumar Falasdinu (PA), ciki har da shugaban PA Mahmoud Abbas, gabanin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York na watan Satumba mai zuwa. Wadannan matakai na nufin cewa da alama Abbas ba zai iya zuwa New York  don gabatar da jawabinsa na shekara kamar yadda ya saba yi ba. Wannan mataki dai na cikin jerin takunkuman da Amurka ta kakabawa jami’an Falasdinawa a watan Yulin da ya gabata, a daidai lokacin da wasu kasashen yammacin duniya ke neman amincewa...
    Cibiyar Bloomberg ta bayar da rahoton cewa, Rwanda ta karbi  rukunin farko na bakin haure da aka kora daga Amurka, a karkashin wata yarjejeniya mai cike da takaddama tsakanin gwamnatin kasar da  gwamnatin Donald Trump. Mai magana da yawun gwamnatin Rwanda  Yolande Makolo ya tabbatar da cewa “rukunin farko na bakin haure bakwai da aka tantance sun isa Rwanda a tsakiyar watan Agusta.” A karkashin yarjejeniyar, Kigali ta yi alkawarin daukar mutane kusan 250, wadanda suka yi alkawarin kula da lafiyarsu, da wurin kwana, da koyar da su sana’o’i. Canja wurin ya zama wani ɓangare na babban ƙoƙarin Washington na tura bakin haure zuwa wasu kasashe da ta kulla yarjejeniya tare da su kan hakan. Tun daga lokacin da ya...
    Jack Neriya, tsohon shugaban hukumar leken asirin Isra’ila a Syria da Lebanon, ya yi gargadi game da masu tunann cewa ta yi rauni,  yana mai jaddada cewa “kungiyar ta sake gina karfin soji kuma ba ta da niyyar yin watsi da makamanta.” A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin, Neriya ya ce, “Tun daga watan Nuwamba, Hezbollah ta sake tsara sahunta, ta dawo kera jiragen sama marasa matuka da sauran makamanta, tare da jaddada kudurin ta na ci gaba da yin amfani da makamanta.” Ya kara da cewa, bayyanar babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem a bainar jama’a a cikin kayan soji na nuni da daukar matakin da ya dace, musamman ma a lokacin...
    Mayakan ‘Yan ta’adda na  kungiyarAl-Qaeda sun karbe ikon garin Farabougou da ke tsakiyar kasar Mali, mako guda bayan da suka kwace sansanin sojojin da ke garin, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa. Kungiyar ‘yan ta’adda ta (JNIM) ta sanar a wasu jerin sakonni da ta fitar cewa,  ta kwace garin tare da kafa abin da ta kira tsarin shari’a musulunci. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto wasu jami’an yankin da suka tsere daga Farabougou na cewa yanzu haka garin na karkashin ikon kungiyar JNIM. A makon da ya gabata ne aka tilastawa sojojin ficewa daga sansaninsu da ke Farabougou, daya daga cikin sansanoni mafi girma a yankin, bayan wani hari da mayakan masu ikirarin jihadi suka kai musu. Tun daga...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya isa Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, domin halartar taron gwamnonin Arewa maso Gabas karo na 12 da za a gudanar gobe Asabar. Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum  ne, zai jagoranci taron. Taron zai mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma hanyoyin magance matsalolin ayyukan jin-ƙai a yankin. Mutum 12 sun nutse bayan sake kifewar jirgin ruwa a Sakkwato An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Za a yi taron ne na tsawon kwanaki biyu, inda ake sa ran gwamnonin za su bayar da muhimman shawarwari da kuma cimma matsaya kan matsalolin . A cewar Isma’ila Uba Misilli, Daraktan Yaɗa Labarai na fadar...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya isa Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, domin halartar taron gwamnonin Arewa maso Gabas karo na 12 da za a gudanar gobe Asabar. Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum  ne, zai jagoranci taron. Taron zai mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma hanyoyin magance matsalolin ayyukan jin-ƙai a yankin. Mutum 12 sun nutse bayan sake kifewar jirgin ruwa a Sakkwato An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Za a yi taron ne na tsawon kwanaki biyu, inda ake sa ran gwamnonin za su bayar da muhimman shawarwari da kuma cimma matsaya kan matsalolin . A cewar Isma’ila Uba Misilli, Daraktan Yaɗa Labarai na fadar...
    Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar.   Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Ambasada Zango ya ja hankali kwamitin da ya kara zage damtse wajen yin gaggami, yana mai cewa dukkan katunan da ba a amsaba har yanzu suna hannun INEC.   Ya yaba wa gwamnatin jihar da ta kafa wannan kwamiti, yana mai cewa mambobin kungiyar da shugabanin Waiya za su taimaka wajen gudanar da wannan aiki cikin nasara.   Ya kuma tabbatar da cewa kwamitin zai hadin kai da INEC wajen wayar da kan masu zabe kan sabon rajistar da kuma amsar katunan zaben.   Da yake magana a fadar gidan gwamnatin Jihar Kano, kwamishinan yada labaran ya bayyana cewa Gwamnan Jihr Kano, Abba Kabir Yusuf ne da kansa ya kafa kwamitin don shigar da dukkan kungiyoyi a cikin jihar, ciki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima, rashin saka rigar iyo, amfani da jiragen ruwa marasa inganci, da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro. Duk da wannan, gwamnati ba ta ɗauki matakan tsaro ba. A halin yanzu, magidanta a Shagari da ƙauyuka maƙwabta na cikin tashin hankali suna jiran labari game da ‘yan uwansu da suka ɓace, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    An sake samun damuwar kifewar jirgin ruwa a Ƙaramar hukumar Shagari inda jirgin ruwa ya nutse da mutane 12 a Ƙaramar hukumar ta Jihar Sakkwato wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu namiji da mace sauran 10 suka samu raununka. Hatsarin ya faru ne da daren ranar Alhamis a gulbin Shagari inda mutane suka shiga cikin damuwa da kaɗuwa kan jirgin daya nutse da mutane da babur guda biyu da sauran kayan amfani, a wata ɗaya jirgi uku ya nutse a ruwa a Sakkwato. Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa Nasir Umar wanda lamarin ya faru gaban idonsa ya ce, “jirgin...
      Tare da jagoranci da zuba jari, Nijeriya na iya samun fiye da Dala biliyan 4 a shekara a kudaden fitar da fata, kirkirar miliyoyin ayyukan yi, da kuma dawo da matsayin tarihi a matsayin babbar mai karfi a duniya a fannin fata.   Misali daga Jihar Legas Jihar Legas kwanan nan ta kaddamar da Mushin Industrial Leather Hub, da nufin samar da kudaden fitarwa na Naira biliyan 387.5 a kowace shekara. Wannan abin ban mamaki ne, idan aka yi la’akari da cewa Legas ba ta da wani tushe a fannin kiwo. Wannan kaddamarwar tana nuni wani rashin daidaito: a yanzu dai Legas ce ke jagoranci tare da hangen nesa da tsara dabarun da ya kamata a ce jihohin Arewa...
    A ranar 23 ga watan Augusta aka gabatar da shirin musayar al’adu mai taken “Echoes of Peace” a birnin Mexico na kasar Mexico. Cikin jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo, Mr.Shen Haixiong, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya ce yana farin cikin gayyatar baki su hallarci wajen gabatar da shirin domin a waiwayi tarihi tare a kuma fahimci abun da ya faru, wanda tasirinsa ya keta lokaci da yankuna. Ya ce a shirye kafar CMG take ta zurfafa hada hannu da abokan hulda na kasa da kasa wajen hada kai domin shawo kan kalubale da neman ci gaba ta hanyar hadin gwiwa. (Fa’iza Mustapha)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen yakin HKI suka cilla a kan motarsa a kauyen Sair cikin lardin Nabadiyya. Tashar talabijin ta Al-mayaddeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, sojojin yahudawan sun jefa boma-bomai har guda hudu a kan garin Kafar Kila a kudancin kasar ta Lebanon. Labarin ya kara da cewa a garin kafar kila, sojojin yahudawan sun kai hare hare da dama a yau Jumma’a bayan wadanda muka bayyana amma basu kai ga kashe ko raunata wani ba. A jiya Alhamis ma jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hare hare a wurare da dama daga...
    Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Muhammad Hassan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasashen masu rauni a duniya sun damu da yadda manya-,manyan kasashen duniya suka kyale HKI take yin abinda taga dama a kasar Falasdinu da ta mamaye. Kuma hakan zai sa kasashe da dama su kauravewa HKI. Labarin ya kara da cewa HKI a cikin shekaru kimani biyu da suka gabata, sun kashe falasdinawa fiye da dubu 62, amma MDD da kuma sauran kasashen yamma sun hana hatta shigar abinci a cikin zirin gaza....
    Ajayi-Kadri ya ce kungiyar ta yi cikakken nazari kan sake gabatar da harajin na FOB wanda ta tabbatar zai kara dagula lamura ne kawai da sake jefa masana’antu cikin mawuyacin hali.   “Gaskiyar lamarin ita ce, farashin kashi hudu cikin 100 na kamfanonin ya yi yawa fiye da yadda aka samu karin kashi bakwai cikin dari da kuma karin kashi daya cikin dari na harajin tsarin shigo da kayayyaki,” in ji shi.   Ya kara da cewa, a sauran kasashen yammacin Afirka kamar Ghana, Cote d’Iboire, da Senegal, ana tsare-tsaren da aka yi niyya ko tattara kudade a tsakanin kashi 0.5 zuwa kashi daya cikin 100 na FOB, tare da karin haraji kawai kan kayan alatu ko kuma wadanda ba...
    Shugaban kamfanin rarraba wutan lantarki na kasar Iran ya bada sanarwan cewa kasar China ta zuba jari na kimanin dalar Amurka miliyon 70 a aikin samar da wutan lantarki mai karfin MW 200 wanda kamafanin SATBA yake ginawa a lardin Bushar na kudancin kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Gholam Reza Hashmati ya bayyana cewa wannan shi ne zuba jari mai tsoka wanda kamfanin waje yayi a shirin samar da makamashi mai tsabta na kasar Iran. Yace MW 200 zai taimaka wajen samar da wuta mai tsabta ya kuma rage dogaro da man fetur da kuma gas wadanda suka gurbata yanayi. Hashmati ya kammala da cewa yankin Bushar yana gaba a cikin yankunan kasar Iran...
    Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: Ina kiran mutanen Jamus kan cewa ku ne kuka samar da ikidar Nazi, a yayinda mu a kasar Italia da Spaine muka samar da akidar Fasim a nahiyar turai a baya, wana ya kai kasashen turai ga lalacewa.. Jami’ar ta bayyana haka ne bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro na Jamus suka yi kan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa wadanda kuma suke bukatar HKI ta...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike mai ƙarfi na ƙwararrun jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar rundunar ‘sojan Najeriya, domin gano abin da ya jawo aka kashe wani jami’in soja da wani sifeton ’yan sanda ya yi a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), CSP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu a hedikwatar rundunar da ke Bauchi a ranar Juma’a. Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Wakil ya ce, an ɗora wa kwamitin alhakin tattarawa da...
      Haka kuma, Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, kasar Sin tana son mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da kulla hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare tare da Amurka, bisa tabbatar da kare muradun ikon mallakar yankunan kasarta, da tsaro da kuma ci gaban kasar.   Ya kara da cewa, a shirye muke mu yi aiki tare da Amurka a kan turba guda, da aiwatar da muhimman yarjejeniyoyi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ci gaba da sadarwa a tsakaninmu, da warware batutuwan da muka sha bamban a kai, da fadada hadin gwiwa, da kuma ci gaba da lalubo hanyar da ta dace manyan kasashen biyu su tafi tare da juna a sabon zamani.   Jami’in ya...
    An kashe makiyaya huɗu tare da jikkata wani a ƙauyen Fili, da ke yankin Doemak, a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan a Jihar Filato. Rahotanni daga yankin sun ce an kai musu hari ne lokacin da suke tsaka da kiwo. Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Sakataren kuɗi na Ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a Qua’an Pan, Saeedu Abdurrahman, ya tabbatar da lamarin. Ya ce ’yan bindigar sun kashe makiyayan amma ba su sace shanunsu ba. Ya ƙara da cewa lokacin da ake binne waɗanda suka rasu, ’yan bindigar sun sake kai wani harin, amma jami’an tsaro sun...
    A Arewa maso Yamma, an kama ‘yan ta’adda 35 kuma an kuɓutar da mutane 76. A Arewa ta Tsakiya, an kama mutane 49, an ceto mutane 36, yayin da a Kudu maso Gabas aka kama mambobin IPOB tara. A Kudu maso Kudu, sojoji sun kama mutane 48, sun lalata wuraren tace ɗanyen mai, tare da ƙwato ɗanyen mai da dizal da kuɗinsu ya kai sama da Naira miliyan 443. Janar Kangye ya tabbatar da cewa, za su ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare domin tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, manyan tituna, tashoshin ruwa da wutar lantarki, gadojin kan hanyar ruwa da masana’antu, duk wadannan an tanade su ne don su zama hanyar rage talauci da tallafawa al’umma. Ta hanyar inganta yanayin rayuwa da samar da damarmakin tattalin arziki, kasar Sin ta yi nuni da cewa, tana kara karfafa martabar jama’ar Afirka ta hanyar samar musu da ci gaba.   ’Yancin Cin Gashin...
    Sanata Kabiru Garba Marafa tsohon ɗan Majalisar Dattawa da ya wakilci yankin Zamfara ta tsakiya jigo a Jam’iyar APC a jihar ya fice daga jam’iyar. Sanata Marafa ya bayyana ficewarsa a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook a ranar Jumu’a ya ce bayan tattaunawa da magoya bayansa sun cimma matsayar barin Jam’iyyar APC kan ta zalunce su. An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Ƙara Kuɗin Fasfo: Gwamnati na jefa ’yan Najeriya cikin matsi — Obi “Bayan mun yi waiwaye a shekara biyu da rabi da suka gabata mun gano cewa, APC a matakin ƙasa da jiha ta zalunce mu, a matakin jiha lalacewar jam’iyar ya kai matuƙa tun bayan kafa kwamitin riƙon...
    Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi.   Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su dukufa da yin addu’o’in neman zaman lafiya a yankin.   Da yake magana da kafar BBC bayan taron, mai ba da shawara ga ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, kungiyar ta yi nazari da bitar matsalolin da suke addabar arewa tare da cimma matsayar cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa.   “Matsalolin nan ga su nan a zahirance, kuma dole ne a tursasa gwamnati ta...
    Shehu, a cikin littafin nasa wanda ya bai wa wakilinmu na LEADERSHIP, ya yi zargin cewa; Obasanjo ya bijiro wa Buhari da wasu bukatu a lokacin da yana shugaban kasa (Obasanjo).   Ya kara da cewa, “Akwai da dama a kusa da Buhari da ke ganin cewa; abin ban mamakin da ya faru a tsakanin Buhari da wanda ke gabansa a aikin sojan da yake mutuntawa, Shugaba Olusegun Obasanjo, shi ne sakamakon bukatar da aka ce Obasajon ya nemi a bai wa wani dan kwangila da yake so a aikin wuta ta Mambila.   “A kan haka, Buhari cikin ladabi ya fada wa tsohon shugaban kasar cewa, ya bar shi ya gudanar da abin da ya kamata, ta hanyar bin...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa A cewarsa, Ado ya aikata wannan aika-aika ne tare da wasu masu laifin a ranar Talata. Waɗanda suka haɗa da: Musa Kwalle da Dan Abba da Sule Musa da wani Arrow dukkansu daga ƙauyen Gerawa. Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Agusta da misalin ƙarfe...
    Da aka tuntubi Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed mai ritaya, ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce; jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.   Haka zalika, mazauna Ndanaku da ke Karamar Hukumar Patigi a Jihar Kwara, sun kauracewa wurin sakamakon hare-haren ‘yan bindiga. Kazilika, harin na zuwa ne makwanni kadan bayan faruwar makamancin haka a garin Babanla da ke Karamar Hukumar Ifelodun.   Kwamandan ‘yan banga, Gina Gana; wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa; an kai hare-hare guda biyu ne kwanaki uku da suka gabata, wanda ya tayar wa da kowa hankali a garin.   Har wa yau, a makon day a gabata ne Gwamna...
    Kungiyar Marafa ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da watsi da tsarinsa na siyasa da kuma rashin tallafawa al’ummar da ke fama da matsalolin tsaro. Daga ƙarshe, ta bayyana cewa Marafa da dukkan magoya bayansa a kananan hukumomi da mazabu 147 na Zamfara sun fice daga APC, kuma nan gaba za su bayyana sabon matsayar siyasar da za su bi.     —   Wannan sigar za ta fi ja hankalin masu karatu a yanar gizo. Kana so in ƙara ƙaramin taken ƙasa (sub-headline) da ke ƙara jan hankali, irin na jaridu, misali: “Tsohon Sanatan Ya Ce Zamfara Ta Fi Kowa Fama da Sace-Sace Amma Gwamnati T a Yi Watsi da Ita”?   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Ambaliyar ruwar da ta biyo bayan mamakon ruwan saman da aka tafka ta raba kauyuka shida da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato da saurann yankunan jihar. Kauyukkan da ambaliyar ta shafa su ne Makuwana da Dangawo da Faru da Gumbula da ’Yan Faruna da kuma Magajin Dawaki, sannan ta lalata hanyar da ta hada kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni. An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ Tuni dai Majalisar Dokokin Jihar ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da ke kula da harkokin ruwa da su dauki matakin da ya dace kan wadanda lamarin ya shafa. Hakan...
    Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar.   Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi.   Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya soki gwamnatin tarayya kan ƙarin kuɗin fasfo da aka sanar cikin makon nan. Ya bayyana cewa wannan ƙarin ya nuna rashin la’akari da halin da talakawa ke ciki a yau. A cewar Obi, sabon farashin fasfo na – ₦100,000 mai shafuka 32 da ₦200,000 mai shafuka 64 – ya fi sabon albashin ƙasa na ₦70,000, abin da ya ce bai dace ba da halin da ma’aikata ke ciki. Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000 Ya zargi gwamnati da ƙara ƙaƙabawa jama’a ƙarin nauyi maimakon sauƙaƙa musu, musamman a lokacin da tattalin arziƙin...
    Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Hossein-Ali Haji-Deligani, Mataimakin Shugaban Kwamitin Mataki na 90 na Majalisar Dokokin Iran, ya tabbatar da cewa za a shigar da kudirin zuwa tsarin majalisar a rana mai zuwa sannan a sake duba shi a wani budadden zama. “Kamar yadda muka fada a baya, wadannan kasashe sun riga sun fara aiwatar da takunkumin da aka kakaba mana. Babu wani sabon abu...
    Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda ka ke tare da shi ya fahimci me kake faa ba.”   Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), Dakta Sunusi Yakubu Ahmed, ya bayyana jin dadinsa matuka bisa zabar kwalejin don gudanar da wannan taron.   Dakta Sunusi ya ce: “Tun lokacin da na ga an yi irin wannan taron a Jami’ar Northwest, na bukaci nima ina da burin...
    Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kira mummunan halin da ake ciki a Gaza a matsayin abu mafi muni a wannan lokaci ta fsuakr mawuyacin hali da dan adam yake ciki. Yayin da yake magana da manema labarai a birnin New York a ranar Alhamis, Antonio Guterres ya bayyana yadda ake lalata tsarin abinci da ruwan sha da na kiwon lafiya a Gaza, lamarin da ya sa mutane ke fuskantar yunwa. Guterres ya bayyana damuwarsa kan mamayar da sojojin Isra’ila suka yi a birnin Gaza, yana mai cewa hakan na nuni da wani gagarumin ci gaba a yakin. “Daruruwan dubban fararen hula-da suka gaji kuma sun gaji-zasu sake tilastawa yin gudun hijira, tare da jefa iyalai cikin mawuyacin hali. Dole...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
    Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar.   Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki.   Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa. Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta...
    Ba wai muna yin jayya da sanarar da ofishin Nuhu ya samu a tsakanin wadannan watanni ba ne kuma muna sane da kokarin da yake yi, na ganin cewa, ‘yan Nijeriya na samu su kwanta su yi barcin dare, idanuwansu biyu a rufe ba tare da wata fargabar ko za a kai masu hari ba.   Tabbas, muna jinjina masa kan yunkurin da yake ci gaba da yi na rage kalubalen rashin tsaro da Gwamnatin mai ci ta gada.   Amma mummunan harin da wasu mahara suka kai a watannin baya a yankin Yelwata, inda suka yi wa wasu al’umomin yankin kisan kiyashi da kuma harin da ‘yan bindiga suka kai kan Masallaci a garin Malumfashi ta Jihar Katsina, ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.   Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke shirin, latsa nan
    Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna.   Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta tarayya, domin kokarin gano musabbabin faruwar al’amarin.   A cikin sanarwar da NRC ta fitar a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa; jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan hanyarsa.   Kazalika, hukumar ta bayyana cewa; daga cikin fasinjojin, mutum akalla 14 ne suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuma,...
    Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. ‎A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake daga bisani Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya wanke shi daga zargi, inda ya ce ba satar kudaden aka yi ba, na aiki ne. Magauta sun sa NNPCL a gaba – Ojulari Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso To sai dai jaridar ta sake yin labari mai taken “Gwamnan Kano ya kare hadiminsa barawo, ya ce gwamnatin Ganduje ma ta...
    Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci. Bunkasar Harshen Hausa ya sa harshen ke barazanar batar da kananam harsuna wadanda tuni wasu da dama a yau suka bace ba amo ba labarin su a bisa ga yadda yake mamaye harsuna a mabambantan kasashe. Sai dai duk da kima da martabar da Harshen Hausa yake da shi da yadda daruruwan miliyoyin al’umma ke magana da Harshen har yau Jamhuriyar Nijar kadai ce kasar da ke amfani da Hausa...
    Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari ya ce mutanen da ba sa nufin Najeriya da alheri sun sa kamfanin a gaba saboda sabbin tsare-tsaren da yake kawowa na inganta fannin man fetur a kasar. Ya bayyana hakan hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Manyan Ma’aikatan  Bangare Man Fetur da Iskar Gas na Kasa (PENGASSAN) a hedkwatar kwamfanin da ke Abuja. Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso Dangote ya ƙulla yarjejeniyar gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 2.5 a Habasha Ojulari ya ce duk da yake sun san za su iya fuskantar kalubalen, amma ba za su taba bayar da kai bori ya hau ba a yunkurinsu na inganta rayuwar...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dangantaka tsakanin Iran da China na dauke da dabarun manufofi masu kyau Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasar Iran na da sha’awar gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana da kasar China, musamman a fannin raya dabarun kiyaye hanya, yana mai bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin kyaukyawar dabara. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis don daidaita yin nazari kan fannoni daban-daban na dangantaka da hadin gwiwa, da kuma bayyana ajandar ziyarar shugaban kasar China. Taron ya samu halartar manyan jami’ai da shugabannin hukumomin zartarwa da abin ya shafa. A yayin wannan taro, an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Matakin da gungun kasashen Turai ke son dauka kan Iran yana dagula tsarin diflomasiyya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi la’akari da yadda kasashen Turai uku suka yi amfani da tsarin warware takaddamar da ba bisa ka’ida ba a karkashin tsarin hadin gwiwa na (JCPOA) da kuduri mai lamba 2231 a matsayin doka, yana mai cewa wannan matakin yana dagula tsarin diflomasiyya. A daidai lokacin da kasashen Turai uku ke son amfani da tsarin warware takaddamar da ba bisa ka’ida ba a kan ka’ida ta JCPOA da kuduri mai lamba 2231, a yammacin ranar Alhamis, Kaya Kalas, babban wakilin kungiyar EU mai kula da harkokin waje da kuma mai kula...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani ga Tawagar Turai na kokarin dawo da takunkumi kan kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwa a matsayin martani ga sanarwar da Tawagar Tura ta yi wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da baya kan ka’ida dangane da kuduri mai lamba 2231. Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kakkausan harshe tare da yin Allah wadai da shelanta batu da baya kan doka da tawagar Turai Faransa da Jamus da Birtaniya suka yi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da kuduri mai lamba 2231 na shekara ta 2015. Wannan matakin bai dace ba, wanda ya ci karo da Tsarin Raba Rikici (DRM) na Haɗin gwiwar...
    Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma suna farin ciki da arangama kai tsaye da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan soji na goyon bayan Gaza muddin gwamnatin ta ci gaba da yakin da take yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan birnin Sana’a ba zai shafi goyon bayan da al’ummar Yemen ke yi ga...
    Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon Shirin Isra’ila na fadada ayyukanta a birnin Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi gargadi kan mummunan sakamakon matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila zata dauka na fadada ayyukan soji a birnin Gaza, yana mai yin Allah wadai da manufofin fadada gine-ginen matsugunan yahudawa ‘yan mamaya a yankunan gabar yammacin kogin Jordan. A jawabin da ya yi wa manema labarai a jiya Alhamis, gabanin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a hedkwatar Majalisar dake birnin New York, Guterres ya bayyana cewa, matakin farko da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka na kwace birnin Gaza ya sanar da wani sabon yanayi mai hadari. Ya kara da cewa “fadada...
    Yanzu haka a nan kasar Sin ana ta shirye-shiryen gudanar da babban bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar sojojin Japan, da nasarar yakin kin tafarkin murdiya, wanda shi ma wani lokaci ne da zai dada tabbatarwa duniya zahirin abubuwan da suka wakana, tare da karyata sassan dake kokarin lullube gaskiya, da kaucewa daukar alhakin ta’asar da aka aikawa al’ummar Sin a yayin mamayar birnin Nanjing. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Manyan Jami’ai A Ma’aikatar Tsaro Ta...
    A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya. Wannan ya nuna niyyarsu ta hada hannu wajen tunawa da tarihi da kiyaye zaman lafiya da adalci.   Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil...
    An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89.   Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya. Kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tekun duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Teku ta Duniya, Hukumar Kwastam ta Duniya, da tsarin Majalisar Dinkin Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani ta kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama sabon Sarkin Zuru Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya. Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar...
    A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare. Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen...
    Ƙasar Habasha ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani reshe na Rukunin Kamfanonin Dangote na Nijeriya domin gina wata sabuwar masana’antar samar da takin zamani na kimanin dala biliyan 2.5. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙo da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed ya wallafa a shafin X ranar Alhamis. Sanusi Mikail Sami ya zama sabon Sarkin Zuru Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso Abiy ya ce wannan yarjejeniya da Dangote Group na attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, za ta sanya ƙasarsa cikin jerin manyan ƙasashen da ke samar da takin zamani a duniya. Ya bayyana cewa wannan aikin gina masana’antar wanda za a fara nan ba da jimawa ba, za ta riƙa samar...