2025-09-18@20:50:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9060
«hare hare ta»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan nan. A karkashin Sashe na II, bangare na 4 na dokar, dukkan mutane da kungiyoyi da abin da haraji ya shafa dole ne su yi rajista a hukumomin haraji da suka dace kuma su samu Katin Tantance Haraji (Tax payer Identification Card). Dokar ta ba hukumomin haraji ikon bayar da Tax ID a madadin wadanda suka gaza yin rajista, ko su ki karbar bukata idan...
A yau Lahadi ne aka kammala baje kolin kasa da kasa na hada-hadar cinikayyar hidimomi na kasar Sin na shekarar 2025, ko CIFTIS a takaice a nan birnin Beijing. A cewar mashirya bikin, baje kolin ya cimma manyan nasarori sama da 900 a fannonin gine-gine, da fasahar sadarwa, da hada-hadar kudade da sauransu. CIFTIS na bana, ya gudana ne tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga watan nan na Satumba, bisa jigon “Rungumar fasahohi masu basira, karfafa hada-hadar cinikayyar hidimomi,” ya kuma hallara masu baje hajoji a dandalinsa na zahiri su kusan 2,000, da wasu karin kamfanoni kimanin 5,600 da suka baje nasu hajojin ta yanar gizo. Har ila yau, a cewar mashirya baje kolin, ya zuwa tsakar ranar Lahadin nan,...
Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16, wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement....
A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, fadar shugaban ƙasa, ba ta fitar da wata ƙwaƙwarar sanarwa, kan maƙasudin soke takardar ɗaukar aikin da aka yiwa Umunubo ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su. A ranar 8...
Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!. Da daman mutane ba sa zaɓar wani kansila da zuciya guda, sai don ya dare kujerar ne ya biya musu bukatunsu na daidaiku. Haka Ciyaman, haka “yan Majalisun jiha, haka Gwamna, haka” yan Majalisun taraiya, haka ma kujerar Shugaban Kasa. A tunanin akasarin mutane a yau, bukatunsu na daidaiku, shi ne mazaɓa, shi ne karamar hukuma, shi ne jiha, kai, kacokan ma shi ne Nijeriya. Saboda haka, wajen samun biyan wadancan bukatu, komai...
“Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana da muhimmiyar ma’ana a fannin warware matsalolin da suka shafi tsarin shugabancin duniya a yanzu. A halin yanzu, sauyin karfi a tsakanin kasashe masu ci gaba da ma kasashe masu tasowa shi ne sauyi mafi girma da aka samu a sabon zamanin da muke ciki a fagen kasa da kasa, inda tarin kasashe masu tasowa suka bunkasa da sauri. To sai dai kuma tsarin duniya...
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila. Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba; LIVERPOOL Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar Naira 500,000, waɗanda suka samu Azurfa Naira 250,000, yayin da waɗanda suka lashe Tagulla suka tashi da Naira 150,000. A jawabinsa na rufe gasar da aka gudanar a filin wasa na Uyo, babban birnin jihar, Gwamna Eno ya bayyana cewa dukkan ’yan wasan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 31 na jihar. Baya ga kyautar da ’yan wasa suka samu, gwamnan ya bai wa kowace...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati ta gargaɗi jihohi 11 kan yiwuwar afkuwar ambaliya a wannan makon Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Kayan da aka bayar sun haɗa da shinkafa, taliya, man girki, da kuma tufafi, kayan mata da shadda. Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), Dokta Mohammed Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya ba da umarnin gaggauta tallafa wa al’ummar...
An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi. Bikin na bana, ya hallara baki daga sassan duniya da dama, an kuma gabatar da lambobin yabo ga fina-finai da wasannin kwaikwayo karkashin rukunoni 27. Cikin fina-finan da aka karrama akwai Ne Zha 2, wanda ya lashe lambar yabo ta wasan zane mai motsi mafi kayatarwa. Sai fim din “There’s Still Tomorrow”, wanda ya zama fim mafi kayatarwa. Fim din “She and Her Girls” ya samu yabo...
A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin cire kayayyakin lantarki. “Rundunar ta fara cikakken bincike kan lamarin, kuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno an kwashe gawar zuwa asibiti domin a gudanar da binciken likitanci yadda ya kamata.” Ya jaddada cewa rundunar ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin gargaɗi ga mazauna jihar da su guji aikata lalata kayayyakin gwamnati. Daso ya ƙara da...
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis. A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta. An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan a Akwa Ibom Ban taɓa nadamar shiga Kannywood ba — Kabiru Nakwango Sauran sun haɗa da Neja, Kebbi, Kano, Katsina, Sakkwato da Zamfara. Sanarwar ta bayyana cewa cikar kogunan Gongola, Benuwe da Neja na ƙara barazana ga al’ummar da ke zaune a gefen kogunan. Gwamnati ta shawarci al’ummar da ke yankunan da abin ya shafa, musamman waɗanda ke kusa...
A cewar kakakin ‘yansandan, jami’an sun tare wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka mai lamba GGE 473 BH bayan direban ya kasa bayar da kwakkwaran bayanin kansa da kuma motar. Ya bayyana cewa binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano wata bindiga da aka kera a cikin gida, harsashi masu rai guda hudu, fasfon aikin ɗansanda na bogi da kuma waya lambar mota mai lamba FGE 68 a Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba 001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma a ENL Consortium, za su rinƙa yin amfani da lambApapaETO bisa nufin rage cunkoso a ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa.ɗauke da launin rawaya,” Inji Lawal. Ya bayyana cewa, wannan sabon garanbawul ɗin da aka yi, za ta taimaka wajen matsalar ƙetarawa hanyar da manyan motocin ke fuskanta a Tashar ta Apapa. Lawal ya ci gaba da cewa, bisa nazarin da aka gudanar a...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar Naira 500,000, waɗanda suka samu Azurfa Naira 250,000, yayin da waɗanda suka lashe Tagulla suka tashi da Naira 150,000. A jawabinsa na rufe gasar da aka gudanar a filin wasa na Uyo, babban birnin jihar, Gwamna Eno ya bayyana cewa dukkan ’yan wasan sun fito ne daga ƙananan hukumomi 31 na jihar. Baya ga kyautar da ’yan wasa suka samu, gwamnan ya bai wa kowace...
Hakazalika, sojojin na Brigade 12 tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da ’yan banga a wannan rana, sun ceto fasinjoji 17 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi. Hakazalika, dakarun Sashe ta 1 ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun ceto wani a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benuwe. Haka kuma a jihar Filato a wannan rana, dakarun Sashe ta 8 ta ‘Operation Enduring Peace (OPEP)’ sun kama wasu da ake zargin barayin ne a karamar hukumar Mangu tare da kwato makamai da alburusai da kudade. A wani samame kuma sojojin na Shiyya ta 1 OPWS sun kwato bindiga kirar AK-47 daya da harsashi 29 a wani sintiri a...
Masu lura ko sa ido kan harkokin ilimi sun ce biyan kuɗaɗen cikin lokaci za su taimaka matuƙa wajen samun matsin da takurar da ƴan makaranta ko Iyayensu ke fuskant, bugu da ƙari kuma za su kasance a wuraren da suke karatu domin maida hankali kan abinda ya sa suke a makarantar ko kwalejin Hukumar ta kafar sadarwar zamani duk waɗanda suke amfana da tsari da su tabbatar da bayanan Banki da suka bada da na makaranta daidai suke domin hakan ne zai bada dama ta ci gaba da samun kuɗin duk lokacin da aka tashi biya ba ater da ɓata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan titin garin Mubi a ɗimauce. Anan ne, jami’an ‘yansandan suka ceto yaran da suka hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya da Mohammed Alhassan, dukkansu mazauna garin Gwange, Maiduguri, jihar Borno. Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa wani mai suna Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange, Maiduguri ne ya ɗauko yaran daga Maiduguri ba bisa ƙa’ida ba....
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da sanarwar ta G7, tana mai cewa ba ta da tushe balle makama Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah-wadai da zarge-zargen da mambobin kungiyar G7 da kawayenta suka yi dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tana mai kallon hakan ba gaskiya ba ne. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana zargin da ke kunshe a cikin sanarwar hadin gwiwa na kasashen G7 da kawayenta dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cewa ba gaskiya ba ne. Sanarwar ta kara da cewa: Yin zargin karya kan wadanda ke da alhakin kare tsaron kasar Iran wani lamari ne karara na murguda gaskiya da kuma...
Cikakkun bayanai kan halartar Iran zuwa taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya na kasar Iran Muhammad Islami ya yi karin haske kan yadda Iran za ta halarci taron shekara -shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA. Mohammad Eslami ya bayyana dangane da cikakkun bayanai na halartar taron shekara- shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA inda ya ce: A gobe ne za a fara taron shekara- shekara na hukumar IAEA karo na 69 a birnin Vienna. Ya kara da cewa: “Iran zata tsara tare da gabatar da wani kuduri na yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin nukiliyarta na zaman lafiya...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana dalilin da ya sa tawagarta ba ta halarci kada kuri’a kan batun Falasdinu ba Ofishin Jakadancin Iran ya jaddada cewa, duk wata hanyar warware matsalar Falastinu a zahiri dole ne ta dogara kan amincewa da hakkin al’ummar Falastinu na dogaro da kai da kuma watsi da duk wani batun tilasta musu yin gudun hijira. Ta kuma jaddada cewa, za a iya samun dawwamammen zaman lafiya ne ta hanyar kawo karshen mamaya da kuma samun cikakken ‘yancin kai gami da samun ‘yancin kai na kasar Falasdinu, tare da la’akari da ainihin nufin ‘yan asalinta-Musulmi, Yahudawa, da Kirista—ta hanyar kuri’ar raba gardama mai ‘yanci, kamar yadda aka gabatar a cikin takardar yarjejeniya mail amba S/2019/862. A...
Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su. A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da ma yadda ya ce fim ɗin Hausa ya taɓa zama silar sasanta wasu ma’aurata da aurensu yake tangal-tangal. Tun yaushe ka shiga harkokin fim ɗin Hausa? Ai harkar fim ɗin Hausa daga baya ta fito, a da wasan kwaikwayo ake yi. Na fara wasan kwaikwayo na rediyo wajen 1970, lokacin ina ƙarami. A lokacin rikoda ta fito. To a sannan na fito a matsayin mace...
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
Kona mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, a cikin dare mai wahala ga zirin Gaza Da sanyin safiyar Lahadi 14 ga watan Satumban shekara ta 2025 jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, musamman birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata da dama. Sun kuma tayar da bama-bamai tare da tarwatsa gidaje da hasumiyai da nufin tilasta wa mazauna wurin tserewa tare da raba mafi yawan adadinsu da muhallinsu domin gudu zuwa tsakiya Gaza da kuma kudancin gabar tekun. Majiyoyin lafiya a asibitin Al-Shifa sun ba da rahoton mutuwar wani Bafalasdine tare da jikkatar wasu a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata...

Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba
Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza. Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya...
“An biya wasu bukatunmu, gwamnati ta yi alkawarin duba sauran bukatun, don haka, an dakatar da yajin aikin, za mu dawo wuraren ayyukanmu don ci gaba da aiki a ranar Lahadi, mun yi hakan ne domin nuna fatan alheri da kuma taimaka wa ‘yan Nijeriya da ke neman lafiya a cibiyoyinmu daban-daban,” in ji Osundara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi. Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su. Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya, tare da rufe tashar rediyo ta kashin kai a Jihar Neja, kafin ya ƙaru zuwa ga kai hare-haren da aka ɗauki nauyi kan taronmu na Kaduna, sannan kuma da hare-hare a kan ayarin motocin shugabannin ADC a Kebbi. “Haka kuma an kai hari a wurin taron ADC a Alimosho a Jihar Lagos, wannan yana nuna cewa APC ta ji kunya kuma ba ta girma ko...
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar korar Falasɗinawa sama da mutum 250,000 daga birnin Gaza tun bayan da suka fara zafafa kai hare-hare a yankin. Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an Falasɗinu suka ce da dama sun gaza ficewa daga kudancin ƙasar saboda cunkoso. Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta — Sanusi II ’Yan rakiyar amarya 19 sun mutu a hatsarin mota a Zamfara Mai magana da yawun sojojin Avichay Adraeeya wallafa haka a shafin X, yana cewa fiye da kashi 1 bisa huɗu na waɗanda suka rage a Gaza sun gujewa birnin don kare lafiyarsu. Sai dai, Hukumar Tsaron Farar Hula ta Gaza, ta ba da rahoton cewa adaɗin waɗanda suka...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da maza da mata da yara ta faɗo daga saman karyayyiyar gadar, ta nutse a cikin ruwa. Wani ɗan uwan amaryar, Babangida Halifa Ibrahim Fass, wanda ya rasa ’yan uwa a cikin hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da ake kai ’yar uwarsa amarya gidan mijinta da ke Jega a Jihar Kebbi. Ya ce, “Motar ta faɗo ne daga kan gada ta nutse...
Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, kasashen Saudiya, Turky da Iraki su jira randa boma-baman HKI zasu fada a kan kasashensu. Rezai ya bayyana haka ne rana guda kafin a fara taron gaggawa na kasashen larabawa da musulmi a yau lahadi a birnin Doha na kasar Qatar. Ya ce idan taron na Doha ya kasa samar da kawaice kasashen don fuskantar...
Wani mutum mai shekara 67 aka kai asibiti da raunuka masu barazana ga rayuwa, abin takaici kuma ya rasu a asibiti a ranar Juma’a, 5 ga Satumba. An bayyana sunansa da James Gbadamosi.” Bayan faruwar lamarin, ƴan sanda sun bayyana cewa sun kama Wright-Walter mai shekaru 37, suka gurfanar da shi bisa laifin kai hari a watan Agusta, amma aka ba da belinsa. Sai dai an sake kama shi a ranar Asabar bayan rasuwar Gbadamosi, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare a ranar Litinin. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Andre Wright-Walters, mai shekaru 37 (05.02.1988) na Aɓery Hill, Greenwich, an gurfanar da shi a ranar Lahadi, 7 ga Satumba. Ya bayyana a gaban kotun majistare ta...
Jiragen yakin HKI sun rusa dogon gini kuma gidajen mutane Annoor dake unguwar Tel Hawa na birnin Gaza, a shirinta na rusa dukkan dogayen gine gine a birnin Gaza. Tashar talabijibijin ta presstv ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun tilastawa dubban mutane a wasu unguwanni a birnin na Gaza kauracewa gidajen nasu a dai dai lokacin yahudawan suke ci gaba da rusa dogayen gine gine a birnin. Labarin ya kara da cewa manufar yahudawan a wadannan rushe-rushe sun hada da korar falasdinawa daga gidajensu, daga karshe korarsu daga kasarsu. Tun watan da ya gabata ne gwamnatin natanyahu ta fara aiwatar da wannan inda sojojinsa suke amfani da makamai masu karfi don cimma wannan manufar. Ya zuwa yanzo dai sun kashe...
A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata. Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba ne masu shirya jerin gwano a birnin Auckland, na kasar suka bada labarin cewa wannan shi ne tattaki mafi girma wanda aka gudanar a cikin kasar don goyon bayan al-ummar Falasdinu tun lokacin da aka fara yakin kimani shekaru biyu da suka gabata. Wadanda suka shirya zanga zangar sun bayyana cewa mutane kimani 50,000 suka fito wannan tattakin na goyon bayan Falasdinawa a Gaza, da...
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci shawara Ali Vilayati ya yi allawadi da kasar Azerbaijan kan shirya taron yahudawan turai a kasar a cikin watan Nuwamba mai zuwa, kuma ya bayyana taron a matsayin tsokanace ga musulmi da kuma addinin musulunci, kuma ba zai je ko ina ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Vilayati yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa , wannan shi ne karon farko wanda aka taba gudanar da taron yahudawan duniya a birnin Baku na kasar Azerbaijan, kasa ta musulmi shia. Ya ce, wannan shi ne karon farko wanda aka gudanar da taron yahudawan duniya a kasar musumi shia, kuma kowa ya san cewa, taron tsokanane...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni waɗanda ba su da nagarta. Ya bayyana haka ne a bikin “Kano International Poetry Festival” da aka yi a Kano a ranar Asabar. Gini mai hawa 3 ya rufta kan mutane a Legas HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Sarkin ya ce matsalolin ƙasar nan sun samo asali ne daga rashin shugabanci na gari. “Ƙasar nan tana tashi da faɗuwa bisa ingancin shugabanni. Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta. “Kowace rana kuna gani a jaridu da labarai, ’yan majalisa suna ɓata lokaci kan abubuwan da ba su da amfani, yayin da sauran ƙasashe suke tattauna abubuwa kamar...
“An ajiye gawar a ɗakin ajiye gawarwaki yayin da bincike ke ci gaba. Za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala binciken.” Da yake magana kan sauran masu laifi da aka kama a faɗin ƙananan hukumomi 18 na jihar, kwamishinan ya ce an cafke su ne bisa zargin aikata laifuka da suka haɗa da: kisan kai, garkuwa da mutane, fashi da makami, shiga ƙungiyoyin asiri, mallakar miyagun ƙwayoyi ba bisa doka ba, da sata, da sauransu. Lawal ya nuna cewa an samu nasarar waɗannan kame ne ta hanyar ƙoƙarin jami’an rundunar da kuma haɗin kan jama’ar jihar, waɗanda suka bayar da sahihan bayanai ga rundunar. A cewarsa: “A cikin makonnin da suka gabata, rundunarmu ta...
Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin Isra’ila da take yi kan alummar falasdinu. A cikin wani bayani da ya aike da shi a shafinsa na X ya ce wannan mataki zai tilastawa shugaban Amurka yin gaggawa wajen mika umarninsa ga gwamnatin Isra’ila bisa hujjar kawo zaman lafiya a duniya da kuma bada kyautar zaman lafiya ta Nobel. Kasar Qatar ta sanar da kiran zaman gagganawa na kasashen larabawa da na musulmi a ranar litinin mai zuwa domin tattaunawa game da harin da Isra’ila ta kai domin kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta. Manyan jami’an hamas da suke tattaunawa kan batun bukatar...
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun bude wuta kan gungun falasdinawa dake neman agaji a yankin gaza, inda akalla mutane 4 suka mutu, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata. Wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da sama da mutane paladinawa 1000 dake neman agaji da sojojin Isra’ila suka kashe a kusa da inda ake raba kayan agaji. Dake karkashin kulawar amurka da isra’ila a yankin na Gaza. Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akalla yankin gaza yana bukatar manyan motocin agaji 500 zuwa 600 a duk rana domin biyan bukatun su na yau da kullum, sai dai har yanzu Isra’ila na ci gaba da rusa gidaje a yankin Gaza. Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar...
A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta kara lalubo albarkatun dake bangarorin al’adu da yawon bude ido na Sichuan, da gabatar da kyawun al’adun Bashu da karfafa aikin sadarwa cikin ci gaba mai inganci na lardin Sichuan. Har ila yau, an kaddamar da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohin bidiyo na ultra HD da na daukar murya da dakin gwaje gwajen ayyukan watsa labarai na kasa a birnin na Chengdu. (Mai fassara: Fa’iza...
Yau Asabar, an gudanar da taron dandalin tattauna al’adu na kasa da kasa na Golden Panda na 2025 a birnin Chengdu. Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, ya halarta tare da sanar da bude taron. Mahalarta na kasar Sin da na kasashen waje da suka halarci bikin bude taron sun bayyana cewa, ba za a iya raba tinkarar kalubale da samun kyakkyawar makoma, da karfin al’adu da wayewar kai ba. Sun jaddada muhimmancin zurfafa hadin giwwar al’adu na kasa da kasa a fannonin raya ilimi, kimiyya da fasaha, al’adu, da kafofin watsa labarai don kara inganta hadin kan al’adu da mu’ammalar jama’a. Dandalin...
Rahotanni sun bayyana cewa kasar masar ta bayyana cewa Isra’ila na shirya makarkashiyar kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta, don haka ta gargadi tel aviv da cewa duk wani hari dai dai yake da shelanta yaki kuma za su daga mata kafa ba, Wata majiyar labarai ta bayyana cewa jami’an kasar masar sun yi kira ga isra’ila da su koma teburin tattaunawa domin ganin a cimma matsaya kan batun dakatar da bude wuta a yankin gaza, mai makon jefa yankin cikin yaki da tashin hankali. A yan kwanaki nan ne hki ta kai hari ta sama a yankunan farar hula birnin Doha na kasar Qatar inda ta yi kokarin kashe manyan jami’an kungiyar Hamas dama wasu fararen hula na kasar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa alakar iran da Tunusiya wani babban misali ne na irin yadda kasar iran ke son su fadada dangantaka da sauran kasashen musulmi bisa girmamawa da mutunta juna. Haka zalika Araqchi ya jinjinawa kasar Tunusiya game da irin matakin da ta dauka musamman a lokacin harin wuce gona da iri da hki takai a kasar iran a watan yuni, yace wannan goyon bayan ya nuna irin zurfin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma ya bayyana cewa iran a shirye take ta yi aiki da kasar tunusiya a bangarorin daban-daban wajen musayar kwararewar da suke da shi a bangaren kimiya da fasaha da dai sauransu. Ana ta bangaren kasar Tunusiya tace tana...
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Taraba, ASP Leshen James, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce suna neman saurayin tare da sauran mazauna gidan da suka tsere. “Lokacin da jami’anmu suka isa wajen, ba kowa a cikin gidan. Saurayin da sauran mazauna gidan sun riga sun gudu,” in ji shi. Ya ƙara da cewa ’yansanda za su gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da Comfort. Lamarin ya haifar da firgici da damuwa ga ɗalibai da mazauna yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Rahotanni sun bayyana cewa babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince daftarin kudirin dake nuna goyon bayan kafa kasar falasdimu mai cin gashin kanta, inda ka samu kasashe 142 suka kara kuri’ara amincewa yayin da kasashe 10 kuma sun nuna rashin amincewa sai kuma guda 12 da suka kauracewa kada kuria. Wannan daftarin kudurin ya nuna irin yadda duniya ke goyon bayan kafa kasar palasdinu adaidai lokacin da Isra’ila take ci gaba da kisan kare dangi a Gaza, yayin da duniya ke ci gaba da yin tir da cin zarafi da take hakkin dan adam a gazan, Duk da yake cewa wannan daftarin kudurin ba dole ba ne amma ya kara wa matakin kima a siyasance, kuma ya kara jan...
Gwamnatin Jihar Kuros Riba, ta ce ta gano ma’aikatan bogi har guda 800 a wasu ma’aikatun jihar. Tun da farko, an daɗe ana zargin gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Farfesa Ben Ayade da biyan albashi ga wasu mutane da ba ma’aikatan gwamnati ba, musamman a ƙananan hukumomin jihar. HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200 a tukunya guda Kwamishinan ma’aikata ƙananan hukumomi, Darlington Bassey Eyo ne, ya tabbatar da hakan a Kalaba ranar Juma’a. Ya bayyana cewa gwamnati ta fara aikin tantance ma’aikata tun farkon shekarar nan, inda ta duba kowace ma’aikata ɗaya bayan ɗaya. A cewarsa, wannan ne ya sa suka gano ma’aikatan bogi da...
Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta yi karin haske kan shirin tattauna batun kamfanin TikTok a ganawar da tawagogin Sin da Amurka za su yi a kasar Sifaniya a gobe Lahadi, 14 ga wata. Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, matsayin kasar Sin kan batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma bai taba canzawa ba. Ta ce kasar Sin tana da cikakkiyar niyyar kare hakkin kamfanoninta, kuma za ta tantance batun kamfanin TikTok bisa doka. Ban da haka, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan ikon kebanta bayanai da tabbatar da tsaronsu, ba za ta taba bukatar wani kamfani ya tattara bayanai a sauran kasashe ta wata haramtacciyar hanya ba. Sanarwar ta kara da cewa, bisa...
Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya ce kasarsa na goyon bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Shugaba Vucic ya bayyana haka ne yayin da yake hira da wakilin CMG a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, inda ya ce tsarawa da gabatar da wannan shawara mai ma’ana, ya zama wani abun da ya wajaba, saboda da farko, a zamanin da ake ciki, ana bukatar samar da karin ikon wakilci ga kasahe masu tasowa a fannin kula da al’amuran kasa da kasa. Kana na biyu, yanzu sannu a hankali ana lalata sakamako da nasarorin da dan Adam ya samu ta fuskar dokoki da ka’idoji na kasa da kasa, yanayin dake bukatar...
Mariya Sanusi Dantata, mahaifiyar attajirin Afirka Aliko Dangote, tare da fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, sun halarci gasar karatun Alƙur’ani da Maryam Shettima ta shirya a Jihar Kano. An yi gasar laƙabi da #ReciteWithShetty, inda taken shi ne “Alƙur’ani: Jagora Wajen Tsaftace Kafofin Sada Zumunta”. ’Yan bindiga sun buɗe wa ’yan zaman makoki wuta a Anambra An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Manufar gasar ita ce bunƙasa tarbiyya da inganta amfani da kafafen sada zumunta. A yayin karrama waɗanda suka shiga gasar, Shetty, ta bayyana cewa dubban yara daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka shiga gasar ta hanyar kafafen sada zumunta. “Na yi mamakin yawan mahalarta. Hakan ya nuna akwai haziƙan matasa...
A nasa jawabin, Air Marshal, AVM JA Usman, ya yaba wa hafsan hafsoshin sojin saman bisa jajircewarsa da kuma sadaukarwa wajen ciyar da harkokin sojin sama da sauran ma’aikata gaba. ya yi nuni da cewa, taron ya sabunta ƙudirin hukumar na yin amfani da fasahar zamani, ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara ƙarfin gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin Operation ACCORD III sun kashe wani fitaccen shugaban ƴan ta’adda mai suna Babangida Kachala a jihar Kogi. Wannan na zuwa ne bayan samun bayanan sirri da aka samu kan motsin ƴan ta’adda a dajin Ofere da yankin Ayetoro Gbede. Bayanin da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na Sojoji, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ya ce, dakarun sun kafa shingen kwanton-ɓauna, amma daga bisani su ma ’yan ta’addan suka yi musu kwanton-ɓauna yayin da suke komawa sansani. A fafatawar da ta biyo baya, Sojojin suka yi amfani da ƙarfin makamai suka halaka ɗaya daga cikin ’yan ta’addan. Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa Binciken da...
Dokar Tsabtace Amfani da Wuta ta Ƙasa. Dokar Gyara Yanayi ta Ƙasa. Hanzarta Ba da gargaɗi. Wayar da kan jama’a kan haɗarin ambaliyar ruwa. Tilasta dokokin muhalli. Horarwa da sabunta ƙwarewar jami’ai ƙwararru. Shigar da kayan aiki na zamani, da sauransu. Har ila yau, ya bayyana cewa za a iya sarrafa ambaliyar ruwa ta hanyoyi kamar: Taruwar ruwan sama (rain harɓest) kamar yadda ake yi a China. Gyara da gina ƙarin madatsun ruwa (dams). Kafa hanyoyin ruwa. Kafa ƙarin ɗakunan gwaje-gwaje kan ambaliyar ruwa. Haramta amfani da roba ɗaya-ɗaya (single plastic use). Kulawa akai-akai da tsarin magudanan ruwa a faɗin ƙasa. Gudanar da ruwa (water management) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
ya kuma isa wurin tare da gano gawar mamacin a cikin wata mota ƙirar ‘Peugeot 406’, ɗauke da lamba kamar haka; BWR-577 BF. “Ba tare da ɓata wani lokaci ba, aka kai gawar zuwa babban asibitin Asokoro, inda likitoci sukatabbatardacewa; hargawar ta fara ruɓewa. “Kwamishinan ƴansanda na babban birnin tarayya Abuja, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan wannan al’amari da ya faru tare da bayar umarnin ƙara ƙaimi wajen gano ko wane ne mamacin.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dokar ta ba da damar dakatarwa na ɗan lokaci ko kuma cire rajistar Tax ID gaba ɗaya idan mai riƙe da shi ya daina gudanar da kasuwanci. A gefe guda, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2025, ta ba Shugaban Zartarwa na Hukumar babban ikon, wanda zai kasance shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kwamitin zai haɗa da wakilai daga Ma’aikatan Kuɗi, Tsare-Tsaren Ƙasa, Shari’a, Man Fetur, Babban Bankin Nijeriya, Haraji da Kwastam, Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni, da sauran muhimman hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a, Araqchi ya ce, “Akwai yiwuwar sake yin wani taro da jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, kuma hakan ya dogara ne da shawarar Turai. Dangane da tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira, ya ce, wadannan shawarwarin masu muhimmanci ne sosai, da kuma shawarwarin da ake yi a bayan yaki, inda hotunan shahidai ke wucewa a kan idonun mutane daya bayan daya, ba tattaunawa...
Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da kuma abubuwan da suka faru a lardin Suweida na kasar. Shugaban rikon kwaryar ya fada a jiya Juma’a cewa: Kasarsa ta yi saurin sake gina huldar dake tsakaninta da kasa da kasa, kana ta samu goyon baya daga galibin kasashe musamman na yankin. Ya yi nuni da cewa, ba za a so a kasance cikin halin damuwa da wata kasa ba, kuma kwallon tana cikin...
Jami’in kungiyar Hamas yayi tsokaci kan yunkurin kashe tawagar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Doha Jami’in kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas, Osama Hamdan ya ce: Yunkurin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi na kashe tawagar da ke tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar wani hari ne kai tsaye kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tsagaita wuta. Ya kara da cewa a wata hira da aka yi da shi a gidan telebijin, “yunkurin kashe tawagar Hamas hari ne kai tsaye kan shirin shugaba Trump, idan har Isra’ilawa sun amince da Shirin na Trump, to su saurari martanin Hamas, maimakon mayar da martani ta hanyar jefa bam a birnin Doha da wurin taron jami’an kungiyar.” Hamdan ya yi...
Sama da Falasdinawa 228,800 ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren kisan kiyashin ‘yan sahayoniyya kan Gaza a cikin wannan mako Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; Falasdinawa 38 ne suka yi shahada yayin da wasu 200 suka jikkata da aka kai su asibitoci a yankin cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga ta yau da kullun cewa, daga cikin wadanda suka yi shahadan akwai biyu da aka ciro daga karkashin baraguzan ginin, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga kisan kiyashin da sojojin mamayar Isra’ila ke yi tun ranar 7 ga watan Oktoban 2023 zuwa shahidai 64,756 da kuma jikkatan 164,059. Tun...
Sojojin Yemen sun sanar da kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a yankuna daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila Dakarun Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai farmaki kan wasu wurare masu muhimmanci a yankin Jaffa da aka mamaye. Wannan farmakin na goyon bayan al’ummar Falastinu da ake zalunta ne, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suka aikata a kan ‘yan uwa a zirin Gaza, da kuma wani mataki na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kaiwa kasar Yemen. Rundunar sojin kasar ta Yemen ta kuma jaddada cewa; Rundunar sojin kasar ta kuma kai harin ne ta hanyar amfani da makamai masu...
Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani matsayin da yawancin mambobin PDP ba sa jin daɗinsa. Kafin yanzu, jam’iyyar ta shiga cikin wata babbar matsala kan matsayin sakatare jam’iyyar na ƙasa, tsakanin Samuel Anyanwu, wanda Wike yake goyo baya, da Sunday Ude-Okoye, wanda yake samun goyon bayan Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah. Mafi yawancin shugabannin jam’iyyar sun yi tunanin cewa idan har Anyanwu ya dawo a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa zai...
Fitaccen ɗan wasan ya tuna wani lokaci da aka kama shi bayan ya tsaya wa wani a kotu wanda ya gudu, amma aka sake shi saboda shahararsa. Duk da ɗansa na daga cikin manyan masu gyaran hotunan Fim (editing ), ya ce matsayin da Allah ya ba shi a harkar fim alheri ne na ƙaddara. Ya shawarci abokan aikinsa da su ji tsoron Allah, su riƙa kare addini da al’adu, sannan su yafe wa juna. Ya kuma roki al’umma da kada su gaggauta yanke hukunci kan masu fim. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu. “Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin...
Chef Hilda Baci mai shekara 28 ta kama hanyar kafa sabon tarihin girka shinkafa dafa-duka (Jollof) ’yar Najeriya mafi yawa a duniya. Hilda Baci ta kafa wannan sabon tarihi ne inda ta girka shinkafa basmati buhu 200 a wata katafariyar tukunya a bainar jama’a. Ta yi wannan sabon abin bajinta ce shekara biyu kacal bayan ta shiga kundin tarihi na duniya na Guinness a matsayin wadda ta shafe awanni mafiya yawa tana girke-girke a duniya. A ranar Juma’a ta fara girkin a otel ɗin Eko Hotel & Suites, da ke Legas, kuma sama da mutum 20,000 mashahurai da sauransu sun yi rajista don halarta. An kama buhun tabar wiwi 150 bayan hatsarin mota a Kano Abba ya tarbi tagwayen da...
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da “Sanarwar New York” da nufin farfado da shawarwarin samar da kasashe biyu a Gabas ta Tsakiya wato Isra’ila, da kuma Falasdinu a daya bangare – amma ba tare da kungiyar Hamas ba. Kasashe 142 ne suka amince da shi, yayin da 10 suka nuna adawa da shi (ciki har da Isra’ila da Amurka) sai 12 da suka kaurace kada kuri’ar. . Bayan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, kasashe da dama sun bayyana aniyarsu ta daukar irin wannan matakin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a bude ranar 22 ga watan Satumba, ana kallon wannan tsari a matsayin karin tursaswa Isra’ila ta kawo karshen yakin da take ci...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai halarci babban taron kasashen musulmi da na Larabawa da za a yi a Doha a ranakun Lahadi da Litinin, taron da Qatar ta kira domin samar da tallafi ga Falasdinawa a Gaza da kuma mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar a ranar 9 ga watan nan kan kasar ta Qatar. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce zasu halarci taron yana mai cewa shi da shugaban kasar za su gabatar da jawabai. “Lokaci ya yi da za a yi aiki, kuma kalmomi kadai ba su isa ba,” in ji shi yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na IRIB a yammacin ranar Alhamis, yana...
Wakilin dindindin na Turkiyya a Majalisar Dinkin Duniya Ahmet Yıldız ya yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai Doha, yana mai kiransa da “ta’addanci” da kuma wani yunkuri na tada zaune tsaye a yankin yammacin Asiya Da yake magana a madadin kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) yayin wani zama na musamman na kwamitin sulhu na MDD da aka gudanar a ranar Alhamis, Yıldız ya yi tir da harin a matsayin wani bangare na tsare-tsare na Isra’ila da kuma kokarin dakile zaman lafiyar yankin. An kira taron na musamman ne a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai kan wasu manyan jami’an Hamas a babban birnin Qatar.. Sanarwar ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan wannan...
“Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa. Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba da su. Limamin da ya jagoranci sallar jana’izar gawar da aka samu a kwarin Dangoma, Mallam Musa Umar Al mishawi ya bayyana cewa; marigayin ya samu rauni a goshinsa. “Marigayin, mazaunin Unguwar Gidan Dangoma ne da ke tudun jukun ta garin Zaria, sannan kuma an yi jana’izarsa kamar yadda a safiyar yau kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji shi. Kazalika, har zuwa lokacin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
Akalla Falasdinawa 64,756 sukayi shahada a kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da ke kewaye. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kawo gawarwakin mutane 38 da suka hada da biyu da aka zakulo daga baraguzan gine-gine a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yayin da mutane 200 suka samu raunuka, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 164,059. Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa, hare haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa 14 tare da raunata wasu 143 yayin da suke neman agaji a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ya kai adadin Falasdinawa da aka kashe yayin da suke neman agaji zuwa 2,479,...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa rikicin Gaza ya kara kamari, inda ya yi gargadin cewa kusan shekaru biyu na killacewar Isra’ila da kai hare-haren bama-bamai sun yi illa ga lafiyar yara, ilimi.. “Bayan kusan shekaru biyu na abubuwan ban tsoro lamarin ya yi tasiri ga, kowane bangare na rayuwar yara,” inji Tess Ingram, manajan sadarwa na UNICEF na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka,. “Yara ba su da isasshen abinci da za su ci, ba su da ruwa mai tsafta, a kullum suna kokari su tsira daga hare-haren bama-bamai da ke ci gaba da yin barazana ga rayuwarsu. Cututtuka suna yaduwa, kuma yara sun rasa shekaru uku na zuwa makaranta,”. Share...
Ya ƙara da cewa a faɗin Afirka, bashi ya zama babban ƙalubale ga tattalin arziki, inda ƙasashe da dama ke kashe fiye da kuɗin kiwon lafiya wajen biyan bashin da suka ci. Ya ce kashi 35 cikin 100 na bashin ƙasashen Turai na daga masu ba da rance masu zaman kansu ne, kashi 39 daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa irin su IMF da Bankin Duniya, kashi 13 daga ƙasashen da ke bayar da rance kai tsaye, yayin da kashi 12 daga Ƙasar China. Abbas ya bayyana cewa Nijeriya ta kuduri aniyar jagorantar kafa tsarin duba bashin ƙasashen Yammacin Afirka ƙarƙashin WAAPAC, domin daidaita rahotanni, samar da ƙa’idojin gaskiya da bayyana bayanai, tare da bai wa majalisu damar samun bayanai cikin lokaci...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama buhu 150 maƙare da tabar wiwi a yayin da ake tsaka aikin ceto bayan wani hastarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano. Hukumar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne tsakanin wata mota ƙirar Volkswagen Golf da wata babbar mota a yankin Gadar Tamburawa da ke Jihar Kano. Kakakin NDLEA na Jihar Kano, ASN Sadiq Mohammed Maigatari, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin da aka ceto ya yi ƙoƙarin tserewa amma an yi nasarar kama shi. Ya ce a yayin bincike ne aka gano buhuna 150 na tabar wiwin wanda nauyinsu ya kai kilogram 112. Abba ya tarbi tagwayen da aka raba...
A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya. Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan. A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci...
Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka. A cewar ma’aikatar, bangarorin biyu za su tattauna kan haraje-harajen Amurka da yadda aiwatar da matakan kayyade fitar da kayayyaki da batun manhajar TikTok da sauran batutuwan tattalin arziki da ciniki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja An yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman. Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta...
“Masu sayayya na kasar Sin na son sabbin abubuwa da sauyi, kuma muna bukatar masu ci gaba habaka harkokinsu a nan.” Mataimakin shugaban kamfanin Unilever Zeng Xiwen ne ya bayyana haka, yayin baje kolin cinikayya da zuba jari karo na 25 da aka kammala a baya bayan nan. Shugabannin kamfanonin kasa da kasa da dama ne suka halarci taron tare da bayyana kudurinsu na daukar manufofi masu dogon zango a kasar Sin, inda suka yi amana cewa, wajibi ne su ma harkokin kasuwanci da suka tsaya da kafafunsu, su ci gaba da kirkiro sabbin abubuwa domin tafiya tare da ci gaba mai inganci na kasar Sin. Karin damarmaki na kara bullowa ga kamfanoni kasashen waje a kasar Sin. Yanzu haka...
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta raba kayan tallafi ga al’ummar Jalingo-Kamo da ambaliyar ruwa ta shafa a Karamar Hukumar Kaltungo, inda iftila”in ya shafi gidaje kimanin 90. Rabon kayan ya biyo bayan umarnin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya amince da bayar da kayan abinci da na masarufi domin rage raɗaɗin da jama’ar da abin ya shafa suke ciki. NAFDAC ta kama jabun maganin maleriya na ₦1.2bn a Legas Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo Yayin rabon kayan a fadar Hakimin Jalingo-Kamo, Sakataren Hukumar SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna Abdullahi ya ce sun gudanar da cikakken bincike da ƙirga waɗanda abin ya shafa kafin rabon. Abdullahi ya bayyana lamarin...
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro (maleriya) da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan ₦1.2bn a Legas. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a shafinta na sada zumunta X, inda ta ce jami’anta sun kai samame a wani ɗakin ajiyar kaya da ke yankin Ilasa-Oshodi, inda aka gano katan 277 na jabun magungunan maleriya nau’in Malamal Forte. Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja NAFDAC ta ƙara da cewa, “Ta kama katan 277 na jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro na Malamal Forte...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya ce: “Ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare hakki da tsaron al’umma, kuma ba za su taba tasirantuwa da kage-kagen yanayi ba, kuma za su yi aiki da karfi da azama wajen tabbatar da muradun al’ummar Iran.” Wannan dai ya zo ne a wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Alhamis, inda ministan harkokin wajen kasar Abbas...
Akpabio ya yi kira ga duk ƙasashen membobin WAAPAC da su samar da izinin majalisa ga kwamitocin da suka dace, yana mai cewa hakan zai tabbatar da ‘yancinsu da ingancinsu wajen kare dukiyar jama’a. “Bashin gwamnati, idan aka sarrafa shi yadda ya kamata, zai zama aiki ne mai muhimmanci wajen ɗaukar nauyin ci gaba, ayyukan more rayuwa, da ci gaba mai ɗorewa. Amma idan aka bar shi ba tare da sanya ido ba aka ɓoye shi cikin rashin gaskiya, zai zama nauyi da ke sanya makomar ‘yan ƙasa cikin haɗari. Wannan shi ya sa majalisa ba za yi watsi da sanya ido a kansa wajen bashi kulawa ba. “Kwarewar Nijeriya ta nuna cewa idan kwamitocin majalisa suka samu ikon doka,...
Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta. Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta...
An kammala taron baje kolin zuba jari na duniya na Sin karo na 25 (CIFIT) a jiya Alhamis 11 a birnin Xiamen. A yayin taro na wannan karo, an kulla yarjejeniyoyin ayyukan zuba jari guda 1,154, inda jimillar kudin dake kunshe a ciki ta kai kudin Sin Yuan biliyan 644 (kwatankwacin sama da dala biliyan 90.5 ). An kuma fitar da rahotanni masu inganci guda 21. Taron mai taken “Hadin kai da Sin don zuba jari ta yadda za a samu bunkasa nan gaba,” ya gudana ne a fadin filin baje koli da ya kai murabba’in kilomita 12. An gudanar da ayyukan habaka zuba jari sama da dari, kuma tawagogin kasashe da yankuna fiye da 120 sun halarta, tare da...
Wani dalili da ba zato ba tsammani ya janyo gazawar kashe manyan shugabannin Hamas a Doha Kafofin yada labarai sun bayyana wani dalili na bazata a ranar Laraba da ya biyo bayan gazawar da Isra’ila ta yi na kashe manyan shugabannin Hamas a Doha babban birnin Qatar. Kamfanin dillancin labaran RT ya nakalto tashar talabijin ta Channel 12 cewa, kwana guda bayan kaddamar da shirin kawar da ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Doha, rahotanni na nuni da cewa harin bai yi nasara ba, sakamakon matakin da shugabannin Hamas suka dauka na yin sallar azahar tare da ficewa daga dakin tattaunawar. Wani abin ban mamaki shi ne, shugabannin Hamas sun bar wayoyinsu a cikin dakin tattaunawar, lamarin da ya...
Sanata Ibrahim Lamiɗo, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta a yankinsa, inda ya ce hare-hare da satar mutane sun zama ruwan dare. A hirarsa da manema labarai, Sanatan ya ce: “Gaskiya abin tsoro ne rayuwa a Gabashin Sakkwato. Kusan kowace rana sai an kai hari, an kashe mutane ko kuma an sace su. Muna cikin tashin hankali sosai.” ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da yake yi wajen ganin an kawo gyara, wasu ’yan siyasa suna kawo cikas. Sai dai ya ce ba zai fasa jajircewa wajen ganin...

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan
Bugu da kari, kafa wurin kare muhalli na kasa da kuma tsara ayyukan kamun kifi a tekun tsibirin Huangyan na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antar kamun kifi a yankin. Matakin da Sin ke dauka a wannan karo ya nuna iyakoki da manufofin da aka tsara a karkashin doka, ya kuma fayyace iyakokin ayyukan da suka kamata a yi a tekun tsibirin Huangyan, kana ya bullo da shiri mai ma’ana domin rigakafin barkewar rikice-rikice. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Direban ya yi nasarar tserewa, amma sun harbi motar, inda Zakari Benjamin da Samaila suka samu raunuka a ƙafafu,” in ji shi. ‘Yansanda daga Kontagora sun isa wajen da abin ya faru, sannan suka kai waɗanda suka ji rauni asibiti. Abiodun ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa wajen, amma ‘yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji. Ya kuma shawarci direbobi da su guji yin tafiya cikin dare. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin. An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
’Yan bindiga sun kai wa wata mota hari a kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a Jihar Neja, inda suka jikkata mutum biyu. Harin ya faru ne a Tudun-Fulani bayan direban motar ya ƙi tsayawa lokacin da ’yan bindigar suka buƙaci ya tsaya. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 Rashin tsayawarsa ya sa maharan suka buɗe wa motar wuta, inda suka jikkata fasinjoji biyu da ke zaune a kujerar gaba. Wannan lamarin ya faru ne bayan sa’o’i da ’yan bindigar suka sace wasu makiyaya a garin Usalle da daren ranar Laraba. Rahotanni sun nuna cewar ’yan bindigar sun tura makiyayan bakin hanya sannan...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Hukumar Binciken Hatsari ta Najeriya (NSIB) ta fitar da rahotonta na farko, inda ta tuhumi wani matuƙin jirgin sama na Air Peace da kuma wani ma’aikacin jirgin da laifin shan miyagun ƙwayoyi da barasa. Masu binciken hatsarin sun gwada ma’aikatan jirgin cewa suna amfani da abubuwan da ake zargin su bayan da jirgin su da ya yi yunƙurin sauka tare da kauce hanya ba tare da izinin hakan ba a titin jirgin sama na filin jirgin sama na Fatakwal a ranar 13 ga Yuli, 2025. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Hakan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na share fage mai ɗauke da...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da miƙa ƙudirin doka ga Majalisar Dokokin Jihar domin haramta auran jinsi da kuma wasu aiyukan batsa a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a ofishin gwamnati na birnin Kwankwasiyya. A wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tauye darajar addinin Musulunci da al’adun Kano ba. ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano Ya bayyana cewa ƙudirin ya fi karkata kan hana auran jinsi ɗaya,...
Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Adelabu, ya ce gwamnati ta samu nasarar samar da wutar lantarki da rarraba ta a matakin da ba a taɓa samu ba a tarihin ƙasar. Ya bayyana cewa bunƙasa wutar lantarki shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, domin tana tallafa wa makarantu, asibitoci, masana’antu da kasuwanci. Ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu. Ubangiji tabaraka wata’ala ya yi murnar ranar haihuwar Annabi Yahya AS (wasalamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare shi (Yahya), ranar da aka haifeshi, da ranar da zai koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe shi da rai). Annabi Isa AS kuwa, da kanshi ya yi...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da mika kudirin dokar haramta auren jinsi daya, luwadi da madugo ga Majalisar Dokokin Jihar domin amincewa da shi a matsayin doka. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Juma’a, ya ce gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin zaman majalisar zartarwar jihar karo na 31 da aka gudanar a reshen gidan gwamnati da ke Kwankwasiyya City a Kano. Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta kan koyarwar addinin Musulunci ba, yana mai jaddada cewa dole ne Kano ta ci gaba...