2025-11-03@01:53:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 165
«tilasta wa iyaye»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Gwamna Umar Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a birnin Minna na Jihar Neja. Wannan dai na zuwa ne sakamakon hare-haren da ya janyo salwantar rayuka da aka samu a bayan nan a babban birnin. Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyya A cewar gwamnan, an haramta zirga-zirgar baburan ’yan acaɓa da masu Keke Napep daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar kowacce rana. Gwamnan ya bayyana hakan a yayin wani taro na musamman da ya gudana da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da ya ƙunshi sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a Fadar Gwamnatin jihar a ranar Talata....
A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa. “Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin. Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun fara komawa harkokinsu na yau da kullum. “Muna gode wa sojojin bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa,” inji shi. Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a Buni Yadi ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a game da buƙatar ƙarin tsaro a yankin. Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta tura ƙarin sojoji don hana faruwar irin...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa babu wani kamfen batanci da zai hana Gwamna Dauda Lawal aiwatar da ayyukan da suka shafi al’umma a fadin jihar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da sadarwa na gwamna, Malam Salihu Nuhu Anka ya rabawa manema labarai a Gusau. A cewar Anka, Gwamna Lawal ya fara aiki ne a wani aikin ceto, kuma tuni mazauna jihar suka fara cin ribar dimokuradiyya. Ya bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne kan kalaman da ya bayyana a matsayin maras tushe da wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Magaji Dosara ya yi, yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya kalubalanci kalaman da Gwamna Lawal ya...
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA, ta yi nasarar kama hodar iblis wadda aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi. Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas Hukumar ta bayyana cewa ta kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini. NDLEA ta ce jami’anta sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi riƙon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan al’ada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iyayen riƙo. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya kuma jaddada cewa, “An yi duk wani shiri don kauce wa hakan, amma duk da haka mun gaza, a madadin gwamnati da hukumomin tsaro ku yafe mana”. Gwamnan ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da suka addabi yankin Irigwe, ya kuma yi alkawarin sabunta alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar. Mutfwang ya bukaci al’umma da su dawo da tsare-tsaren tsaro na iyaye da kakanni, ya kuma yi kira ga matasa da su sa ido sosai, musamman a lokacin damuna mai zuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin dalibai 70 zuwa Masarautar Saudiyya domin karatun digiri a fannoni na addini da na zamani. Wannan na daga cikin shirin “Kaura Capacity Building Project 2025“ karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar. A yayin wani taron manema labarai, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin addinali, Injiniya Imran bn Usman, ya bayyana cewa kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar za su ba da sunayen dalibai uku, yayin da aka ware wa babban birnin jihar, Birnin Kebbi, guraben dalibai 10. Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ce za ta dauki nauyin tafiyar daliban zuwa Saudiyya, yayin da gwamnatin Saudiyya za ta dauki nauyin karatunsu da walwalarsu bayan isarsu. Mai ba da...
Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali. Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa. Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata. “Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar...
Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace. Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan. Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji An saki fasto an kuma tsare wanda ya kai kuɗin fansa Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin. Sai dai a baya, Danjuma Auta,...
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce Amurka na da masaniya kan irin karfin kare kai da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi, yayin da ya ce kasar ta shirya tsaf domin kare kanta. Ya kuma jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta yarda da Washington ba, amma duk da haka za ta gwada ta yayin tattaunawar da za a yi nan gaba a ranar Asabar mai zuwa,” in ji Abbas Araghchi yayin wani taron manema labara a Aljeriya. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman yaki, amma idan ya zama dole ta san yadda za ta kare kanta. » “Muna shakkar aniyar Amurka kuma ba mu da tabbacin cewa suna da...
An gudanar da taro na farko na kwamitin raya cinikayya da kiyaye muhalli na hukumar kula da cinikayya ta duniya wato WTO na shekarar 2025 a birnin Geneva dake kasar Switzerland a kwanakin baya, inda tawagar wakilan kasar Sin ta karbi bakuncin taron tattaunawa kan hadin gwiwar fasaha da cinikayya da sana’o’i masu kiyaye muhalli, inda aka gabatar da dabarun Sin na raya sana’o’i da fasaha masu kiyaye muhalli. A cikin jawabansu, masanan Sin sun yi amfani da ayyukan samar da makamashin da ake iya sake amfani da su, a kasashen Habasha da Sri Lanka da kuma aikin daidaita matsalar wutar lantarki na Afirka da sauransu a matsayin misalan dabarun Sin na hadin gwiwar fasaha. Fasahohin Sin sun kunshi fannnoni...
Kasar ta sha alwashin ci gaba da taimakawa kasashen nan guda uku na kawancen sahel da suka hada da Mali, Burkina faso da kuma Nijar a fannin tsaro. Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan ya gana da takwarorinsa na ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a birnin Moscow, yana mai cewa a shirye suke su taimaka domin bunƙasa alaƙar soji da ƙasashen. “Ina jaddada aniyar Moscow ta taimakawa domin samar da gamayyar rundunar soji ta yankin Sahel, tare da ƙarfafa dakarun soji da sauran jami’an tsaro na waɗannan ƙasashe uku ta hanyar ba su horo da makamai,” in ji Lavrov. Wannan bayanin ya fito ne a yayin taron manema labarai da bangarorin...
An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno. Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar 3 ga Afrilu, 2025, yayin da tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da na makarantar horas da ’yan sanda ta Mopol Gwoza da wasu sassan rundunar ’yan sanda ke sintiri a ƙafa. Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027 Sufeta Andrawus Musa da ke aiki a rundunar 6PMF a Maiduguri ya samu munanan raunuka...
Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu. A ranar Laraba ne, ya sanya harajin kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka da kuma karin haraji kan wasu manyan abokan kasuwancin kasar. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga kamfanonin Turai da su dakatar da shirin zuba jari a Amurka. “Ina ganin abin da ke da muhimmanci, shi ne a dakatar da saka hannun jarin da za a cikin ‘yan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko’ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta...
Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata, agogon kasar. A yayin bikin bayar da gudummawar kudi ga wadanda girgizar kasar ta shafa a birnin Nay Pyi Taw a yau Talata, shugaban majalisar gudanarwar kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, ya ce, mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar wacce ta afku a kasar a ranar Jumma’a, sun kai 2,719, yayin da wasu 4,521 suka jikkata, kana 441...
Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron. Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a kokarin da kwamitin ya yi na kiyaye muhalli. Dole ne a nace ga jagorancin da JKS ta bayar a wannan bangare, da ma sauke nauyin dake wuyan hukumomin wurare daban-daban karkashinta. Taron ya kuma jadadda cewa, ya kamata a kara karfin sa ido a siyasance, da mai da hankali kan yadda ake tabbatar da manufofi da tsare-tsaren kwamitin, ta yadda za a ba da tabbaci...
Rundunar ’Yan Sandan Kano, ta kama wani matashi bisa zargin kashe jami’in tsaron sa-kai a filin Idi yayin hawan sallah ƙarama. A cewar sanarwar da ’yan sanda suka fitar, matashin mai shekara 20, ya daɓa wa jami’in wuƙa yayin da yake aiki tare da tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi a ranar Lahadi. Farashin fetur ya ƙaru sakamakon hana Dangote mai a Naira Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi Haka kuma, wani jami’in sa-kai ma ya ji rauni kuma yana jinya a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano. Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi. A baya-bayan...
A wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina, mutane tara sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata. Hatsarin dai ya shafi wata babbar motar bas da ke ɗauke da fasinjoji 20. Aliyu Ma’aji, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa gaggawar tuki ne ya haifar da hatsarin, inda direban ya rasa ikon sarrafa motar. An Gabatar Da Motar Asibiti Ta Farko Mai ISO Na Matsayin Kasa Da Kasa A Hukumance Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC Haɗarin ya yi sanadin mutuwar mutane...
Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta daukaka tafiye-tafiye zuwa Syria zuwa mataki na 4 mafi girman inda aka gargadi, Amurkawa da kada su je kasar Siriya bisa kowane dalili. Ofishin jakadancin ya gargadi ‘yan kasar game da yiwuwar kai hari kan “ofisoshin jakadanci, kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin jama’a na Syria” a Damascus. Halin tsaro a Syria ya tabarbare bayan da kungiyoyin ‘yan ta’adda, karkashin jagorancin...
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya. Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su. An ce an kai gawarwakin mutanen goma sha hudu zuwa wani wuri da ba a sani ba. Ana gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya duk shekara a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce kasar Amurka ta yi amfani da batun kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje, kamar jerin sunayen kamfanoni, wajen sanyawa sauran sassa takunkumai bisa hujjar “barazana ga tsaron kasa, da kuma keta manufofin diplomassiyar Amurka”, wanda hakan ya zama wani babban mataki na nuna fin karfi. Guo ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum na yau Laraba, lokacin da yake tsokaci game da matakin Amurka na shigar da kamfanonin Sin fiye da goma, cikin jerin sunayen wadanda ta hana su shigar da hajoji Amurka, bisa jadawalin da ma’aikatar kasuwancin Amurka ta fitar. Game da hakan, Guo ya ce bangaren Sin zai dauki...
Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura. Yace, an sami gudunmawar kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah. A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu, Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati “A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi. “Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take. “Suna cikin guje...
A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa a dangantakar Sin da Amurka, ya dace da moriyar jama’ar kasashen biyu, da kuma fatan al’ummomin duniya baki daya. Dangane da rikicin Ukraine kuwa, Guo Jiakun ya ce a baya-bayan nan, kungiyar “Kawancen zaman lafiya” kan rikicin Ukraine ta gudanar da wani taro a birnin New York, domin tattauna halin da ake ciki game da...
An Zabi ‘Yan Kasar Zimbabwe Kuma Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympic
‘Yar kasar ta Zimbabwe Kiristy Coventry ta zama mace ta farko daga fito daga nahiyar Afirka,kuma mace da za ta rike shugabannin hukumar wasannin Olympic. An zabi Kirsty ‘yan shekaru 41 ne a yayin kada kuri’a ta sirri da aka yi da ‘yan takara 7 su ka yi gogayya. An yi zaben ne ne a yayin taron hukumar ta Olympic karo na 144, a birnin Costa, Navarino a kasar Greece a jiya 20 ga watan nan na Maris. Gabanin zabenta dai , Kirsty ta kasance wacce ta zama gwarzuwa ta iyo har sau biyu a wasannin Olympic. Za ta fara aikin nata ne na shugabancin hukumar wasannin Olympic a ranar 23 ga watan Yuni, da za ta gaji Thomas Bach...
Mazauna sun shiga zaman ɗar-ɗar a yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas. Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa fiye da motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar. Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu. Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar, Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu....
An shiga wata 11 da Gwamnatin Jihar Sakkwato ƙarƙashin Gwamna Ahmad Aliyu ta tuɓe rawanin wasu sarakuna da take ganin sun yi abin da bai dace ba na shiga siyasa. Tun bayan cire sarakunan, mutane sun yi tsammanin gwamnati za ta nada wadanda take muradi ne kai-tsaye domin su maye gurbin tubabbun sarakunan, amma shiru kamar ba wasu da ke jiran hukunci da sakayyar gwamnati mai ci. Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu Har yanzu gwamnati ba ta fito ta fadi dalilin rashin sake nada sababbin sarakunan ba domin ci gaba da wakilcin jama’a, ganin an bar garin kufai ba cikakken basarake. A baya da ma...
Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da kadarori na sama da Naira miliyan 50 suka salwanta sanadiyyar gobarar a cikin watan Fabrairun 2025 a Jihar Kano. Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar. Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Za a mayar da waɗanda Lakurawa suka raba da garuruwansu – Gwamnan Kebbi Ya ce, a cikin watan Fabrairu, 2025, hukumar kashe gobara ta jihar ta samu jimillar kiraye-kirayen lambar wayar kashe gobara 77, da lambar kiran neman ceto 11 da kuma ƙararrakin gobara na ƙarya uku. “Kimanin kadarori da gobara ta lalata a cikin watan Fabrairu sun kai darajar kuɗi N50,318,000 yayin da...
Majalisar dokokin jihar Kano ta wanke Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha. A yayin aikin tantance kwamishinonin, ya jaddada mahimmancin kiyaye babban tsarin ga birane da yankunan karkara. Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa. Adamu wanda a baya ya taba rike mukamin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tsare-Tsare Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), ya bayyana jin dadinsa ga majalisar a yayin zaman majalisar. Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore ya bukaci Adamu da ya kara samun nasarori a KNUPDA tare da yi masa fatan Alheri a sabon mukaminsa. Nadin Adamu ya yi daidai da...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450. Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga...
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin. “Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin da lokaci yake kara kurewa, tasirin haramcin yana karuwa a Gaza. Lazzarini ya kara da cewa “akwai hadarin komawa ga yanayin da muka fuskanta watannin da suka gabata, game da kara yaduwar yunwa a tsakanin mutanen zirin Gaza sakamakon matakan da Isra’ila take dauka. “Isra’ila” ta sanar da dakatar da isar da kayayyakin jin kai zuwa Gaza a ranar 2 ga Maris, tare da yin...
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
Aƙalla fasinjoji 16 suka ƙone ƙurmus, yayin da wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku ranar Talata a Jihar Ogun. Aminiya ta ruwaito cewa hadarin wanda ya rutsa da mota ɗaya kacal ya afku ne a gidan Buhari da ke kan titin Abeokuta zuwa Shagamu. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana ‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’ An bayyana cewa, hatsarin dai ya rutsa da wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba KJA 949 YJ, da misalin ƙarfe 1:00 na rana. Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar. Ta ce ba...
Iran Tayi Tir Da Shirin Shugaban Amurka Na Sake Tsugunar Da Al’ummar Gaza Kakakin gwamnatin kasar iran Fatime mohajerani ta yi tir da aniyar shugaban Amurka Donald trumph na kwashe alummar gaza zuwa wasu wurare, kuma ta biyyana shi a matsayin ci gaba da siyasar kisan kare dangi kan alumma falasdinu, Shugaban na Amurka Donald trump yayi wannan bayanin ne a taron manema labarai da yayi a fadar white hause da fira ministan isra’ila binjamin natanyaho a watan jiya, inda ya nuna aniyarsa ta kwashe alumma yankin gasa zuwa wasu kasashen larabawa. Tare da gina wajen shakatawa da babbar tashar jiragen ruwa a wajen. Shuwagabannin kasashen laraba wa da na musulmi sun jadda mastayinsu na amincewa da yancin falasdinawa tare...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye girmama kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik a fannoni 4. Firaminista Brown ya yi nuni da cewa, kasarsa ta tsibiran Cook ta dora muhimmanci ga girmamawar da Sin ta nuna mata, kasar Sin ta kiyaye yin hakan tun da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu....
Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 22 a hannun ’yan bindiga. An sace shi ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke garin Tsiga a Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari. Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta Maharan sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 250 kafin su sako shi. Sai dai bayan tattaunawa, an biya kuɗin fansa, wanda ya kai ga sakinsa. A halin yanzu, likitoci na kula da shi a wani asibiti da...
Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa. An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan kamar yadda majiyar ta tabbatar. ’Yan sanda sun ce jaririn ya mutu da misalin ƙarfe 7:45 na safiya...
A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu. Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da ingantacciyar murya guda ta kasashe masu tasowa. Wang ya bayyana a yayin taronsu cewa, kasar Sin a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwar cin moriyar juna tsakaninta da kasar Afirka ta kudu, da kara gaggauta bunkasuwar kasashen biyu, da kuma kara yin hadin gwiwa don kara daukaka murya da wakilci na kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka a cikin ajandar kasa da kasa. Wannan...
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Ƙungiyar Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan takwararta na ISWAP da dama yayin wani ƙazamin rikici da suka tafka ranar Juma’a a Ƙaramar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno. Bayanai sun ce an kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 yayin harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ƙarƙashin jagorancin wani ta’adda mai suna Bakoura. Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto Wata majiya ta shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, cewa yaƙin da aka fara tun da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Fabrairu ya haɗa da sansanonin ISWAP da ke Toumbun Gini...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin fito ko haraji na 100% na kayakin kasashensu dake shiga kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, maganar shugaban zai kara sabani a cikin kasashen kungiyar, ta BRICS wanda suke ganin Amurka ta mamaye al-amuran tattalin arziki a duniya. An kafa kungiyar BRICS ne a shekara 2009 kuma kasashen da suka fara kafata sune, Brazil, Russia, India, da kuma China, amma daga baya kungiyar ta kara fadada, inda kasashen Afirka ta kudu, Iran, Habasha, da kuma Hadaddiyar daular Larabawa. Bayan da kasar Rasha ta karbi shugabancin kungiyar na...
Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana a wannan Talata a yayin wani taron manema labarai cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan ma’abuta girman kai, da kuma shahidan bil’adama a kan mulkin mallaka”. Ya kara da cewa jana’izar za ta ci gaba da zaburar da mutane masu ‘yanci a duniya shekaru da dama masu zuwa.” Daher ya yi nuni da cewa bikin zai dauki...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu. A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan. Tunda farko...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu. Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen. Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025. A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa. Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun maslaha.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa da ta wakilai. A cikin wasikar da aka karanta yayin zaman majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce an sami karin kudin ne sakamakon karin kudaden shigar da hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta samu na Naira tiriliyan 1.4, yayin da hukumar hana fasakwabri ta kasa ta tara Naira tiriliyan 1.2, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka tara. A don...
Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan hanyarsu daga Barikin Myoung da ke yankin Marocco a Shomolu. Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa a Adamawa Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Waɗanda suka samu raunuka suna jinya a asibitin sojojin Nijeriya da ke Yaba, yayin da aka ajiye gawarwakin sojojin da suka rasu a ɗakin ajiye gawa a asibitin. Hedikwatar Runduna ta 81 ta Sojojin Nijeriya,...
Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin sansanin Sojojin. Wani Soja da ya tsira daga harin ya bayyana cewa, “Jini ne ko’ina. Na tsira ne kawai saboda ina baya.” Mun Kashe Ƴan Ta’adda Sama Da 70, Kafin Mu Yi Rashin 22 – Sojoji Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara Sojan (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a...
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin yin aure a wajen wani taro ba tare da amincewar iyayensu ba. A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, matasan sun yi auren ne a wajen shaƙatawa bayan wani da ba su da alaƙa da shi ya biya sadakin amaryar. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya Ya bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa ƙa’idar Musulunci kuma ba za a yarda da irin wannan lamarin ya ci gaba da faruwa a Kano ba. “Muna sanar da cewa mun kama ma’auratan, kuma za mu ci gaba da bincike don kama abokansu da duk wanda...
Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024. Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata. Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye. Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21...
Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe. An gurfanar da masoyan da suka kai wa malami hari a Kano Kotu ta ɗaure matashi shekara 2 kan satar wayoyi a Kano Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wasu nakiyoyi da wani mutum ya ɓoye a wajen domin aikin haƙar ma’adinai. Lamarin ya yi sanadin lalacewar gidaje kusan 12 a yankin, inda ya jefa al’umma cikin tashin hankali. Fatima Sadauki ta rasa ranta...
An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 18 sakamakon hatsarin wata tankar mai da ta yi bindiga a Jihar Enugu. Alƙaluman da mahukunta suka fitar ya nuna cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31 ciki har da mutum 10 da suka samu raunuka daban-daban yayin da aka ceto wasu uku da suka tsallake rijiya da baya sai kuma mutum 18 ɗin da suka ƙone ƙurmus. An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila Hakan na ƙunshe cikin sanarwa da mai magana da yawun rundunar hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa reshen Jihar Enugu, Olusegun Ogungbemide ya fitar da yammacin ranar Asabar. Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin wanda ya...