Aminiya:
2025-09-17@23:28:24 GMT

Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 a Borno

Published: 16th, February 2025 GMT

Ƙungiyar Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan takwararta na ISWAP da dama yayin wani ƙazamin rikici da suka tafka ranar Juma’a a Ƙaramar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno.

Bayanai sun ce an kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 yayin harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ƙarƙashin jagorancin wani ta’adda mai suna Bakoura.

Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto

Wata majiya ta shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, cewa yaƙin da aka fara tun da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Fabrairu ya haɗa da sansanonin ISWAP da ke Toumbun Gini da Toumbun Ali.

Mayaƙan Boko Haram, waɗanda rahotanni suka ce sun ragargaji sansanin na ISWAP  a wani ƙazamin faɗan ya ɗauki tsawon yini guda ana gwabzawa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kashe wasu manyan kwamandojin ISWAP musamman ‘yan kabilar Buduma a yayin harin.

A cewar majiyar, daga cikin ’yan ta’addan ISWAP da aka kashe sun haɗa da wasu manyan-manyan kwamandojin da ake kyautata zaton sun taka rawa wajen kisan kiyashin da aka yi wa manoma da dama a Kukawa a tsakanin 12 zuwa 13 ga watan Janairu na wannan shekara ta 2025.

Majiyar ta ce mayakan Boko Haram sun yi wa kungiyar ta ISWAP asara mai yawa bayan da suka mamaye sansaninsu, inda suka ƙwace makamai da kayan aiki.

A wani yunƙuri na faɗaɗa hare-haren nasu, an ce mayaƙan na Boko Haram daga tsibirin Bokorram sun ɗaura ɗamara domin tunkarar mayaƙan ISWAP a Gemu da Mallam Karamti.

Zagazola ya bayyana cewa akwai yiwuwar ana gab da samun ƙarin fadace-fadace, musamman a Ƙaramar Hukumar Kukawa, yayin da mayaƙan Boko Haram ke ƙara ƙaimi wajen yaƙar ISWAP.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP jihar Borno da mayaƙan

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

 

Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar