Shugaba Tinubu Ya Kara Yawan Kudi A Kudirin Kasafin Bana Zuwa Naira Tiriliyan 54.2
Published: 6th, February 2025 GMT
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa da ta wakilai.
A cikin wasikar da aka karanta yayin zaman majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce an sami karin kudin ne sakamakon karin kudaden shigar da hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta samu na Naira tiriliyan 1.4, yayin da hukumar hana fasakwabri ta kasa ta tara Naira tiriliyan 1.2, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka tara.
A don haka shugaban majalisar ya mika bukatar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa domin tantancewa cikin gaggawa, inda ya tabbatar da cewa za a kammala nazarin kasafin kudin kafin karshen wata.
Daga Bashir Meyere
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Naira tiriliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.
Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.
A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.
Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.
Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.
“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.
Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.