Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA
Published: 29th, January 2025 GMT
Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata.
Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye.
Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21 cikin mutane 46 da ake zargi da aikata laifukan a gaban kuliya domin yanke musu hukuncin da ya dace da su, yayin da ake ci gaba da shari’ar 85 a Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu.
Kwamandan ya ce hukumar ta bayar da shawarwari ga mutane 219 da suka dogara da muggan kwayoyi tare da gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a cikin al’umma, makarantu, ƙungiyoyin addini, da wuraren aiki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Yobe
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare.
Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata.
Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni.
A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kada kuri’ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta’addanci.
Majalisar dokokin Ghana ma ta kada kuri’ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023.
Wadanne kasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa?
Kasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka yi hakan a 2021.
Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta ce jimillar mutum 1,518 aka zartar wa hukuncin kisa a duniya, inda aka samu karin kashi 32 cikin 100. Sai dai ta ce hakikanin adadin ya zarta haka sosai saboda yadda kasashe ke boye batun.
Bayan China, Amnesty ta ce kasashen da suka fi kashe mutane a 2024 su ne Iran (972), da Saudiyya (345), da kuma Iraki (63). Su ne suka zartar da kashi 91 cikin 100 na duka kasashen duniya.
Ana yi wa China kallon kasar da ta zarta kowacce aiwatar da hukuncin kisa a duniya, amma ba a sanin hakikanin adadin mutanen, saboda gwamnati ba ta bayyana su.
Kasashen Koriya ta Arewa da Bietnam ma na amfani da hukuncin kisa sosai amma ba su bayyanawa a hukumance.
Amnesty ta ce ta samu rahoton zartar da hukuncin kisa a bainar jama’a akalla sau uku a 2022 a Iran.
Ta ce Iran din ta kashe akalla mutum biyar saboda laifukan da suka aikata a lokacin da suke kasa da shekara 18 da haihuwa.
Saudiyya ta kashe mutane mafiya yawa a duniya a 2022 cikin shekara 30.
Kasashe biyar; Bahrain, Comoros, Laos, Nijar, Koriya ta Kudu – su ne suka yanke wa mutane hukuncin kisa a 2022 bayan sun shafe tsawon lokaci ba su yi amfani da shi ba.
Duk da cewa adadin na raguwa a Amurka, amma ya karu a 2021, amma duk da haka ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da shekarar 1999.
Mutum nawa aka kashe saboda safarar miyagun kwayoyi?
Amnesty International ta ce sama da kashi 40 cikin 100 na mutanen da aka zartar wa hukuncin kisa a 2024 saboda laifukan ta’ammali da miyagun kwayoyi ne.
A 2022, an kashe mutum 325 saboda laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi. Kasashen da suka aikata hakan su ne:Iran 255 Saudiyya – 57 – Singapore – 11
A 2023, Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan mace ta farko cikin shekara 20. A 2018 aka kama Saridewi Djaman da laifin safarar hodar ibilis.
Ta yaya kasashe ke zartar da hukuncin kisa?
Saudiyya ce kadai ta zayyana fille kai a matsayin hanyar aiwatar da hukuncin kisa a 2022.
Sauran hanyoyin sun hada da rataya, da allura mai guba, da kuma harbi da bindiga.
A watan Janairun 2024 jihar Alabama ta Amurka ta zartar wa wani mai laifin kisa Kenneth Smith hukuncin kisa ta hanyar amfani da iskar nitrogen gas.
Ya zama mutum na farko a duniya da aka zartar wa hukuncin ta irin wannan hanyar, a cewar cibiyar Death Penalty Information Center da ke Amurka.
Lauyoyin Mista Smiths sun ce salon da ba a taba gwadawa ba kafinsa “rashin imani ne”.
Alabama da wasu jihohin Amurka biyu ne suka amince da amfani da iskar gas din saboda kwayoyin da ake amfani da su wajen yi wa mutum allura mai guba ba sa samuwa cikin sauki.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA