2025-09-17@21:53:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 142
«Yarin kasar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin siyasar waje na majalsar shawarar musulunci ta Iran ya gabatar da rahoto akan hali na karshe da ake ciki dangane da batun tattaunawa da Amurka. Arakci ya kuma fadawa kwamitin cewa; Mu ma’abota diflomasiyya da tattaunawa ne, amma za mu tattauna da Amurka ne ba kai tsaye ba,kuma duk da hakan ma har yanzu ba mu...
A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri. Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL A jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya kasance wani babban mataki na bude kasuwar kasar Sin ga kwayoyi dangin gyada na kasar Zambiya, wanda zai amfanar da manoman kasar nan gaba ba da jimawa ba. Ya kara da cewa, baya ga wannan yarjejeniyar...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara. Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
Jakadan kasar Sin a kasar Laberiya Yin Chengwu da ministar harkokin wajen kasar Laberiya Sara Nyanti, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha, a madadin gwamnatocin kasashensu, jiya Juma’a a Monrovia, babban birnin kasar Laberiya. Minista Nyanti ta godewa gwamnatin kasar Sin bisa gagarumin goyon bayan da take bai wa kasar Laberiya, ta kuma ce yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha da bangarorin biyu suka rattabawa hannu, za ta taimaka wa kasar Laberiya wajen cimma muradin raya kasa na ARREST. Ta ce Laberiya na son yin amfani da wannan dama wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin raya kasa, da tattalin arziki, da cinikayya, gami da zuba jari....
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai da za su taimaka wajen kamo sauran fursunonin da suka tsere. Haka kuma, an buƙaci dangin waɗanda suka tsere da su mika kansu ga hukuma domin guje wa hukunci mai tsanani. Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun irin wannan matsala ba, domin a baya an samu fursunoni sun tsere daga gidajen yari daban-daban a Nijeriya. Hakan na nuni da buƙatar ƙara tsaurara matakan tsaro a gidajen gyaran hali domin hana faruwar irin haka a gaba. A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin kamo sauran fursunonin da suka tsere domin...
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba. Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga Owena Ijesha a karamar hukumar Oriade ta jihar Osun, daurin sa’o’i 300 (dari uku) da yiwa al’ummar hidima na tsawon sa’o’i biyar a kowace rana ba tare da zabin biyan tara ba, bayan da ya same shi da laifin aikata laifukan da suka shafi yanar gizo wato walawala ko yahoo boyi. Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC...
Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa, daga nan aka bai wa iyalansa gawarsa domin yin jana’iza. Kakakin ‘yansandan Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce suna samun labarin lamarin, jami’ansu suka fara bincike, musamman a wajen POS da ke kusa da inda aka nemi a biya kuɗin fansar. A yayin binciken, sun kama wani matashi mai shekara 23, Rabi’u Muhammadu daga ƙauyen Leka, wanda lambar wayarsa aka yi amfani da ita wajen kira mahaifin yaron. Sun kuma gano asusun bankin da aka bayar don a biya kuɗin fansar. Da aka tambayi Rabi’u, ya bayyana cewa Samson Ozoichikel, mai shekara 35 daga ƙauyen Sade, shi ne ya shirya yin garkuwa da yaron. Sannan ya ambaci wasu matasa biyu, Muhammad Sani (Jingi) mai...
A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya ba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen murmurnar wannan nasara. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da cewa, Iran a ko yauce tana fatan zaman lafiya a kasashe makobata da kasar sabuda dalilai da dama daga ciki Iran tana amfani da kasashe makobta don kyautata yanayin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu. Firai ministan kasar Armenia Nikol Pashjinyan a zantawarsa ta wayar tarko da shugaban kasar Iran ya ce: Gwamnatinsa zata yi kokarin ganin an aiwatar da yarjeniyar daki daki kamar yadda...
Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta fara atisayen tantance gwanintar harbi na shekarar 2025 daga ranar Litinin 17 zuwa 19 ga watan Maris a Barikin Yar Gaba da ke Dutse, Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 26 Armoured Brigade, Laftanar Uzoma Egwu-Ukpai, ya sanyawa hannu aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. Sanarwar ta bayyana cewa, atisayen tantance gwanintar harbi ana yi ne domin auna ƙwarewar jami’an soji wajen sarrafa makamai da ingancin harbinsu. Laftanar Uzoma Ukpai ya shawarci al’umma da kada su firgita yayin atisayen idan suka ga sojoji suna kai-komo ko suka ji karar harbi, musamman mutanen da ke zaune...
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe bana a Kano — Nalako NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko. Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba...
Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha. Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018,...

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai
Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan. “NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da tashoshi sama da ɗari a faɗin ƙasar nan, tana isar da shirye-shiryen ta ga sama da mutane miliyan 200. “Hakan ya sa muke da buƙatar amfani da wannan haɗin gwiwa don musayar bayanai da fasaha, tare da amfana da juna.” Ministan ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun haɗa da musayar bayanai, shirye-shirye, da fasaha domin inganta ayyukan gidajen watsa labarai na Nijeriya tare da...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada kudurin Najeriya na aiwatar da cikakken yarjejeniyar biyu da aka kulla tsakanin China Media Group da manyan gidajen watsa labarai na gwamnati a Najeriya – Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) a taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a Beijing. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Jakadan Sin a Najeriya, Mista Yu Dunhai, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa a yau alhamis. Ya ce, wadannan yarjejeniyoyi sun ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin watsa labarai da sadarwa, domin inganta dangantakar Najeriya da Sin. Ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun shafi...

Hamas Ta Ce Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ne Kadai Za Ta Kubutar Da Fursinonin Yahudawa Daga Hannun Kungiyar
Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa, akwai alamun Natanyahu Firai ministan HKI yana son ya sake komawa yaki a Gaza. Hamdan ya ce, kafin haka gwamnatin HKI ta dakatar da aikin aiwatar da yarjeniyar da suka kulla da ita, yana son ya yi watsi da ita, sannan ya bukaci a sake tattaunawa kan sauran abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar. Jami’in na Hamas y...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘ba zamu tsawaita kashi na farko na yarjeniyar ba, haka ma ba za mu amince da gabatar da sauye –sauye a cikin yarjeniyar ba. Mardawi yace HKI za ta karbi fursinonin da suka rage a hannun Hamas kadai ne, ta hanyar ko tsarin da yarjeniyar ta amince da shi. Ya ce: Benyamin Natanyahu yana, cikin dimwa...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce ake wa laƙabi da Masu Gida ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Wasan wanda aka fara da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ya na daga cikin manyan wasanni masu zafi da ke ɗaukar hankalin masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Nijeriya. Kano Pillars Ta Dakatar Da Kocinta Na Tsawon Makonni Uku Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi? Rabiu Ali da Jerry Alex ne su ka jefa wa Pillars ƙwallayensu biyu a wasan, da wannan sakamakon Sai Masu Gida su ka koma matsayi na 4 akan teburin gasar Firimiyar Nijeriya. Ƙungiyar ta Kano ta dakatar da kocinta Usman...
Maryam Abubakar sabuwar jaruma ce a Masana’antar Kannywood ’yar Hajiya Hauwa Garba da aka fi sani da ’Yar Auta ko Sabirar Gidan Badamasi. A zantawarta da Aminiya ta ce babban burinta shi ne ta yi fice da suna kamar yadda mahaifiyarta Hajiya Hauwa Garba ta yi: Mene ne takaitaccen tarihinki? Sunana Maryam Abubakar wadda aka fi sani da Maryam Intete. An haife ni a Najeriya na yi makarantar firamare a Kawo (Kawo ta Kano), na yi karamar sakandare a Jogana, na kuma yi makarantar Unguwar Badawa a matakin Babbar Sakandare daga nan sai na tafi Saudiyya, inda a can na kara karatu. Yanzu ina da shekara 22 a duniya. Yaya aka yi kika tsinci kanki a Masana’antar Kannywood? Eh, ina...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji. Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin da Netanyahu ya dauka na dakatar shigar da kayan agaji cikin Gaza, wata tsokana ce, kuma laifin yaki ne sannan uwa uba keta yarjejeniyar datakar da wuta da musayar fursunoni ce. Bugu da kari, kungiyar ta Hamas ta ce bukatar da Netanyahu ya gabatar na tsawaita zango na farko na yarjejeniyar, wani yunkuri ne na gujewa aiwatar da ita kanta yarjejeniyar. Haka nan kuma Hamas...
Wani jami’in ya ce yarjejejeniyar za ta ba da dama ga Zelenskyy da Trump su tattauna batun ci gaba da bayar da tallafin soji ga Ukraine, dalilin da ya sa Kyib ke son kammala yarjejeniyar. Trump ya kwatanta wannan matsaya da aka cimma a matsayin “babbar yarjejeniyar,” wacce za ta kai ta tiriliyan na daloli. A wani labarin kuma, Kasar Ukraine ta bayyana cewar hare-haren da Rasha ta kai wa garuruwan dake kusa da filin daga a gabashin kasar sun hallaka akalla mutum 5 tare da raunata wasu 8 ‘yan sa’o’i bayan wani mummunana harin jirgi mara matuki kusa da birnin Kyib. Gagarumin ruwan wutar da jiragen saman Rasha marasa matuka suka kai cikin dare sun hallaka mutum 2 a...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. » Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga...
A wani mataki na nuna kara kusanci tsakanin kasashen Somaliya da Habasha, shugaban kasar Habasha Abiy Ahmed ya ziyarci Somaliya. A Shekara guda da ta wuce, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna. Bayan shafe shekara guda ana zaman dar-dar, a watan Disambar da ya gabata ne a kasar Turkiya, kasashen biyu suka sake kulla huldar jakadanci ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar Ankara. Shugaban kasar Somaliya Hassan Cheikh Mohamoud ya gabatar a matsayin “mahimmin mataki” na daidaita huldar dake tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar da yammacin jiya Alhamis, an bayyana cewa: Habasha da Somaliya kasashe ne masu dogaro da juna da makoma guda da kuma ra’ayi daya na tabbatar da...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da aikin soji a yammacin gabar kogin Jordan. Fu Cong ya bayyana cewa, dole ne mulkin Gaza bayan yakin ya bi ka’idar “Falasdinawa su yi mulkin Falasdinu”, kuma ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga sake gina Gaza. Kana kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su kara himma wajen kira ga...
Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025. Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Amma a wani al’amari mai ban mamaki, sai aka hangi wata tawaga daga kamfanin na Saudiyya a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Muhammad Hassan, ta...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu tsakanin Isra’ila da Hamas. Tun dai bayan cimma yarjejeniyar Hamas ta saki Isra’ilawa 22, a yayin da ita kuwa Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa sama da 1,100. A karshen matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta, za a yi musayar fursunonin Falasdinawa 1,900 da aka yi garkuwa da ‘yan Isra’ila su 33 da suka hada da matattu takwas. Ana dai ci gaba...
Shugabannin kasashen Larabawa sun tattauna kan batun Gaza dama halin da ake ciki yankin. Bisa gayyatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, an gudanar da taron ‘yan uwantaka na yau da kullun a birnin Riyadh a ranar Juma’a inji kamfanion dilancin labaren kasar na SPA. Taron ya samu halartar sarki Abdullah II na Jordan, da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da shugaban kasar Masar, da Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa hyan, da Sarkin Kuwait Sheikh Meshal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, da kuma Yarima mai jiran gado kuma firaministan kasar Bahrain Yarima Salman bin Hamad Al Khalifa. Taron ya ba da damar tuntubar juna kan batutuwa daban-daban na shiyya-shiyya da...
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI. Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron su da tawagar kasar ta Amurka a yau. Ya kuma kara da cewa abubuwan da HKI ta sa a gaba sun hada da ganin kasar Iran bata mallaki makaman Nukliya ba, da shafe kungiyar hamas, sakin fursinoni a hannun Hamasa da kuma samar da huldar jakadanci da kasar Saudiya. Wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu manya manyan jami’an sojojin kasar suna tunanin dakatar da...

Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Da Hamas Sun Yi Tirsa Da HKI Kan Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Ofer
Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya. Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.
Jiragen Yakin HKI Sun kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a kudancin kasar Lebanon, wanda hakan keta yarjeniyar tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu. Kamafanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kusa da kogin Litan, Yohmor Al-shaqif da kuma Zoutr Al-sharqiyya, da kuma Deir Siryan, zibqin da Yater. Babu rahoto kan wadanda suka ji rauni ko suka rasa rayukansu. Gwamnatin HKI ta bayyana cewa ta kai hari ne kan rumbunann ajiyar makamai na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon. Duk ntare da tsagaita wuta tsakanin Hizbullah da kuma HKI a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, bayan watanni 14 da fafatawa, sojojin HKI sun ci gaba da kai...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata a fara ranar Litinin, ke ja da baya ba kamar yadda aka fara ba inji shi. Da yake zargin Isra’ila da “jinkiri” wajen aiwatar da kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta na makonni shida, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, Bassem Naim ya yi gargadin cewa wannan lamarin ya jefa yarjejeniyar cikin hadari kuma zata iya haifar da rugujewarta....

“Yar Sakon Amurka A Kasar Lebanon Morgan Ortagus Tana Shan Mayar Da Martani Daga Bangarori Mabanbanta
Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar. Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba. Kungiyar malaman addinin musulunci ta fitar da bayani da a ciki ta ce; “Furucin mataimakin manzon Amurka a gabas ta tsakiya, Morgan Ortagus wacce ‘yar sahayoniya ce,tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Lebanon wanda ya tsallake ka’idojin aikin diplomasiyya.” Ita ma gwamnatin kasar ta Lebanon ta fitar da bayani tana mai cewa abinda Ortugas din ta furta, ra’ayinta ne, bai shafi gwamnatin Lebanon ba. Shi kuwa...
Kotu ta ba da umarnin tsare tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje. Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf kan zargin almundahana. A safiyar Litinin ne EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, inda bayan an karanta masa tuhumar da ake masa ya musanta aikata laifin. Daga nan ne lauyansa O.I Habeeb, ya buƙaci umarnin kotu na tsare shi a ofisoshin EFCC zuwa lokacin zai shigar da buƙatar beli. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe...
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa ido da masu shiga tsakani don dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” in ji shi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin dazu. Sheik Qasem ya ce kungiyar Hizbullah na taka-tsan-tsan don bai wa gwamnatin Lebanon damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Faransa da Amurka suka shiga tsakani...
A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...
Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano Yarjejeniyar tsagaita wutar an ƙulla ta ne don bayar da damar musayar fursunonin da Hamas ke riƙe da su da kuma waɗanda ke tsare a Isra’ila. Sai dai wannan matakin ba zato ba tsammani ya haifar da rashin tabbas kan ci...
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan. Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon. “Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,”...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon. Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar...
Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...