Aminiya:
2025-11-03@07:19:43 GMT

Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta

Published: 2nd, March 2025 GMT

Maryam Abubakar sabuwar jaruma ce a Masana’antar Kannywood ’yar Hajiya Hauwa Garba da aka fi sani da ’Yar Auta ko Sabirar Gidan Badamasi.

A zantawarta da Aminiya ta ce babban burinta shi ne ta yi fice da suna kamar yadda mahaifiyarta Hajiya Hauwa Garba ta yi:

Mene ne takaitaccen tarihinki?

Sunana Maryam Abubakar wadda aka fi sani da Maryam Intete.

An haife ni a Najeriya na yi makarantar firamare a Kawo (Kawo ta Kano), na yi karamar sakandare a Jogana, na kuma yi makarantar Unguwar Badawa a matakin Babbar Sakandare daga nan sai na tafi Saudiyya, inda a can na kara karatu. Yanzu ina da shekara 22 a duniya.

Yaya aka yi kika tsinci kanki a Masana’antar Kannywood?

Eh, ina harkar fim yanzu kuma zan iya cewa ina cikin wadanda suka fara tunda kuruciyarsu.

Na taso na ga yadda mahaifiyata take yi ne, shi ya sa ni ma na ce ina da sha’awar shiga harkar don in bayar da tawa gudunmawar.

Wane buri kike da shi tun kina karama?

Insha Allah zan ci gaba da karatuna don yanzu haka ina kokari ci gaba da karatu domin kwarewa a wani fannin daban bayan fim.

Shin kin haɗu da wasu matsaloli da kika fara fim?

Gaskiya ban haɗu da wata matsala ba, don ina yin wasu ’yan abubuwa haka ina ɗora wa a shafina na TikTok, wasu na yi min magana suna cewa gara ki hakura da fim ki yi aure. Ni kuma sai in ce musu aure lokaci ne insha Allahu zan yi idan lokacin ya zo.

Waɗanne abubuwa kike ganin ba haka kika zata ba a Kannywood?

Gaskiya idan zan iya bayar da shawara, idan mutum bai iya abu ba, yana da kyau ka zaunar da shi ka fahimtar da shi ko kuma idan an kawo maka kushe misali a ce idan ka zauna da mutum ka ji mene ne dalili?

Kada ka yanke hukunci nan take ba tare da jin ta bakinsa ba. Yanke hukunci lokaci daya babu kyau.

Mu ’yan Adam ne muna saba wa junanmu wani abin ma ai ba ka yi ba sai a je wajen ubangidanka a ce ka yi wani abu alhali ba ka yi ba. To wannan ne gaskiya nake ba manyanmu shawara su rika jin ta bakinmu idan an kawo musu kushe.

Mene ne burinki a masana’antar?

Ina fatar abubuwa da yawa. Na farko ina so in ga na yi suna kamar yadda mahaifiyata Hajiya Hauwa Garba ta yi.

Na biyu ina so in shahara a duniyar fim baki ɗaya.

Wane fim kika fi son fitowa a ciki?

Yanzu ka ga da Chamama da Barkwanci duk sun haɗu ba a gane kowane ɓangaren.

Ina hadawa ne, amma ba na yin kwalliya irin ta mahaifiyata.

A cikin finafinan da kika fito, wanne ya fi burge ki?

Akalla dai na yi finafinai da dama, amma uku sun fi fice saboda ban dade ba a masana’antar. Amma a ciki wanda ya fi burge ni shi ne Naja’atu.

Wadanne nasarori kika samu?

AlhdulilLahi na samu nasarori da dama. A ce mutum ya yi fice a san shi ma ai wani abu ne.

Nasarata ta farko da na samu zuwa na aikin Saudiyya na ga mutane da yawa sun san ni da suka gan ni, na ji matukar farin cikin yadda suke nuna ni. Wannan kadai ma nasara ce.

Wasu za su so sanin dalilin da ya sa kika haɗa sana’a da mahaifiyarki?

Ban ga abin mamaki ba, saboda tun ina yarinya mahaifiyata take harkar fim, wanda hakan ya sa na saba ganin yadda take yi. Wannan ya sa ko da na shigo ban sha wahala ba.

Kin fuskanci ƙalubale ko turjiya ta wajen mahaifi kan wannan harka?

Eh, mahaifina da farko ya ce min ba ya son harkar fim, ya fi son in yi aure, amma da na zauna muka fahimci juna da shi sai ya ce min shi ke nan babu damuwa Allah Ya taimaka.

Sakonki ga masu bibiyar finafinanki da masoyanki?

To sakona gare su shi ne su ci gaba da yi min addu’a Ubangiji Allah Ya kai ni gabar da nake son kaiwa. Ina godiya gare su. Allah Ya bar zumunci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hauwa Garba Maryam Abubakar

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Ga yadda ake hada Fab biskit (wani irin biskit mai dandanon madara da sukari, mai taushi da dan kamshi kamar na “shortbread”).

Da farko za ki samu roba haka sai ki zuba sukari da Bota, ki cakuda su da cokali ko maburkaki har sai sun hade jikinsu kuma sun yi laushi. Sannan ki fasa kwai a ciki, ki zuba filaibo, ki ci gaba da cakudawa.

A wani kwano ko robar daban, ki hada fulawa, bakin fauda, madara, da dan gishiri. Sai ki zuba wannan hadin a cikin wancan kayan da kika fara hadawa. Ki gauraya su sosai har sai ya zama kullu mai laushi, ba mai taurin gaske ba.

Idan ya yi tauri, ki kara dan madarar ruwa ko dan mai ko buta. Ki baza kullun a faffadan tire, ki yi masa rolling ki yanka da cutter ko roba da siffar da kike so. Ki sanya a cikin tanderu mai dan zafi (180°C) na minti 15–20 har sai ya fara yin kalar kasa kasa).

Ki fitar ki barshi ya huce kafin ki adana.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su November 2, 2025 Labarai Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna November 2, 2025 Manyan Labarai Wadi Al-Salam: Maƙabartar Musulmai Mafi Girma A Duniya November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
  • Allah Ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa
  • Yadda Za Ku Hada Fab Biskit
  • Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci
  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai