Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai
Published: 7th, March 2025 GMT
Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan.
“NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da tashoshi sama da ɗari a faɗin ƙasar nan, tana isar da shirye-shiryen ta ga sama da mutane miliyan 200.
“Hakan ya sa muke da buƙatar amfani da wannan haɗin gwiwa don musayar bayanai da fasaha, tare da amfana da juna.”
Ministan ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun haɗa da musayar bayanai, shirye-shirye, da fasaha domin inganta ayyukan gidajen watsa labarai na Nijeriya tare da ƙarfafa aikin jarida bisa kyawawan ƙa’idojin duniya.
Haka nan, ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa da Chana domin yaƙi da labaran ƙarya da yaudara ta hanyar yaɗa bayanai marasa tushe.
Ya ce: “Labaran ƙarya da yaudara manyan barazana ne ga duniya. Mun san cewa ƙasar Chana tana da matuƙar damuwa game da wannan batu, haka nan kuma Nijeriya.
“Wannan ba matsala ce da ta shafi ƙasashen mu biyu kawai ba, matsala ce ta duniya baki ɗaya. Saboda haka, muna son yin aiki tare da ƙasar Chana domin yaƙi da labaran bogi da yaɗa ingantattun bayanai da za su amfani al’umma.”
Idris ya tabbatar wa jakaden na Chana cewa Nijeriya na kiyaye ‘yancin ‘yan jarida, wanda wani muhimmin ɓangare ne na jajircewar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya.
Ya ce: “A Nijeriya, ‘yan jarida suna da ‘yancin aikin su. Duk da yake akwai matsaloli a wasu lokuta, muna aiki a kai a kai domin gyara su. Nijeriya tana da ‘yancin watsa labarai mai yawa, kuma muna son ci gaba da hakan.”
Har ila yau, ya buƙaci kamfanonin ƙasar Chana da su yi amfani da damar da manufofin Tinubu ke samarwa wajen zuba jari a Nijeriya.
A nasa jawabin, Jakada Yu Dunhai ya jaddada aniyar sa ta ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da Chana, tare da yaba wa Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Ƙasa Tinubu.
Ya ce: “Ina da sa’a sosai kasancewa jakada a lokacin da Shugaban Ƙasa Tinubu yake aiwatar da Ajandar Sabunta Fata don ƙarfafa Nijeriya. Haka nan, a ƙasar Chana, Shugaba Xi Jinping yana jagorantar ƙasar zuwa cigaba ta hanyar sauye-sauyen zamani na ƙasar Chana.”
Jakaden ya bayyana cewa a taron FOCAC da ya gabata a Beijing, Shugabannin Nijeriya da Chana sun amince da ɗaukaka alaƙar ƙasashen zuwa matakin haɗin gwiwar dabarun cigaba.
Haka nan, ya nuna muhimmancin aiwatar da yarjejeniyoyin tsakanin NTA, FRCN, da China Media Group, yana mai cewa kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma.
Ya kuma yaba da yadda kafofin watsa labarai na Nijeriya ke gudanar da ayyukan su bisa gaskiya, daidaito, da riƙon amana.
A ɓangaren zuba jari, jakaden ya bayyana cewa Shugaba Xi Jinping ya ware dala biliyan 50 ($50bn) domin zuba jari a Afrika cikin shekaru uku masu zuwa a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyoyin da aka cimma a taron FOCAC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a ƙasar Chana watsa labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa.
A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Pulling Out Parade ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta. Wannan biki na nuni da kammala aikin Soja a matakin ƙoli, kuma yana ɗaya daga cikin manyan al’adun da ake yi wa manyan jami’an da suka yi aiki da ƙwarewa da sadaukarwa.
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP Kasashen Afirka Biyar Da Suka Fi Karfin SojiJanar Musa ya yi aikin Soja na tsawon shekaru masu yawa, kuma ya yi shugabanci a matsayin Shugaban Tsaron Ƙasa daga Yuni 2023 zuwa Oktoba 2025. A wannan lokaci, ya jagoranci manyan hare-haren yaƙi da ta’addanci tare da ƙarfafa hulɗar haɗin gwuiwa tsakanin sassan Sojojin Nijeriya.
A ranar 24 ga Oktoba, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sabon tsarin jagorancin rundunar Soja, inda ya naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon Shugaban Tsaro, wanda hakan ya kawo ƙarshen wa’adin Janar Musa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA