“Yar Sakon Amurka A Kasar Lebanon Morgan Ortagus Tana Shan Mayar Da Martani Daga Bangarori Mabanbanta
Published: 7th, February 2025 GMT
Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar.
Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba.
Kungiyar malaman addinin musulunci ta fitar da bayani da a ciki ta ce; “Furucin mataimakin manzon Amurka a gabas ta tsakiya, Morgan Ortagus wacce ‘yar sahayoniya ce,tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Lebanon wanda ya tsallake ka’idojin aikin diplomasiyya.
Ita ma gwamnatin kasar ta Lebanon ta fitar da bayani tana mai cewa abinda Ortugas din ta furta, ra’ayinta ne, bai shafi gwamnatin Lebanon ba.
Shi kuwa shugaban kungiyar ‘yan majalisar dokokin Lebanon masu wakiltar Hizbullah, Muhammad Ra’ad ya bayyana furucin na ‘yar sakon Amurkan da cewa; Hikidi ne da kuma tsoma baki a harkokin cikin gidan Lebanon.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe.
Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar.
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan AmurkaA cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa.
DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da su taimaka da bayanai da za su taimaka wajen sake kama shi.
Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su kusanci fursunan da ya tsere, domin hakan na iya zama hatsari.
“Domin kare lafiyarku, idan kuka ga wani da kuke zargi shi ne, ku sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa ko gidan gyaran hali, ko kuma ku kira lambar 08038452982,” in ji sanarwar.