Bukatar Inganta Rayuwar Daurarru A Gidajen Yarin Kasar Nan
Published: 2nd, May 2025 GMT
Wannan batun ya nuna a zahii na irin dimbin cinkoson da ake da shi, a Gidajen Gyaran Halin kasar, mussamn duba da cewa, Gidan na nan yadda suke kamar jiya iyu, tun bayan samun ‘yancin Nijeriya daga Turwan mulkin mallaka.
Ga masu kai ziyara Gidajen, babu abinda suke gani, illa yanayi na irin lalacewar da Gidajen ke ciki, musamman duba da rashin tanadar kayan duba lafiyar masu zaman Jarun da yanayin lalacewar da Gidajen suke cikin, wanda hakan ya nuna cewa, ana kawai cin zarafin tsarin Shari;ar kasar ne, musamman ganin yadda ake ci gaba da take ‘yancin Bil’adama.
Idan za a iya tunawa Kwamtin Majalisar Dattawa da ke sanya ido kan kula da harkokin cikin gida, a watan Okutobar 2021, ya amince da kara yawan abincin da ake ciyar da mazu zaman Jarun na kowacce rana, daga Naira 450 zuwa Naira 1, 000.
Bugu da kari, a kasafin kudi na 2023, jami’an Hukumar Kula da Gidan Gyran Hali ta Kasa, sun bayyana a gaban Kwamtin Majalisar Dattawa da ke sanya ido kan kula da harkokin cikin gida, domin kare kasafin Naira 750 na ciyar da masu zaman Jarun din ako wacce rana, inda Kwamitin ya ce, Naira 750 ta yi kadan, ya kara kudin zuwa Naira 1, 000, duba da cewa, haka bisa ka’idar yanayin tattalin arzikin Gidan Gyaran Hali na Kasar.
Bayan tsohon Shugaban Gidan Gyaran Halin na kasa ya sanar da karin a hukumnce, masu zaman Jarun din a daukacin Gidan Gyaran Halin na kasa , sun bayyana farin cikinsu na ganin za a kara masu yawan abincin da ake ciyar da su, kai tsaye.
Bayan watannin bakwai, sai murnar su, ta koma ciki, biyo bayan rahoton da aka wallafa ya nuna cewa, ba a yi wani kari, kan kudin ciyar da masu zaman Gidan Jarun din ba, duk da ikirarin da karin da aka ce, Gwamnatin Taryya, ta amince da yin karin.,
Kazalika, idan za a iya tunawa aranar 31 na watan Yulin 2019, Hukumar Kula da Gidan Gyran Hali ta Kasa ta kirkiro da doka a 20219 wadda ta cike gurbin dokar Hukumar ta 2004, wana ta .yi hakan ne, saboda matsalolin da ake da su a cikin tsohuwar dokarta ta P 29 ta 1972.
Manufar dokar ta Hukumar ta 2019, shi ne, domin a sabunta tsarin Gidajen Gyaran Halin na Kasa, yadda za su kasance, daidai da irn na fadin duniya, musamman kan kare ‘yancin Bil Adama, gyaran Gidajen da bayar da kulawar da ta dace, ga masu zaman Jarun na kasar.
Dokar ta ta 2019 ta nuna banbacin da ake da shi, na tafiyar da Gidajen Gyaran Kasar, da suka hada da, manufofi, gudanar da ayyuka, bayar da kariya, wanzar da matakai da sauransu, wadanda suka sha banban da tsari irin na baya.
Sashi na 2 1 a cikin Baka da A a cikin Baka, ya bai wa Hukumar bin ka’ida ta kasa da kasa, ta kare ‘yancin Bil Adama.
An kafa tsarin tafiyar da Gidan Gyaran Halin kasar ne, wanda ya yi daidai na duniya kan tsari uku da suka hada da, dokar Final Kod da dokokin kasa na 81 ta 1990 da kuma dokar aikata manayn laifuka ta 80, ta kasa ta 1990 sai kuma dokar Shari’a ta jihohi 12 na kasar nan, a wancan lokacin.
Kafa wannan dokar ya nuna cewa, Hukumar Gidan Gyaran Halin Kasar, ta nuna cewa, wata Cibiya ce, da ya wajaba ta rinka saita matasan da suka aikata laifuka, wanda hakan zai sanya, a samu ragin masu aikata laifuka, a cikin alumma.
Nijeriya na da adadin Gidajen Gyaran Hali 256, wanda ya zuwa ranar 3 na watan Maris din 2025, jimlar masu zaman Jarun, cikinsu har da wadanda suke ci gaba da fuskantar Shari’a, sun kai 80,183, inda kuma aka ruwaito, yawan jami’an sun kai 50,153.
Daga cikin wannan adadin, akwai jimlar masu zaman Jarun 3,688 da a yanzu, suke jiran hukuncin rataya a daukacin Gidajen Gyaran Hali, na fadin kasar, wanda hakan yawan ya kai kaso 136.7, inda hakan ya kara haifar da karancin kudaden da za a tafiyar da Gidajen da kuma rashin kayan aiki.
Tabbas, Gidajen na ci gaba da fuskantar cunkos da tauyewa ‘yan Jarun hakkinsu, wanda hakan, ke haddasa ake yawan samun wasu masu zaman Jarun, ke fasa Gidajen su arce.
Jinkirin da ake samu na yanke hukunci da Kotuna ba su yi, musamman yanke hukuncin da ya shafi kisa, hakan na kara janyo samun cunkoso, a Gidajen.
A lokuta da ban da ban, Gwamnatin Tarayya ta sha nuna sha yin alkarin samar da sauye-sauyen a tsarin Shari’a, musamman a bangaren aikata manyan laifuka.
Sai dai, abin takaici, duk da shawarwarin da Hukumomin da Kwamitocin na bangaren Fadar Shugaban kasa har da wadanda suka shude, suka bayar na samar da sauye-sauye a bangaren Shari’a, shawarwain sun koma tamkar Tatsuniyar Gida da Kaki.
Dokar Hukumar ta 2019 ta fuskanci kalubale, wajen wanzar da ita ciki har da karancin kudi na tafiyar da Gidajen, rashin kayan aiki da kuma kare lafiyar jami’an Gidajen.
Tun a 2010, Nijeriya ta sha fuskantar fasa Gidajen Gyran Hali, wanda hakan ya sanya, arcewar, masu zaman Jarun da suka kai 7,000, ciki har da ‘yan ta’adda.
Wasu daga cikin fitattun fasa Gidajen shi ne, na Kuje a watan Yulin 2022, wanda masu zaman Jarun guda 879 suka tsere, ciki har da ‘yan ta’adda 64.
Akasari dai, an alakanta cin hanci da rasahawa, rashin samun bayanan sirri, rashin daukar matakan da suka dace na tsaro, a matsayin manyan matsalolin da Gidajen Gidajn Gyran Halin Kasar, ke ci gaba da fuskanta.
Damuwar mu a nan ita ce, duba da kalubalen da kayan aiki na Gidajen Gyaran Halin Kasar ke ke ci gaba da fuskanta, zai yi wuya a inganta zamantakewar masu zaman Jarun, kamar yadda dokar da ta kafa Gidan ta tanada.
A ra’ayinmu, matukar ba a samar da kayan aikin da suka da ce, ba da kuma smar da kyakyawan yanayin da ya kamata, sauye-sauyen da ake tunanin samar wa a Gidajen, abin zai zama ne tamkar a furtawa, amma ba cika wa.
Ya zama wajbi Gwamnati ta fitar da kudi da kuma bayar da goyon baya wajen gyara tsarin tafiyar da Gidajen, musamman domin inganata rayuwar masu zaman Jarun.
Lalubo da mafita kan wadannan kalubalen abu ne da zai kasance ba na dare daya ba, musamman batun rage cunkoso, inganta rayuwar masu zaman Jarun, kara karfafa shirye-shiyen yiwa Gidajen kwaskwarima da kuma kara horas da jami’an Gidajen Gyaran Halin Kasar.
Wannan dai ya hada da kara gina wasu Gidajen Gyaraaan Hali, musamman domin a rage cunkos da kuma tabbatar da an samar da ababen more rayuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gidajen Gyaran Halin Gidajen Gyaran Hali Gyaran Halin kasar tafiyar da Gidajen Gidan Gyaran Halin Gyaran Halin Kasar Gidan Gyaran Hali masu zaman Jarun wanda hakan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Ta ƙaddamar Da Sabon Shafin Intanet Don Inganta Sayayya A Tsakanin Ma’aikatunta
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin.
Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa.
“Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga cigaban tattalin arziki gaba ɗaya a ƙasar nan.”
Ya ce wannan sabon tsari zai bai wa jami’an sayayya damar samun horo, takardun shaida, da kuma damar yin aiki da ƙwarewa, daidai da matakin duniya.
Idris ya ce: “Za a tabbatar da cewa mu jami’an gwamnati muna sayen kaya ba kawai bisa doka ba, har ma ƙwararru ne kuma masu iya gogayya a matakin duniya.”
Idris ya yaba wa Darakta-Janar na BPP, Dakta Adebowale Adedokun, bisa jajircewa da hangen nesan sa wajen inganta tsarin sayayya a Nijeriya.
Ya ce wannan gidan yana hujja ce ta jajircewar sa wajen ganin an sabunta tsarin sayayya a ƙasar nan.
Ministan ya kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su fahimci cewa sabon gidan yanar ba kawai don gwamnati ba ne, har ma wata hanya ce da za su iya amfani da ita wajen neman ingantattun ayyuka da gaskiya.
“Don haka ina kira ga dukkan hukumomi da jami’an gwamnati da su rungumi wannan shiri gaba ɗaya, kuma ina kira ga kafafen yaɗa labarai, musamman, da su taimaka wajen yaɗa amfanin sa da kuma sa ido kan yadda ake aiwatar da shi,” inji shi.
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack; Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun; Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa; Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim; Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd); da Darakta-Janar na FRCN da NTA, Dakta Mohammed Bulama da Kwamared Abdulhamid Dembos.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp