Congo Da M23 Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Published: 24th, April 2025 GMT
Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani.
Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu.
A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna.
A watan da ya gabata, shugaban ƙasar Congo Félix Tshisekedi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame suma sun jaddada aniyarsu ta tsagaita wuta ba tare da sharaɗi ba a wata ganawar ba-zata da suka yi a birnin Doha.
Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana gwabzawa ya ƙara kamari ne a watan Janairu, lokacin da ƙungiyar M23 ta ƙaddamar da wani farmaki da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda ta ƙwace garuruwan Goma da Bukavu – manyan biranen ƙasar Congo guda biyu, lamarin da ya haifar da fargabar ɓarkewar yaƙi yankin baki ɗaya.
DR Congo na zargin Rwanda da bai wa ƙungiyar M23 makamai tare da tura dakaru domin tallafawa ƴan tawayen.
Duk da ikirarin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka yi, Rwanda ta musanta zargin da ake yi ma ta na goyon bayan ƙungiyar M23.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya
Jamhuriyar Nijar da ƙasar Rasha a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 sun ƙulla yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kuma haƙar yuraniyom.
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce bayan ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashi, Mista Sergei Tsivilev.
Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma“Muhimmiyar manufarmu ita ce mu ƙara inganta rayuwar mutanen Nijar da na Rasha,” in ji Sergei, kana ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom.
“Mun amince cewa za mu horar da manyan jami’ai waɗanda za su iya aiki a fannonin tallafinmu irin na makamashi da noma da lafiya da ilimi, kuma za mu horar da injiniyoyi tun a makarantu domin su ci gaba da karatunsu a jami’o’in da ke Tarayyar Rasha,” in ji shi.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan dangantaka tsakanin Tarayyar Rasha da Nijar, in ji rahoton na ANP.
Bayan ganawar dai Ministan na Rasha ya bayyana godiyarsa ga shugaba da mutanen Nijar domin irin tarbar da aka yi masa.
“Mun ga bayanai da dama game da damarmakin da ke akwai a cikin Nijar, kuma a halin yanzu mutanenmu na ƙoƙarin aiki kan damarmakin da ke nan a Nijar,” in ji Mista Sergei Tsivilev, wanda shi ne shugaban ɓangaren Rasha a hukumar haɗakar gwamnatoci da ƙasashen AES.
“Shugaban ƙasar ya kuma sanar da mu cewa shi zai zaɓi shugaba na ɓangare ɗaya na hukumar haɗakar gwamnatocin nan ba da jimawa ba domin ayyukanmu da ‘yan uwanmu na Nijar su yi ta tafiya babu tangarɗa,” in ji shi.