Leadership News Hausa:
2025-11-03@00:56:18 GMT

Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi

Published: 13th, September 2025 GMT

Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda A Kogi

Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin Operation ACCORD III sun kashe wani fitaccen shugaban ƴan ta’adda mai suna Babangida Kachala a jihar Kogi. Wannan na zuwa ne bayan samun bayanan sirri da aka samu kan motsin ƴan ta’adda a dajin Ofere da yankin Ayetoro Gbede.

Bayanin da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na Sojoji, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ya ce, dakarun sun kafa shingen kwanton-ɓauna, amma daga bisani su ma ’yan ta’addan suka yi musu kwanton-ɓauna yayin da suke komawa sansani.

A fafatawar da ta biyo baya, Sojojin suka yi amfani da ƙarfin makamai suka halaka ɗaya daga cikin ’yan ta’addan.

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi  Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

Binciken da aka yi a wurin ya tabbatar da samun sinƙin harsashin bindiga mai ɗauke da harsasai, da wayoyin salula 31, da na’urar duba hawan jini, da kwayoyin Tramadol, da guraye da layu, da kuma kuɗi Naira 16,000. An kuma gano jini a wurin da ke nuna cewa wasu daga cikin ’yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga, ciki har da Babangida Kachala wanda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

Sojojin sun bayyana cewa za su ci gaba da sintiri da kwanton-ɓauna a yankin domin kawar da sauran ƴan ta’addan baki ɗaya. Rundunar ta ƙara tabbatar da cewa ƙarfinsu da ƙwarin gwuiwarsu na nan daram, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba su bayanai masu inganci domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kogi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Army Nigerian army tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.

Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen  tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP