An kai wa tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami hari a Kebbi
Published: 2nd, September 2025 GMT
Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari.
Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai.
Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya.
“Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja da baya.
Girgizar ƙasa ta hallaka fiye da mutum 800 a Afghanistan An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe“Muna da hakkin kare kai in an ture mu, kariyar kai a shari’ar Musulunci hakki ne, mai girma Gwamna ya ce ya bude littafin siyasa mu ko mun fara karatu,” a cewar Malami, a jawabinsa ga magoya bayansa.
Ya zargi magoya bayan Jam’iyyar APC da kai masu hari, “addini ya aminta mu yi wa ’yan uwa jaje in sun samu rashi, shi ne maƙasudin yin wannan ziyara a garin Birnin Kebbi, bakin abubuwa marasa dadi sun bayyana wadanda suke da nasaba da siyasa, bayyane take mutane sun fito daga hedikwatar Jam’iyyar APC ɗauke da miyagun makamai suna jifan abokan hamayya.”
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kebbi Yakubu Ahmed ya ce ba zai ce komai ba kan zargin, magana ce ta jam’iyya don haka a tuntube jami’yya.
Wakilinmu ya tuntubi Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kana a waya amma bai daga ba, ya kuma tura masa sako bai ce komai ba, ya sake kiran sa, amma ya ji ‘number busy.’
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kebbi, Bello Sani, ya ce ba wani da aka kama kan harin da aka kai wa tawagar tsohon minista Malami.
A lokacin da yake magana da manema labarai bayan ya kammala zama da Gwamna kan matslar tsaro, Kwamishinan ’yan sandan ya ce ana gudanar da bincike kan abin da ya faru.
A cewarsa, gwamnan ya kira taro kan tsaro game da abin da ya faru a unguwar G.R.A inda wasu ’yan jami’yyu suka karya doka da yin wasu al’amurran yakin neman zaɓe.
Ya ce “dole ne mu gayyaci jam’iyun siyasa mu tattauna don su san har yanzu ba a dage shingen fara yekuwar zabe ba.”
Kwamishina ya ce ’yan sanda sun sanya dakaru da za su hana duk wani yekuwar zaɓe don haka yana kira ga jam’iyyun siyasa su kwantar da hankalinsu.
“Abin da ya faru ana kan bincike kuma duk wanda aka samu da laifi za a kama shi ya fuskanci Shari’a,” in ji Kwamishina.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
Antoni Janar na Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke birnin Yamai a Nijar, ya bayyana cewa an kama tsohon Ministan Harkokin Waje, Ibrahim Yacoubou, bisa zargin hannunsa a cikin wata aika-aika ta kisan kai domin yin tsafi.
A cewar Maazou Oumarou, lamarin ya samo asali ne daga wani binciken ’yan sanda da aka fara gudanarwa tun a ranar 29 ga Yuli, 2025.
KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan NejaYa bayyana cewa, an soma gudanar da binciken ne dangane da yunƙurin kisa a wani yanki da ke wajen birnin Yamai, lamarin da ya kai ga cafke ababen zargin a garin Dosso.
Wani mutum mai suna Mahamadou Noura ne ya bayyana cewa shi ne ya yi yunƙurin kisan, tare da wasu kashe-kashe guda shida da ya aiwatar a baya, bisa umarnin wasu mutane, ciki har da tsohon ministan Ibrahim Yacoubou.
Mutumin ya shaida wa mahukunta cewa ya aikata hakan ne domin yin tsafi da gawarwakin, a madadin wasu mutane da suka haɗa da: Issa Ali Maiga da Ismael Morou Karama da Elhadji Bilya da kuma Issa Seybou Hama.
TRT ya ruwaito cewa tuni dai an cafke duk ababen zargin, yayin da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta umurci ’yan sanda da su ci gaba da bincike tare da ɗaukar ƙarin matakan da za su tabbatar da gaskiya.
Sanarwar ta ce: “Manufar wannan mataki na shari’a ita ce a tattara cikakken rahoto da ke ƙunshe da dukkan abubuwan da suka faru, sannan a miƙa shi ga ɓangaren gurfanarwa.”
Mai shigar da ƙara a ɓangaren gwamnati ya ce, la’akari da girman wannan lamari, wajibi ne a gudanar da bincike cikin gaggawa.
Haka kuma ya buƙaci al’umma da su mutunta ’yancin kotu tare da bayar da cikakken goyon baya domin fayyace gaskiya.
Ana iya tuna cewa, Ibrahim Yacoubou na daga cikin manyan jami’an da aka kama bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga Yuli, 2023, sai dai daga bisani an ba shi beli na wucin gadi a cikin watannin baya.