Tsohon Sufeto-Janar na ’yanyan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu
Published: 31st, August 2025 GMT
Tsohon Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Nijeriya, Solomon Arase ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, babban birnin kasar.
Rahotanni sun ce tsohon IG din ya rasu ne a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja a safiyar Lahadin nan.
An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja Chelsea ta kammala ɗaukar Garnacho daga Manchester UnitedKawo yanzu dai iyalai ko rundunar ’yan sandan kasar ba su fitar da rahoton rasuwar a hukumance ba, sai dai wani hadiminsa da Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da hakan.
Arase wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a Afrilun 2015 shi ne Sufeto Janar na 18 a tarihin Nijeriya.
Kazalika, bayan ritayarsa a shekarar 2016, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban hukumar kula da harkokin ’yan sanda ta Nijeriya PSC a Janairun 2023, wanda kuma shugaba Bola Tinubu ya sauke a bara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Solomon Arase
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.