An kashe makiyaya 4, an jikkata wani a Filato
Published: 29th, August 2025 GMT
An kashe makiyaya huɗu tare da jikkata wani a ƙauyen Fili, da ke yankin Doemak, a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan a Jihar Filato.
Rahotanni daga yankin sun ce an kai musu hari ne lokacin da suke tsaka da kiwo.
Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maitaSakataren kuɗi na Ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a Qua’an Pan, Saeedu Abdurrahman, ya tabbatar da lamarin.
Ya ce ’yan bindigar sun kashe makiyayan amma ba su sace shanunsu ba.
Ya ƙara da cewa lokacin da ake binne waɗanda suka rasu, ’yan bindigar sun sake kai wani harin, amma jami’an tsaro sun daƙile harin.
Ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su, Shanono Muhammad, ya ce, “An kashe makiyaya huɗu, ciki har da ƙaramin yaro da ya tafi koyon kiwon shanu.
’An kashe su ne da yammacin ranar Talata yayin da suke kiwo.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mai magana da yawun Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai yi ƙarin haske kan harin ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari mahara Makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu.
A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na X da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai Kukan al’umma kan lalacewar hanyar DukkuDarekan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma hukumar ta DSS.
DSS wadda ta kafa hujja da sashe na 24 da ke cikin kundin dokokin yanar gizo, ta ce Sowore ya yi amfani da shafukansa na dandalan sada zumunta na X da Facebook wajen wallafa wani saƙo da ke cin mutuncin Shugaba Tinubu.
Tun dai a farkon watan nan ne DSS ta buƙaci goge wani saƙo da ɗan gwagwarmayar ya wallafa wanda ta riƙa a matsayin bayanan ƙarya, cin zarafi ta yanar gizo da kalaman haddasa ƙiyayya, waɗanda kuma ta ce na iya haddasa rikici su kuma ɓata sunan Najeriya a ƙasashen waje.
Sai dai har zuwa ranar Litinin, 15 ga watan Satumba, babu wani mataki da aka ɗauka na goge saƙon da DSS ɗin ta buƙata.