Aminiya:
2025-11-02@06:24:48 GMT

An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita

Published: 29th, August 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi ɗan shekara 25 mai suna Jibrin Ado bisa laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita a unguwar Gerawa da ke jihar.

Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne a ranar Alhamis daga wata sanarwa ta manhajar X ta wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama.

Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasa

A cewarsa, Ado ya aikata wannan aika-aika ne tare da wasu masu laifin a ranar Talata.

Waɗanda suka haɗa da: Musa Kwalle da Dan Abba da Sule Musa da wani Arrow dukkansu daga ƙauyen Gerawa.

Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, wanda ake zargin mai suna Jibrin Ado na ƙauyen Daneji, ya haɗa baki da wasu – Musa Kwalle da Ɗan Abba, Sule Musa da Arrow, dukkansu ’yan ƙauyen Gerawa, inda suka shiga gidan mahaifinsa, Adamu Saleh.

“Waɗanda ake zargin sun yi wa matarsa (Saleh) duka, Magajiya Ado, ‘yar shekara 50 da manyan sanduna har sai da ta sume, suna zarginta da maita,” ya rubuta.

Makama ya ci gaba da cewa, an garzaya da mamaciyar zuwa babban asibitin unguwar Ringim da ke unguwar, inda ta rasu a lokacin da take jinya.

“Majiyoyi sun ce tuni aka sako gawarta ga ’yan uwa don binne ta, majiyar ta ƙara da cewa an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin Jibrin Ado, yayin da sauran kuma ke hannunsu”.

Da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Lawan Shiisu ya yi alƙawarin binciken lamarin tare da yin ƙarin bayani nan gaba. Har yanzu bai yi haka ba har zuwa lokacin da aka gabatar da rahoton.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Gerawa Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure

Babbar Kotun Kano mai lamba 7 da ke zama a cikin birni ta bayar da umarnin tsare Aminu Ismail, mazaunin Unguwar Bai a Karamar Hukumar Ajingi ta jihar, bisa zarginsa da kashe mahaifinsa, Malam Dahiru Ahmad, ta hanyar caka masa wuƙa har lahira.

Lamarin ya faru ne bayan samun sabani tsakaninsu kan aniyar Aminu ta ƙara aure, wadda mahaifinsa ya ƙi goyon baya saboda abin da ya kira halin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasa.

Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum

A cewar lauyan masu ƙara, Barrista Lamido Abba Sorondinki, wanda ake tuhuma ya shaida wa mahaifinsa niyyarsa ta kara mata ta biyu, amma mahaifinsa ya ba shi shawarar kada ya yi hakan, yana mai danganta matsalar da halin tattalin arzikin ƙasa ke ciki.

Wannan sabani ya rikide zuwa faɗa, inda ake zargin Aminu da caccaka wa mahaifin nasa wuƙa a ƙirji, lamarin da ya jawo masa rauni mai tsanani har ya rasa ransa.

An gurfanar da Aminu da laifin kisan kai, wanda ya saba da Sashe na 221 na kundin penal code.

Ana ci gaba da shari’ar, kuma kotu ta bayar da umarnin tsare shi har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron ƙarar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 
  • Kamfanin Amazon na shirin sallamar ma’aikata 600,000 don maye gurbinsu da mutum-mutumi
  • Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba
  • Matashi ya rasa ransa a kan soyayya a Yobe