ASUU: Gwamnatin Najeriya ba aiwatar da ko daya daga cikin bukatunmu ba
Published: 28th, August 2025 GMT
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba.
Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita.
Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba.
“Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar gwamnati,” in ji shi.
“Mun amince kan abubuwa da dama, sai dai shugabanninsu, Ma’aikatar Ilimi da Gwamnatin Tarayya ba su ɗauki mataki kan kowanne ba.”
Ya danganta yawan ficewa daga Najeriya da malamai da likitoci ke yi saboda ƙarancin albashi da mummunan yanayi da suke ciki.
A asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos inda yake aiki, ya ce aƙalla likitoci 20 sun bar aiki cikin shekara biyu.
“Yanayin daidai yake da na malaman jami’a. Idan ƙarancin albashi ne ke sa mutane barin aiki, me ya sa ba za a ƙara albashi a riƙe su ba?” ya tambaya.
Ya ƙara da cewa ƙasashe da dama a Afirka suna ɗaukar malaman Najeriya aiki.
“A Uganda, a cikin jami’a guda ɗaya za ka iya samun malamai ’yan Najeriya sun kai 20,” in ji shi.
Shugaban ASUU ya kuma nuna damuwa kan mummunan yanayin kayan aiki a jami’o’in Najeriya, inda ya ce hakan na daga cikin dalilan da ya sa ba sa samun matsayi mai kyau a duniya.
Ya ce daga cikin jami’o’i 333 da faɗin Najeriya, guda biyar ne kaɗai ke cikin jirin manyan jami’o’i 1,000 a nahiyar Afirka.
Ya ce malamai ba sa jin daɗin tafiya yajin aiki, amma gwamnati na tilasta musu hakan saboda rashin ɗaukar mataki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Rasha Sun Zasu Hadakai A fagen Watsa Labarai August 27, 2025 IRGC Sun Halaka Yan Ta’adda 13 A Yankin Sistan Baluchestan August 27, 2025 Zanga-Zanga Ta hana Wakilin Amurka Ziyara A Kudancin Lebanon August 27, 2025 Hamas: Isra’ila Tana Rike Da Gawawwakin Falasdinawa 726 August 27, 2025 Isra’ila Ta kashe Falasdinawa Fiye da 1000 A Yamma Da Kogin Jordan August 27, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za Su Iya Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka A Kan Wasu Sharudda August 27, 2025 Masu Binciken Hukumar IAEA Ba Za Su Shiga Wajen Da Amurka Ta Kai Hari Ba A Cibiyoyin Nukiliyar Iran August 27, 2025 Kasar Venezuala Ta Jinjinwa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Kyakkyawar Hadin Kai Da Ke Tsakanisu August 27, 2025 Kasar Rasha Ta Gabatar Da Shawara Ga Kwamitin Sulhun MDD Kan Shirin Makamashin Nukiliyar Iran August 27, 2025 Majalisar Ministocin Sudan Ta Fara Zamanta A Birnin Khartoum Fadar Mulkin Kasar Tun Bayan Barkewar Yaki August 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.
Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.
Domin sauke shirin, latsa nan