Hatsarin kwalekwale: An ceto mutane 26 ana neman 25 a Sakkwato
Published: 19th, August 2025 GMT
Kawo yanzu an ceto mutum 26 ana ci gaba da neman wasu 25 bayan hatsarin kwalekwale a yankin Goron yo da ke Jihar Sakkwato.
Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta sanar da cewa irgin ruwan ya dauko mutane 51 tare da kayansu da babura kafin ya tuntsure.
Babban Jami’in Kula da Ayyukkan na Hukumar, Aliyu Shehu ya bayyana cewa “Kokarin ceto mutanen na tafiya kuma mun sanar da garuruwa makwabta su taimaka a wajen bincikar mana mutanen a wurin da suke.
A lokacin da manema labarai suka tafi wurin dangin wadanda suka nutse, sun yi jungum don rashin tabbas ga ’yan uwansu.
Ya soka wa budurwarsa wuka har lahira ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa Albashin sanatoci 109 zai biya farfesoshi 4,709Jami’ai daga Hukumar Kula da Gulabe ta Kasa (NIWA) sun tafi wurin, inda Manajan yanki, Injiniya Muhammad Bala ya nuna rashin jin dadin hukumar kan hatsarin.
Ya yi kira ga matuka jirgi su rika kula da ka’idar tuki su daina daukar fashinja da yawan da ya wuce kima.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hatsari kwalekwale Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.
Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.
Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.
Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.
Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.
Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp