2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna
Published: 18th, April 2025 GMT
Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar.
Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa gidan Buhari sa’o’i kadan bayan tawagar Atiku, wanda ya kara tsananta siyasa.
Masu lura da al’amura siyasa sun bayyana cewa kalaman da Ganduje ya yi bayan ganawar, ya tabbatar da cewa APC na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa Buhari ya kasance tare da jam’iyya mai mulki. Wannan matakin na zuwa ne yayin da kawancen ‘yan adawa ke samun karfi, musamman a yayin da ake zaman doya da manja tsakanin gwamnatin Tinubu da ‘yan arewa.
Idan za a iya tunawa a lokacin watan Ramadan, dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya kai ziyarar girmamawa ga Buhari da sauran shugabannin siyasar arewa a lokacin rangadin da ya kai yankin.
Mai sharhi kan harkokin siyasa, Shamsudeen Ibrahim ya bayyana ziyarar da kwamitin gudanarwa na APC da Ganduje ke jagoranta suka kai ga Buhari a matsayin tsoron rasa riko, tsoron rasa arewa, da tsoron rarrabuwar kawuna. Ba ziyarar ‘yan’uwantaka ba ne. Ziyarar neman tsira ne.
Mai sharhi kan harkokin jama’a, Dakta Saidu Dukawa, ya kara da cewa ziyarar ta zama wata manuniya ga jama’a cewa shirye-shiryen zaben 2027.
Dukawa, ya kasance babban malami a jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ya ce, “A bayana, ana yin irin wannan ziyarar ga tsoffin shugabannin kasa da suka hada da Obasanjo da Jonathan don cimma manufofin siyasa, amma yanzu lamarin ya zama tarihi. “
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yan Siyasa Buhari Ziyara
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna
Daga Abdullahi Shettima.
Ƙungiyar taimako mai zaman kanta mai suna Rays Heaven for Special Needs Children and Adults ta gudanar da taron wayar da kai a Kaduna domin ƙarfafa fahimtar muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa da kuma magance matsalolin tattalin arziki da ke shafar rukunin jama’a masu rauni.
Shugaban shirye-shiryen ƙungiyar, Sadiq Abdilatif, ya bayyana cewa wannan shiri mai taken Youth Resilience Project ana aiwatar da shi ne da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (European Union) tare da Global Youth Mobilization Fund.
Ya ce manufar shirin ita ce wayar da kai ga makarantun sakandare, al’ummomi, da sansanonin ’yan gudun hijira kan mahimmancin lafiyar kwakwalwa, tare da ƙarfafa matasa su koyi magana idan suna fuskantar damuwa ko matsaloli, da kuma koyar da malamai da shugabannin al’umma hanyoyin taimaka musu.
Mr. Abdilatif ya bayyana cewa matasa da mutane masu buƙata ta musamman, ciki har da ’yan gudun hijira, na fama da ƙalubalen tunani da na tattalin arziki da ke rage musu ƙarfi wajen gudanar da rayuwa. Ya ce wannan shiri yana nufin gina ƙarfin gwiwa da samar da wakilai a cikin al’umma waɗanda za su ci gaba da yada wannan saƙo a yankunansu.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar na da shirin haɗa shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da ci gaba da wayar da kai a matakin ƙasa, yana mai cewa batun lafiyar kwakwalwa abin ne da ya shafi kowa.
Ɗaya daga cikin mahalarta shirin, Salma Hussaini, wadda ba ta da gani, ta yaba da yadda ƙungiyar ta haɗa masu buƙata ta musamman a cikin shirin. Ta ce ta amfana sosai wajen fahimtar yadda ƙarfin tunani da dogaro da kai ke taimakawa mutum ya shawo kan ƙalubalen da yake fuskanta duk da rashin lafiyar jiki.