Arsenal ta gasa wa Madrid aya a hannu
Published: 9th, April 2025 GMT
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa Real Madrid a daren nan a karawar da suka yi ta kwata-fainal a Gasar Zakarun Turai.
Arsenal dai ta doke Real Madrid da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Emirates da ke Landan.
Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansaAn kammala minti 45 na karawar babu ci, sai dai alƙaluma sun nuna Arsenal ta kai farmaki sau huɗu yayin da Real ta kai hari sau biyar.
Duk da cewa babu ɓangaren da ya samu nasarar zura ƙwallo amma wasan wanda Irfan Peljto na ƙasar Bosnia Herzegovina ya yi alƙalanci ya yi matuƙar zafi tsakanin ɓangarorin biyu.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne ɗan wasan tsakiya na Arsenal, Declan Rice ne ya zura ƙwallon farko a minti na 58 ta hanyar bugun tazara bayan da ’yan wasan Madrid suka yi wa Bukayo Saka ƙeta.
A minti na 70 ne Declan Rice ya ƙara zura ƙwallo ta biyu a ragar Real Madrid ta hanyar bugun tazara kamar yadda ya yi a karon farko.
A yayin da aka ci gaba da ɗauki ba daɗi ne Mikel Merino ya zura ƙwallo ta uku a minti na 75 da take wasa, bayan ɗan wasa Lewis Skelly ya zuro masa ƙwallon daga gefe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arsenal
এছাড়াও পড়ুন:
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno
Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar.
Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.”
Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita 11 daga garin Rann, da misalin karfe 11 na safe a ranar Litinin.
Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin NajeriyaTa ƙara da cewa an kai wasu da suka jikkata asibitin Rann domin kula da su.
Babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren sojoji ko ’yan sanda game da faruwar lamarin.
Sai dai kuma, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, Kenneth Daso, bai yiwu ba saboda layin wayarsa ba ya shiga.