Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Bita Ga Alhazai
Published: 8th, April 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan kammala azumin watan Ramadan.
Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami horo da ilimi kan yadda ake aiwatar da aikin Hajji domin dacewa wannan ibada da suka kashe makudan kudade don gannin sun aiwatar da ita.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, za a wayar da kan alhazai da kuma koya musu yadda za su kula da kansu da kuma yadda za su aiwatar da aikin Hajji bisa ga koyarwar addini.
Ya ce, ana gudanar da wannan taron bitar ne a kullum, a cibiyoyi 27 da aka ware a fadin jihar.
Haka kuma, ya ce, taron bitar zai taimakawa Alhazan wajen fahimtar dokoki da sabbin tsare-tsaren da hukumomin Saudiyya da hukumar Hajji ta kasa NAHCON suka tsara domin aikin Hajjin shekarar 2025.
Labbo ya yi kira ga dukkanin alhazan bana da su rika halartar wadannan tarurruka domin sanin abubuwan da suka dace.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma yaba maniyyatan bisa yadda suke daukar wannan taron koyarwa da muhimmanci.
Daraktan ya kuma shawarce su da su ci gaba da nuna dabi’un kirki kamar yadda suka saba, tare da zama jakadu nagari ga jihar, da kasa baki daya, tare da bin doka da oda a masarautar Saudiyya.
Ya ce, hukumar ta riga ta tanadi masauki mai tsafta kusa da Masallacin Harami ga alhazan jihar, tare da shirya yadda za a rika ba su abinci ta hannun wani kamfani na kasar Saudiyya.
Labbo ya kuma yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da hadin kai da yake bai wa hukumar a kowane lokaci.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Taron Bita
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Yi Allurar Rigakafi Ga Dabbobi Sama Da Miliyan Daya A Babura
Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.
Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana.
A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar.
Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar.
Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu.
Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin dadinsa game da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a yankin, yana mai kira gare su da su ci gaba da gudanar da rayuwa cikin fahimta da hadin kai.
Haka zalika, yayin taron, Shugaban Sashen Noma da Albarkatun Kasa, Malam Lawan Sabo Kaugama, ya bayyana cewa an ware cibiyoyi guda goma sha biyu domin gudanar da aikin rigakafin wanda ake sa ran zai dauki kwanaki hudu.
Ya yaba da kokarin gwamnatin jiha da ta karamar hukuma wajen samar da allurar rrigakafn da kuma duk wasu kayan aiki da ake bukata.
Usman Muhammad Zaria