Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci.
Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida — namiji ko mace.
A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna:
Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi. Fitar da zakkar fid da kai, wato Zakkar Kono. Cin dabino ko abinci kafin zuwa Sallar Idi. Yin wankan idi kafin zuwa halartar sallar idi. Sanya sabbi ko mafiya kyawtun tufafi da mutum ya mallaka. Sanya turare da yanke farce Ana son sanya turare ga maza. Yawaitawa da kuma bayyana kabarbari ga maza da mata. Daina yin kabbarori daga lokacin da aka tayar da sallar.Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, LaiLaha illAllah, Allahu Akbar walillahil hamdu. Sauraron huduba bayan kammala Sallar. Zuwa sallar da dawowa ta hanyoyi daban-daban. Rashin zuwa da makami ko wani abu da zai razana mutane sallar idi. Ziyara da taya ’yan uwa da sauran murna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sallar Idi zakkar fidda kai Allahu Akbar
এছাড়াও পড়ুন:
Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali.
Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata NatashaA kwafin wasiƙar da LEADERSHIP ta samu, Babagana ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda aka yi watsi da wanda suke hidimtawa gwamnati da taimaka mata. “Don haka ina sanar da ajiye aiki na a hukumance daga matsayin mai taimakawa gwamna na musamman” cewarsa.
A ƙarshe, ya godewa gwamna Buni bisa damar da ya ba shi na yin aiki a gwamnatinsa, tare da yi masa fatan alheri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp