Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a Gombe
Published: 24th, March 2025 GMT
Wasu fusatattun matasa sun daka wawa kan kayan abincin tallafin azumi da ɗan Shugaba Nijeriya, Seyi Tinubu zai raba a Jihar Gombe.
Aminiya ta ruwaito cewa duk da cewa bai kai ga zuwa jihar ta Gombe ba, amma kayan abinci da zai raba tuni sun isa jihar.
Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas Ban bai wa majalisa haƙuri ba — NatashaWani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna matasan na wawason katan-katan na kayan abinci daga kan wata mota da ke tsaye a bakin titi.
An hangi matasan na jefa wa waɗanda ke ƙasa kayan abincin — inda suke karɓa su kama gabansu.
Kayan abincin sun haɗa da buhunan shinkafa da sikari da mai da taliya da kuma gishiri.
Yayin da tuni an raba ɗaya daga cikin motocin ɗauke da kayan abincin, matasan sun tare guda inda suka yi wawushe komai da ke cikinta.
A bayan nan dai ɗan gidan shugaban ƙasar na shawagi a wasu jihohin arewacin Nijeriya, inda yake haɗuwa da mazauna jihohin da kuma shugabannin siyasa wajen buɗa-baki.
A yayin waɗannan ziyarce-ziyarce ne kuma ɗan shugaban ƙasar yake ƙaddamar da rabon tallafin abinci ga mabuƙata da albarkacin watan azumi.
Sai dai wannan lamari na ci gaba da janyo cece-kuce a faɗin ƙasar, a yayin da wasu ke yabawa wasu ko kushe suke yi.
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi Allah wadai da rabon abincin da ɗan shugaban ƙasar ya yi a yankin Arewa, yana bayyana hakan a matsayin wani nau’i na rashin mutunta al’adun Arewa.
A cikin wani bidiyo da karaɗe shafukan sada zumunta, Lamido ya bayyana hakan a yayin wani taron buɗa-baki na mambobin jam’iyyar PDP da ya gudana a garin Bamaina da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
A makon jiya ne ɗan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed, ya yi kira ga Seyi Tinubu da ya yi amfani da ziyararsa don tallafa wa matasan jihar.
Shamsuddeen Bala Mohammed ya ce bai kamata a mayar da matasan Bauchi kamar mabarata ba, sai dai a ba su damar dogaro da kansu ta hanyar ayyukan yi da horo na musamman.
Shamsuddeen ya bayyana cewa matasan Bauchi sun fi buƙatar ayyukan yi da jari, ba kayan abinci kawai ba.
Ya buƙaci a ba su tallafi kamar Keke NAPEP, kuɗin kafa kasuwanci, da kuma horo a fannin sadarwar zamani da cinikayyar kirifto domin inganta rayuwarsu.
Ɗan gwamnan na Bauchi ya ce yana da kyau a koya wa matasa yadda za su dogara da kansu fiye da ba su abinci da zai kare a rana ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Gombe Kayan abinci kayan abincin kayan abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta gano ma’aikatanta 240 da ke ƙarɓar albashi sau biyu a duk wata, da wasu 217 da ke amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) guda ɗaya.
Wani mai magana da yawun gwamnati, Dakta Sulaiman Wali Sani, ya gaya wa manema labarai a ranar Lahadi cewa an gano wannan badaƙalar ce a yayin da ake tantance tsarin biyan albashin gwamnati.
Dr. Sani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin biyan ma’aikata daidai kuma akan lokaci, kuma gano waɗannan matsalolin wani ɓangare ne na gyara al’amura.
Ya ce sun duba bayanan ma’aikata ta hanyar amfani da hotunan yatsa a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
“Tsohuwar hanyar biyan mutane tana da matsaloli. Mun gano ma’aikata 240 suna karɓar albashi sau biyu kuma mutane 217 suna amfani da BVN ɗaya, wanda zai iya nufin akwai ma’aikatan bogi ko kuma mutane suna amfani da BVN na wani,” in ji Dakta Sani.
Ya kuma ce ma’aikata 1,335 ba su zo don a tantance su ba a tsawon fiye da watanni shida, wanda ya sa suke tunanin ko waɗannan mutanen da gaske suna aiki da gwamnati.
Alhaji Umar Idi, wanda ya duba biyan kuɗin ƙananan hukumomi, ya ce sun gano sunaye 247 da babu tabbaci a kansu. Waɗannan sun haɗa da mutanen da suka yi ritaya, waɗanda suka mutu, ko kuma waɗanda aka ci gaba da biyan su ba tare da izini ba bayan lokacin barinsu aiki.
“Daga cikin waɗannan ma’aikata 247, takwas ne kawai suka zo don tabbatar da cewa har yanzu suna aiki. Za a goge sauran sunaye 239, wanda zai rage wa gwamnati asarar naira miliyan 27 a duk wata,” in ji shi, yana mai cewa za a mayar da kuɗaɗen da aka samu ga asusun gwamnati.
Dakta Sani ya ce gwamnati ba ta ƙoƙarin hukunta kowa ba, kawai dai tana gyara tsarin ne don ma’aikata na gaske da ’yan fansho su ci gaba da karɓar haƙƙoƙinsu ba tare da wata matsala ko yanka ba bisa ƙa’ida ba.
“Tun lokacin da Gwamna Abba ya fara aiki, ya tabbatar da cewa ana biyan ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho a kan lokaci, ba tare da ɓoyayyun cire-cire da aka riƙa yi a baya ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa yanzu da suke tsaftace tsarin biyan kuɗi, ma’aikata su yi tsammanin samun biyan kuɗi mafi inganci a gaba.
Gwamnati ta ce za ta ci gaba da magana da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa an magance duk matsalolin kuma jama’a sun sake amincewa da ayyukan gwamnati.