PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio
Published: 7th, March 2025 GMT
Jam’iyyar adawa ta PDP, ta yi Allah-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan cin zarafinta.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ya fitar, jam’iyyar ta ce dakatarwar wata hanya ce ta ɓoye zargin da ake yi wa Akpabio.
“Wannan mataki ba wai kawai ya hana Sanata Akpoti-Uduaghan damar kare kanta ba ne, har ma yana nuna cewa majalisar na kare rashin ɗa’a,” in ji PDP.
Jam’iyyar ta kuma ce dakatarwar ba adalci ba ce ga al’ummar yankin Kogi ta Tsakiya, waɗanda yanzu suka rasa wakilci a majalisa.
“Wannan cin zarafi ne da amfani da muƙami ba daidai ba, domin Akpabio na ci gaba da zama a kujerarsa duk da irin wannan zargi mai girma.
“Idan har bai da abin ɓoyewa, ya sauka don bayar da damar gudanar da bincike na gaskiya,” in ji PDP.
PDP ta nuna cewa ba wannan ne karon farko da ake zargin Akpabio da aikata irin wannan ba.
Ta ce tsohuwar Shugabar Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Dokta Joi Nunieh, ta taɓa yin irin wannan ƙorafi a kansa.
Jam’iyyar ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa da ya kare sunansa ta hanyar amincewa da bincike maimakon ƙoƙarin ɓoye gaskiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Allah wadai cin zarafi Siyasa zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Pogba Na Shirin Komawa Monaco Bayan Dakatar Da Shi
Bayan hakan, Pogba ya kunce kwantiraginsa da Juventus a watan Nuwamban 2024, kuma tun watan Maris da ya gabata ya samu damar komawa fili domin shirya dawowarsa.
Yanzu haka yana ci gaba da atisaye tare da fatan ƙulla sabuwar yarjejeniya da Monaco domin ci gaba da taka leda a ƙasarsa ta haihuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp