Jami’an tsaro sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Kano
Published: 26th, February 2025 GMT
Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da DSS sun tarwatsa zanga-zangar da ta ɓarke a Ƙofar Nasarawa da ke Jihar Kano.
Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun yi dandazo a ƙarƙashin gadar Ƙofar Nasarawa, lamarin da jami’an tsaron suka yi musu tarnaƙi da barkonon tsohuwa.
Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin RamadanKawo yanzu dai ba a gano dalilin gudanar da zanga-zangar ba, sai dai tuni jami’an tsaro suka sanya shamaki a hanyoyin da ke daura da zuwa Gidan Gwamnatin Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC
Ƙungiyar matasan jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta ce guguwar sauyin sheƙa ta jiga-jigan ’yan siyasa da ke ficewa daga jam’iyyar NNPP alama ce da ke nuna cewa tasirin tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso a siyasance na ƙara disashewa.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar matasan ta KASASCO ta fitar a ranar Talata, ta ce a halin yanzu jam’iyyar APC ba ta buƙatar dawowar Kwankwaso cikinta saboda tasirinsa a siyasance na ci gaba da gushewa.
DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a BornoDarekta Janar na KASASCO, Kwamared Yahaya Usman Kabo, ya ce jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Abbas ta yi tsayuwar daka da kafa tubalin samun nasara a Zaɓen 2027 da ke tafe, la’akari da cewa tana da Sanatoci biyu da kuma wakilci mai ƙarfi a matakin jiha da tarayya.
Ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ke kaɗawa a jam’iyyar NNPP na da nasaba da tasirin jiga-jigan jam’iyyar da suka tsaya kai da fata wajen tabbatar da nasararta a Zaɓen 2023.
Sai dai ya ce a yanzu jiga-jigan jam’iyyar ta NNPP na ficewa daga cikinta zuwa APC saboda zargin rashin adalci da mayar da su saniyar ware da ’yan Kwankwasiyya suka yi.
Aminiya ta ruwaito cewa daga cikin jiga-jigan NNPP da suka sauya sheƙa zuwa APC a bayan nan akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo da Zubairu Hamza Massu.
Akwai kuma Abbas Sani Abbas da Baffa Bichi da kuma Sha’aban Ibrahim Sharada.
Ya ce “sauyin sheƙar waɗannan jiga-jigan ’yan siyasa ta karya garkuwar jam’iyyar a Kano. Saboda haka yanzu APC ta warware duk wasu matsalolin cikin gida da take fuskanta domin tabbatar da nasarar a 2027.”
APC ta ce tana da yaƙinin samun nasara a zaɓen da take tafe wanda take fatan bai wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a Jihar Kano.
Sai dai ta ce dawowar Kwankwaso jam’iyyar babu abin da zai haifar sai kawo ruɗani a cikinta.
“A yanzu Kwankwaso ba shi da wani tasiri a siyasance, shi ya sa yake neman mafaka da babu inda zai same ta face a jam’iyyar APC.
“Sai dai yana da kyau ya fahimci cewa APC ba wuri ba ne na samun mafaka kuma ba ta buƙatar irinsu [Kwankwaso] da babu abin da za su kawo wa jam’iyyar face ruɗani.”