Da Ɗumi-ɗumi: NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu Sumaila Da Wasu ‘Yan Majalisa Uku
Published: 24th, February 2025 GMT
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yan majalisar majalisar da
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinu: Mahmud Abbas Ya Nada Magaji Da Kuma Mataimakasa
Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa a makon da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da yankin sun dade suna takurawa Abbas kan ya nada mataimaki da kuma wasu mataimaka sabuda rawar da gwamnatinsa zata taka bayan yakin gaza.
A yau ne majalisar zartarwa ta amince da nada Hussein Al Sheikh a matsayin mataimakin shugaban majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa a lokaci guda.
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasdinawan WAFA, ya bayyana cewa gwamnatin Abbas ce da hakkin sa hannu a kan yarjeniyoyi da suka shafi Falasdinu, a madadin dukkan kungiyoyin Falasdinawa, banda wadanda su ka dauke da makamai suna yakar HKI, wato Hamas da kuma Jihadul Islami a Gaza.
Mr Al Sheikh, dan shekara 64 a duniya na hannun daman Abbas ne a kungiyarsa ta fatah.