Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP
Published: 23rd, February 2025 GMT
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai mai hankali da zai goyi bayan APC a zaɓen 2027.
PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, baya aikin komai sai ɗumama kujera.
Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — AtaHaka kuma, ana zargin gwamnatin Jihar Kaduna da dakatar da rarraba kayayyakin koyarwa da Sanata Lawal Adamu ya saya domin amfanin makarantun jihar.
Yusuf Dingyadi, Mataimaki na Musamman na Shugaban PDP kan Yaɗa Labarai, ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta haɗa kai da wakilan jama’a don ci gaban al’umma.
“Abin da ake buƙata shi ne gwamnatin jihar, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, ta haɗa kai da sauran wakilan jama’a don inganta rayuwar al’ummar Kaduna.
“PDP jam’iyya ce mai aƙida, kuma idan har kuna ci gaba da kai mata hari, ba za ku taɓa samun ci gaba ba.
“Ba za ku iya ɗaukar ’yan daba da masu yaɗa farfaganda don ɓata mana suna ba, kawai don ku burge Shugaba Bola Tinubu saboda burinku na 2027.
“Babu wani ɗan Arewa mai hankali da zai yi wa APC kamfe a Arewa.
“Gaskiyar ita ce, wasu ’yan siyasa suna yi masa biyayya ne ba don suna goyon bayansa da gaske ba, sai dai kawai don su samu abinci,” in ji shi.
Dingyadi ya shawarci Gwamna Uba Sani da kada ya bari wasu ’yan siyasa su ruɗe shi.
Ya ƙara da cewa, “’Yan majalisar da PDP ta zaɓa suna aiki tuƙuru. Suna yin ƙoƙari a yankunansu sama da na APC.
“Ba za ku iya daƙile nasarar siyasarmu ta hanyar ɗaukar ’yan farfaganda don su kai wa wakilanmu masu aiki hari ba, ko kuma ta hanyar shirya ficewar ’yan siyasa daga PDP a wuraren da aka shirya da gangan.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa martani Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya sheƙar da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban suke yi.
A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ta jawo ɗiga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaɓen 2027.
Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan ƙasar suke kokawa bisa yadda ake gudanar da mulki da kuma yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC.
NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaWannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai da nufin gano alƙiblar da siyasar Najeriya take shirin fuskanta.
Domin sauke shirin. Latsa nan