Abu Ubaidah: Hamas Za Ta Saki Fursunoni 3 A Yau Asabar
Published: 15th, February 2025 GMT
Kakakin dakarun rundunar “Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa za su saki fursunoni 3 na “Isra’ilawa” a wannan rana ta Asabar.
A jiya Juma’a ne dai kakakin na dakarun rundunar “ Kassam” ya fitar da sanarwar cewa za saki fursunoni uku da suke rike da su da su ne: Shasha Alexander,Sagi Dikel Hen,Yaei Horun
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai mai Magana da yawun dakarun na “Kassam” Abu Ubaidah ta sanar da dakatar da duk wani batu na cigaba das akin fursunonin sai illa masha Allahu.
Sai dai daga ranar Alhamis zuwa jiya Juma’a masu shiga tsakani da su ne kasashen Katar da Masar, sun yi kokarin gusar da matsalar da ta kunno kai daga gefen HKI da hakan ya bayar da damar sake komawa kan batun musayar fursunonin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno
Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa da maza 16 da mata huɗu da ƙananan yara guda shida.
Ta yi wa saurayinta ƙaryar shekarunta 27 maimakon 47 An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da PortugalMajiyoyi, ciki har da wani babba soja, sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu da harin na baya bayan da safiyar ranar Talata.
Sun bayyana cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna kan hanyarsu ta tafiya Gamboru Ngala ne daga Rann lokacin da suka isa inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka ɗana bam ɗin.
Bayanai sun ce baya ga mutum 26 da suka mutu, ƙarin mutum uku sun ji munanan raunuka.
“Mun tura wasu masu ba da agajin gaggawa inda lamarin ya auku domin kwashe mutane tare da tabbatar da tsaron sauran fararen-hula a wurin,” kamar yadda wata majiyar sojin da ba ta yarda a bayyana sunanta ba ta shaida wa Anadolu.
Ali Abass, wani ganau wanda ke tafiya a kan hanyar a lokacin da lamarin ya auku, ya ce sojojin da ‘yan sa-kai sun kai waɗanda suka jikkata wani asibiti. Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin ‘yan’uwansa na cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Harin yana zuwa ne yayin da hare-hare ke ƙara ƙaruwa a yankin Tafkin Chadi, inda ‘yan ta’addan Boko Haram ke ƙara ƙaddamar da hare-haren bama-bamai da kwanton-ɓauna kan motocin fararen-hula da na sojoji.
An ba da rahoton hare-hare irin wannan a ranakun 21 ga watan Maris da 12 ga watan Afrilu. Kawo safiyar ranar Talata dai, jami’an tsaro a Borno ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.