Yanzu-Yanzu: Shugaban Hukumar REMASAB, Haruna Zago Ya Rasu
Published: 13th, February 2025 GMT
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa.
Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin KanoHaruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.
কীওয়ার্ড: Haruna Zago
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar kasar Rasha.
Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya.
Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta.
Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna.
Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar Rasha Olog Silgy ya tabbatar da cewa,kasarsa a shirye take ta bunkasa aiki da jamhuriyar musulunci ta Iran a fagen musayar dalibai da kuma nazarce-nazarce da bincike na ilimin likitanci.
Kasashen biyu sun kafa kwamitin hadin gwiwa na yin fada da cutuka masu yaduwa da zai taka rawa mai girma wajen magance cutuka.