Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
Published: 12th, February 2025 GMT
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Besse/Maiyama daga Jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Koko, ya sanar da wannan mataki ne cikin wata wasiƙa da ya aike kuma aka karanta a zauren majalisa.
N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — ZulumYa bayyana rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta masa barin ta.
Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan ficewar wani ɗan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, wanda shi ma ya fice daga PDP sabida rikice-rikice.
Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta zargin jam’iyyar na fama da rikice-rikice.
Ya jadadda cewar kowace jam’iyya tana da bambancin ra’ayi, amma hakan ba yana nufin samun rigingimu ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai Sauya Sheƙa
এছাড়াও পড়ুন:
An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
Hukumar jin daɗin jama’a ta Jihar Kwara tare da haɗin gwiwar Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun kama wasu mabarata a titunan Ilorin, ciki har da wasu da aka samu da kuɗaɗen ƙasashen waje.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mabaraci mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, wanda aka samu da takardar daloli.
Musa Mahmud ya shaida wa manema labarai cewa wani ne ya ba shi takardar Dala a Abuja.
Jami’ai sun bayyana damuwa kan yadda masu bara ke riƙe da kuɗaɗen da ba su dace da yanayin rayuwarsu ba.
Mutuwar majinyata: Asibitin Aminu Kano na roƙon KEDCO ya dawo da wutar lantarki Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II“Za mu bincika asalin waɗannan kuɗaɗen da kuma dalilin da ya sa suke da su,” in ji Adebayo Okunola, shugaban cibiyar gyaran hali a Jihar Kwara.
Jami’an gwamnati sun kwashe kusan mutane 40 daga wuraren da suka haɗa da Tipper Garage, Offa Garage, Tank da Geri Alimi Roundabout.
Jami’an sun ce bakwai daga cikin waɗanda aka kama an taɓa kama su a baya, amma sun koma tituna bayan an sako su.
Kwamishinar jin daɗin jama’a ta jihar, Dakta Mariam Imam, ta ce adadin masu bara da aka kama ya ragu sosai idan aka kwatanta da na baya, inda ta ce suna sauya dabaru don su guje wa kama.
Ta roƙi jama’a da su daina ba wa masu bara kuɗi kai tsaye, su maida gudummawarsu ta hanyar wuraren ibada da gidajen marayu.
Jami’an gyaran hali sun ce za a tilasta wa waɗanda aka kama su yi aikin tsaftace tituna a matsayin horo da kuma darasi.
Wasu daga cikin masu barar sun roƙi gwamnati da ta tausaya musu, ba su da wata hanyar rayuwa sai bara.