Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku fyaɗe
Published: 10th, February 2025 GMT
Kotu ta tsare wani ɗan fashi da ya yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe.
Matashin da dubunsa ta cika yi wa ɗaliban fyade ne a yayin wani fashi a ɗakunan kwanan ɗalibai mata a cikin dare.
Ya yi musu wannan aika-aika tare da yunƙurin kisa ne a daƙinsu kwanan ɗalibai mata da ke wajen harabar jami’ar a yankin Malete a ranar 2 ga watan Disamba, 2024.
A yayin gurfanar da matashin a gaban Kotun Majiatare ta Jihar Kwara da ke birnin Ilorin, an tuhume shi da yin amfani da makami wajen yi wa ɗaliban munanan raunuka, tare da yi musu fyaɗe da kuma sace wayoyin iPhone 13 PronMax da iPhone 11 Pro Max.
’Yan sanda na neman ’yan bola-jari ruwa a jallo a Abuja 2027: Kwankwaso da Aregbesola sun gana kan makomar siyasar Najeriya“Kana gab da kashe ɗaya daga cikinsu ne aka kawo musu ɗauki, kuma bincike ya gano cewa kai ɗan ƙungiyar asiri ne tun shekarar 2020, kuma ƙungiyarku ta Aiye, ta yi ƙaurin suna wajen yin fashi da makami da aikata kisa da kuma yi wa ɗalibai mata fyaɗe,” kamar yadda ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Nasiru Yusuf, ya karanta a takardar zargin matashin ɗan shekara 26.
Daga nan alƙalin kotun, Majistare Sa’idu ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Fabrairu, 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai ɗalibai mata
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.
A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.
Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.
Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.
Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.
Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”
“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”
Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.
Daniel Karlmax