HausaTv:
2025-09-18@06:57:21 GMT

Sam Nujoma Da Ya Samarwa Kasar Namibia ‘Yanci Ya Rasu Yana Dan Shekaru 95

Published: 9th, February 2025 GMT

Shugaban kasar Namibia dake kan gado Nangolo Mbumba ne ya sanar a yau Lahadi cewa, jagoran samun ‘yacin kasar Sam Nujoma ya rasu a jiya Asabar da dare, bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin babban birnin kasar Windhoek.

Sanarwar da shugaban kasar ta Namibia mai ci a yanzu, ya fitar ya bayyana mutuwar Nujoma da cewa; ginshikin da aka kafa kasar akansa ya girgiza.

Sam Nujoma ya jagoranci fadan sama wa kasar ta Namibia ‘yanci daga mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta kudu, a shekarar 1990, sannan kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 15.

A lokacin da yake a raye, al’ummar kasar ta Namibia suna girmama shi matuka a matsayin wanda ya jagoranci fadan samun ‘yanci sannan kuma ya dora kasar akan turbar demokradiyya.

A yayin gwagwarmayarsa ta nema wa kasar ‘yanci, Nujoma ya yi shekaru 30 yana gudun hijira. Kasar dai ta sami ‘yanci ne daga mulkin mallakar tsarin Wariya na Afirka ta Kudu a 1989, bayan da a baya ta kasance a karkashin mulkin mallakar jamus. Majalisar dokokin kasar ta zabe shi a matsayin shugaban kasa a 1990.

Nujoma ya kasance a sahu daya da jagororin da su ka yi  fafutukar samun ‘yanci a nahiyar Afirka da su ka hada Nelson Mandela na Afirka Ta Kudu, Robert Mugabe na Zimbabwe, Kenneth Kaunda na Zambia, Julius Nyerer na Tanzania da Samora Machel na Mozambique.

Kungiyar neman ‘yanci ta SWAPO wacce Nujoma ya jagoranta ta dauki shekaru 20 tana fada da makamai, wacce kuma ta sami cikakken goyon baya a duniya daga ciki har da MDD.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
  • Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar