Gidauniyar ‘TY Buratai Literary Initiative (TYBLI)’ ta kaddamar da shirye-shiryen tallafinta na 2025 wanda ta kudiri aniyar bunkasa ilimi da tsarin koyo a tsakanin daliban Nijeriya. Shirin wanda gidauniyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ta kirkiro kuma ta dauki nauyin wannan shiri na da nufin kwadaitar da koyon Adabin rubutu da kuma bai wa daliban da suka fi hazaka tukuici a fadin kasar nan.

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi Da take jawabi a wani taron manema labarai, Dokta Lizi Ben-Theanacho, shugabar Gidauniyar ta TYBLI, ta jaddada kudirin Gidauniyar na bunkasa adabin rubutu ta hanyar samar da littattafai da kyaututtuka ga dalibai masu hazaka. “Abu na farko da muke fatan aiwatarwa shi ne, mu ba da gudummawa don samar da ilimi mai zurfi a Nijeriya ta hanyar samar da littattafai, tabbatar da ingancin kayan karatun da suka dace. Daga nan, sai mu zakulo dalibai masu hazaka, mu gwangwaje su da kyaututtuka na ban mamaki. “TYBLI Gidauniya ce ta wayar da kan jama’a da bayar da tallafi ga al’umma wacce Laftanar Janar TY Buratai (mai ritaya) ya kirkiro kuma ya dauki nauyin aiwatarwa.” in ji ta.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj

 

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure.

Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia.

Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan nade-nade ne bisa la’akari da irin kwazon da suka nuna a ayyukansu, sadaukarwa, kishin kasa, amana da kuma tsoron Allah.

A cikin sakon taya murna ga wadanda aka nada, Sakataren Gwamnati ya bukace su da su ci gaba da nuna wadannan dabi’u yayin da za su gudanar da wannan muhimmin aiki da aka dora musu, don kara tabbatar da amanar da gwamnatin da al’ummar Jihar Jigawa suka dora a kansu.

Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran tawagar Amirul Hajjin za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa da kuma sauran hukumomin da suka dace a matakin Jiha, Tarayya da na kasa da kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da inganci.

Sanarwar ta bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS
  • Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Nijeriya Na Ke Yi Wa Biyayya Ba Wani Ko Jam’iyya Ba – El-Rufai
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan  Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki