An Bukaci Gwamnoni Su Yi Koyi Da Gwamnatin Neja Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya
Published: 4th, February 2025 GMT
An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa tare da tabbatar da lakabin gargajiya ga wasu fitattun Fulani guda biyu a jihar Neja, da aka gudanar a fadar Sarkin Minna.
Dokta Baba Usman Ngelzarman ya bayyana cewa, hanyar da Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ya bi na samar da sakamako mai kyau, ta yadda za a rage yawan rikicin makiyaya da manoma a jihar abin a yaba ne matuka.
A cewarsa hakan ya sanya bangarorin 2 sun kara fahimta da mutunta juna, wanda ya haifar da karuwar kudaden shiga a jihar da ma Najeriya baki daya.
Mai martaba Sarkin Minna Dr Umar Faruk Bahago, ya jaddada bukatar masu rike da mukaman gargajiya a yankinsa su rika gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah, ta hanyar yin adalci ga kowa, don samun nasara.
A nasa jawabin sabon Jauro Minna kuma Kwamishinan kula da harkokin Makiyaya da kiwo na jihar Neja, Umar Ahmed Rebe ya yi alkawarin kara himma wajen inganta alakar manoma da makiyaya, wadda za ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da walwala domin samun kyakkyawan sakamako.
A nashi jawabin, Wakilin Fulanin Minna, Alhaji Hassan Usman Shiroro, ya yi kira ga Fulanin jihar Neja da su ci gaba da zama lafiya da kowa domin bunkasa ci gaban jihar Neja cikin hanzari, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne abin da ake bukata na duk wani ci gaba mai ma’ana.
Daga Aliyu Lawal
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jihar Neja Kungiyar Miyetti Allah
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Jihar Kwara Ta Fara Allurar Rigakafi Ga Maniyyata
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto wajibi ga dukkan Alhazai bisa umarnin gwamnatin Saudiyya.
Ya ce yin rigakafin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajji.
A cewarsa, an shirya shirin rigakafin ne domin hana yaduwar cututtuka da kuma tabbatar da cewa Alhazai sun samu lafiya da kwanciyar hankali yayin aikin Hajjin.
Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara jigilar rukuni na farko na Alhazai daga jihar zuwa ƙasar Saudiyya ranar 12 ga watan Mayu.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa za a kammala aikin rigakafin ne ranar Laraba 30 ga watan Mayu, sannan kuma za a fara raba tufafi da jakunkunan tafiya nan take.
Alhaji Abdulkadir ya yi kira ga maniyyatan da su kammala duk shirye-shiryen lafiyar jiki da na tafiya cikin lokacin da aka kayyade domin samun nasarar aikin Hajjin ba tare da wata tangarda ba.
Ali Muhammad Rabi’u