HausaTv:
2025-11-03@03:01:19 GMT

Kasashen Larabawa Sun Rubutawa Amurka Wasika Akan Korar Falasdinawa Daga Gaza

Published: 4th, February 2025 GMT

Ministocin harkokin wajen 5 na kasashen larabawa tare da hadin gwiwar jami’an Falasdinawa sun rubuta wa ministan harkokin wajen Amurka  Marco Antonio Rubio wasiki da a ciki suke nuna kin amincewa da shirin korar Falasdinawa zuwa wajen Falasdinu.

 Kasashen da su ka rubuta wasikar sun kunshi Saudiyya, HDL, Katar, Masar da Jordan, sai kuma mai bai wa shugaban gwamnatin Falasdinu shawara Husain Sheikh, sun kuma mika wannan wasikar ne ga mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Amurka mai kula da yankin gabas mai nisa.

 A ranar 25 ga watan Janairu da ya shude, shugaban kasar Amurka ya gabatar da shawarar cewa kasashen Masar da Jordan su karbi bakuncin Falasdinawa daga Gaza.

Tare da cewa Trump din ya ce zaman na Falasdinawa na wani dan karamin lokaci ne,sai dai kasashen larabawan biyu sun ki amincewa da hakan.

Haka nan kuma wasikar ta yi kira da a dauki matakan sake gina Gaza da yaki ya lalata, domin su ci gaba da rayuwa akan kasarsu.

Dangane da makomar Falasdinawa, jami’an diplomasiyyar na Larabawa sun bukaci yin aiki da gwamnatin Donald Trump domin kafawa Falasdinawa kasarsu mai cin gashin kanta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya

 

Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung  November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare