Ɗan Ibo ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya
Published: 31st, January 2025 GMT
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne.
Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna.
Daraktan cibiyar Salama Centre da ke Asibitin Gambo Sawaba ƙofar Gayan Zariya, Hajiya Aishatu Ahmad, ta shaida wa Wakilin namu cewar a ranar 27 ga watan ɗaya na wannan shekarar ne hukumar ‘yan sanda da ke Kasuwar Mata a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta kawo wani mai suna Oguchwku Cibiyarsu tare da wasu yaran Makarantar Firamare ta Jafaru LEA su biyu.
Daraktar ta ce, bayan kammala binciken yaran, bincike ya nuna cewa an yi lalata da su.
Daraktan cibiyar Hajiya Aishatu Ahmad ta ce, sun ɗora yaran akan magani, kuma sun ba ‘yan sanda sakamakon, tare da tura ƙwafin sakamakon zuwa ga Kwamishinan jinƙai da walwala ta jihar Kaduna domin ɗaukar mataki.
Babban jami’I a ofishin ‘yan sanda na Kasuwar Mata ya ce duk da taƙardama akan rashin yarda da sakamakon binciken da Asibitin Gambo Sawaba da iyalan wadda ake zargin suka yi sai na sake tura su asibitinmu na musamman domin ƙara binciken kuma yanzu haka mun tura su zuwa Kaduna.
Duk ƙoƙarin kiran wayar, mai magana da yawan rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna ASP Mansur Hassan, tare da tora saƙon karta kwana amma har zuwa wannan lokacin bai amsa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp