2025-09-17@21:49:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6135
«ne duniya ta»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan fara bikin harshen Hausa ta duniya shekaru goma da suka gabata ne dai manazarta suke bayyana irin cigaba da habbakar da yaren ya samu. Harshen Hausa ya samu zama a mataki na 11 cikin harsunan da ake amfani dasu a fadin duniya tare da fatan nan bada jimawa ba zai dara hakan. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba DAGA LARABA: Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin cigaba ko akasin haka da harshen Hausa da aladunta suka samu cikin shekara goma. Domin...
Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics. Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba. Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Dangane da ci gaban da halin da ake ciki a Gaza, Abdel Aty ya gabatar da kokarin Masar tare da hadin gwiwar bangarorin shiyya da na kasa da kasa, na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta ba da tabbacin sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni da kuma bude hanyar shigar da kayan agaji. Ya lura da matsaloli na jin kai da suka biyo bayan manufofin Isra’ila na haifar...
Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa. A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa. A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci. A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani. Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa...
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayar da rahoton a ranar Litinin cewa mutane sama da rabin miliyan ne suka koma Khartoum a cikin watan Yuli, wanda ke nuna karuwar komawa babban birnin Sudan da yaki ya daidaita. A cewar hukumar, kimanin mutane 500,074 ne suka koma birnin, wanda ya karu da kashi 400 cikin 100 idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a watan Yuni. Wannan ya biyo bayan kwato birnin ne da sojojin Sudan suka yi daga hannun mayakan Rapid Support Forces (RSF) a cikin watan Maris, a ci gaba da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na kaddamar da shirye-shiryen sake gine-gine da kwantar da hankula. Hukumar ta IOM ta...
Kafar CGTN da jami’ar Renmin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar inganta tuntubar juna tsakanin kasa da kasa a sabon zamani. An kuma gudanar da nazarin ne tsakanin mutanen manyan kasashen duniya da na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wannan Litinin ɗin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sauka a Brasilia da ke ƙasar Brazil, inda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu, domin amsa gayyatar da ƙasar ta yi masa. Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban Brazil, Inacio Lula da Silva, inda aka yi masa faretin ban girma irin na soji da ake karrama shugabannin ƙasashe. PDP ta miƙa wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027 Gwamnatin Kano ta musanta karkatar da N6.5bn daga baitul-malin jihar Ana saran shugabannin biyu da jami’ansu za su tattauna a kan batutuwa da dama da suka shafi sufurin jiragen sama da noma da harkar ma’adinai. Kazalika, shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka...
Albarkacin taron koli na Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO) na 2025, an yi bikin kaddamarwa na kasashen SCO, da shiri mai taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” da CMG ta shirya a yau Litinin a nan birnin Beijing. Tun daga yau, za a fara watsa shirin a manyan gidajen talibijin na Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Pakistan, Iran, da Belarus da sauransu. Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, shirin ya zabi labarai masu ban sha’awa na yadda Shugaba Xi Jinping ke kula da al’adu da ci gabansu, don bayyana muhimman ra’ayoyinsa game da al’adu. A karkashin ruhin “Shanghai”, za a ci gaba da rubuta sabon labari na hadin kai da rabon makoma tsakanin al’adu, tare da kafa kyakkyawar makoma ta bil’adama...
Amma, a cikin wata sanarwa mai kakkausar murya da ya fitar a ranar Litinin, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Sanusi Bature DawakinTofa, ya karya rahoton da cewa “aiki ne na tatsuniyoyi, wadanda abokan hamayyar siyasa suka shirya su, domin bata wa gwamnati suna don su samu madafun iko gabanin zaben 2027. “Kowane tsabar kudi da ke fita a cikin Ma’aikatun gwamnati a tsare suke yadda ya kamata a cikin kundin kasafin kudi na jihar. Don haka, babu wani mutum a cikin gwamnati da ke kula da kudaden jama’a ba tare da wata manufa ta musamman ba,” in ji sanarwar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Har ila yau, rahoton ya ce, matakin na Amurka muradu da dabarunta na siyasar duniya kadai yake karewa, yayin da take dogaro da karfin soja wajen haifar da tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da ma tsarin harkokin tekun na duniya. Bugu da kari, ya soki ayyukan Amurka yana cewa, sun saba doka, ba su kamata ba, kuma suna nuna fuskoki biyu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Wata mata ta mayar da N4.8m da aka yi kuskuren tura wa asusunta a Maiduguri A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027. A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance. Damagum wanda ya shafe fiye da...
Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiya sun bukaci hadin kan kasashen musulmi don magance matsalolin da al-ummar falasdinu take faskanta a gaza. Sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen musulmi su san yadda zasu yi don nisar da abinci zuwa yankingaza da kuma kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. Tashar taabijin ta Presstv ta bayyana cewa Abbas Aragchi ya tattauna da tokwaransa na kasar Saudia Faisal bin Farhan al-Saud ne a gefen taron ministocin harkokin waje na kasashen musulmi OIC na gaggawa wanda aka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiya . Banda haka ministocin sun yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen wadanda suka hada da kasuwanci, yawon shakatawa, da kuma al-adu. Sun kuma ya magana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na biyu, lamarin da yanzu kowa yake nadama saboda an jefa ƙasar cikin tsanani da tsadar rayuwa da rashin tsaro. Za a yi amfani da Hausa wajen samar da zaman lafiya — Abdulbaqi Jari Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru A yayin wani taro na Arewa maso Yamma da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, madugun ƙungiyar na ƙasa, Dokra...

Sin Ta Shiga Jerin Kasashe 3 Dake Sahun Gaba Wajen Gudanar Da Cinikayya Da Kasashe Da Yankunan Duniya 157
Shugabar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta ce Sin ta shiga jerin kasashe uku dake sahun gaba wajen gudanar da cinikayya da kasashe da yankunan duniya 157. Sun Meijun, ta bayyana hakan ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai da ta gudana, inda ta ce a shekarar 2024 darajar hada-hadar cinikayya tsakanin Sin da kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya ta kai yuan tiriliyan 22, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan uku, ciki har da wadanda suka hada da sama da kaso 50 bisa dari na jimillar hada-hadar shige da ficen hajoji. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Za a yi amfani da harshen Hausa a matsayin hanyar samar da zaman lafiya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya karo na goma (10), wanda za a gudanar a Daura da ke Jihar Katsina, a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025. Jagoran taron, Abdulbaqi Aliyu Jari, wanda shi ne ya ƙirƙiri wannan rana, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina. Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 35 a iyakar Najeriya da Kamaru Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya Ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala, kuma manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya tuni sun fara isowa domin halartar bikin. Jari ya ce an tsara taron ne domin baje kolin al’adun Hausawa...
Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’adda kimanin 35 da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne a kusa da iyakar Najeriya da Kamaru. ’Yan ta’addan sun taru a yankin Kumshe, wani gari da ke kan iyaka a Jihar Borno, da safiyar Asabar domin kai hari kan sansanin sojoji da ke yankin. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, sojojin kasa sun nemi taimakon rundunar sojin sama, inda jiragen yaki suka kai hare-hare a wuraren da aka gano ’yan ta’addan sun taru. “Ranar Asabar, 23 ga Agusta, sojojin runduna ta 21 sun dakile wani hari da ’yan ta’adda suka kai da daddare, inda jiragen yaki suka ragargaza ’yan ta’addan,” in ji wata majiya. Binciken bayan harin ya nuna cewa an...
Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a. Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a jami’ar Najeriya, yana tsare har zuwa yanzu. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Jakadan Falasɗinu da ke Najeriya amma hakarsa ta cin ma ruwa ba. Rushe Kasuwar Alaba Rabo: Mun yi asarar fiye da N20bn — ’Yan Arewa Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 ke taro a Abuja Ibrahim ya shahara wajen kare muradun Falasɗinawa ta kafafen yaɗa labarai, musamman a ’yan watannin nan da...
’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi. Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a Kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata a jihar. A karo na biyu a ’yan kwanakin nan mahukunta a Jihar Legas suka rushe sassa da dama na kasuwar, wadda ta yi fice da kasuwancin kayan abinci da dabbobi da karafa da sauran kayan masarufi, wacce Hausawa suka kafa a shekarar 1979. A cikin watan Mayun 2024, jami’an hukumar ’yan...
Kwamandan sojojin Iran ya yi barazanar mayar da martani mai muni da zai haifar da nadama ga makiya Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran da jarumtarsu suna tsayawa da dukkan karfinsu wajen fuskantar barazanar makiya. A yayin ziyarar da ya kai Jami’ar Kimiyyar Sojin Ruwa ta Imam Khumaini (RA) da ke tashar jiragen ruwa ta Noshahr ta arewacin kasar Iran a jiya Lahadi, Manjo Janar Hatami ya bayyana cewa: “A yau Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da matsayi na musamman a tsakanin kasashen yankin, ya kamata makiya su sani cewa al’ummar kasar na kwarai a cikin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye suke, kamar yadda suka saba a baya, da...
Kafofin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun yarda da gazawar dakile Yemen daga ci gaba da ayyukan soji kan Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, wadanda tashar 12 da tashar ta 13 ke wakilta, sun amince da cewa: Hare-haren da makiya ke kaiwa kasar Yemen, ya gaza hana sojojin Yemen harba makamai masu linzami zuwa yankunan Isra’ila da aka mamaye. Waɗannan tashoshi na yahudawan sahayoniyya sun yi imani cewa; Da’awar iya dakile hare-haren sojojin Yemen kan yankunan Isra’ila, rudu ne kawai na jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila ganin tsawon lokacin da za a iya dauka domin hana kai waɗannan ayyuka saboda “haɗarinsu.” Tashar talabijin ta yahudawa ta 13 ta yarda cewa harin na baya-bayan nan da aka kai kan kasar Yemen ba...
Wani babban kusa a kungiyar Hamas ya yi Allah wadai da kin amincewar firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu na kin amincewa da sabuwar shawarar da masu shiga tsakani suka yi na tsagaita bude wuta a Gaza. Mamban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Bassem Naim, ya fada a ranar Lahadin da ta gabata cewa da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar sulhun Gaza don kare kansa da kuma majalisar ministocinsa na masu tsattsauran ra’ayi, da kuma zafafa yakin da ake yi kan al’ummar Gaza. Ya bayar da misali da rahotannin da kafafen yada labarai na baya-bayan nan da ke nuni da cewa gwamnatin kasar ta yi watsi da yarjejeniyar wani bangare da Hamas, yana mai cewa Tel Aviv na son cimma cikakkiyar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa. Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba...
A nasa ɓangaren, Farfesa Usman Yusuf Bugaje ya gargadi gwamnati cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, matsalar za ta iya bazuwa zuwa manyan birane a jihar. A ƙoƙarin gwamnati, rundunar sojin Nijeriya ta sanar da shirin kafa sabuwar bataliya a ƙaramar hukumar Malumfashi domin ƙarfafa yaƙi da tashe-tashen hankulan ƴan bindiga a jihar Katsina. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian yayin da yake jinjinawa bayanan goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi a ranar Lahadin da ta gabata ya rubuta cewa: “Ina mika godiya ta musamman ga Jagora bisa kyakkyawan ra’ayi da goyon bayan da yake bayarwa, mu saurari shawararsa ta hadin kai da hadin kan kasa daga gare shi.” Shugaba Masoud Pezeshkian yayi wannan jinjina ne biyo bayan jawabin goyon bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya baiwa yunkurin hadin kan kasa da hadin kan al’ummar kasa. Pezeshkian ya rubuta a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadin da ta gabata cewa: “Bisa da kokarin ganin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya isa kasar Saudiyya domin halartar wani babban taro na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi. A yayin da yake jagorantar tawagar diflomasiyya ta kasar Iran, Araghchi ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya a jiya Lahadi domin halartar taron kungiyar OIC da za a bude a wannan Litinin bisa bukatar da Iran da kuma wasu kasashe gabatar na yin hakan. A yayin taron na kwanaki biyu, mahalarta taron za su tattauna kan matsalolin jin kai a zirin Gaza, da yiwuwar kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palastinu, da kuma gurfanar da ‘yan sahayoniya masu laifi a gaban kotu. Kungiyar ta OIC ta ce taron zai mayar...
A yau ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da zama na 102 na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), inda ake sa ran ta yanke hukunci kan wasu jiga-jiganta da ake zargi da cin dunduniyarta, ciki har da Ministan Abuja Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom. Majiyoyi a jam’iyyar sun ce a yayin taron, za a gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin Tom Ikimi, wanda ya ba da shawarar ɗaukar mataki a kan waɗanda ake zargi da yi wa jam’iyyar zangon ƙasa. Har ila yau, taron zai tattauna shirin gudanar da babban taron jam’iyya na ƙasa a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, inda za a zaɓi sababbin shugabanni. Kazalika rahoton...
Malaman addinin Musulunci da shugabannin al’umma sun buƙaci matasan Najeriya da su rungumi rayuwa mai ma’ana bisa koyarwar addini, suna gargaɗi cewa watsi da tarbiyyarsu na iya jefa makomar ƙasa cikin haɗari. An yi wannan kira ne a taron ’Light of Guidance Youth Conference 2025’ da aka gudanar a Abuja, wanda ƙungiyoyin Light of Guidance Foundation da Ma’aruf Foundation suka shirya. Uwargidan Gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Hafsat Kollere-Buni, ta shaida wa mahalarta taron cewa matasa su ne “kadarar ƙasa mafi daraja,” don haka dole a jagorance su da koyarwar Musulunci domin su jagoranci al’ummarsu cikin mutunci. “Idan muka jagorance su bisa koyarwar Musulunci, za su kai al’ummarmu gaba cikin martaba da mutunci. Amma idan muka yi watsi da su, muna...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II. Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe Malamin ya rasu a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarsa a unguwar Jan Kai da misalin ƙarfe 5 na yamma. Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ta bakin Daraktan Yaɗa Labaransa, Isma’ila Uba Misilli. Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga ɗariƙar Tijjaniyya, iyalansa da kuma al’ummar jihar. “Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan marigayi, ɗariƙar Tijjaniyya, Fityanul Islam...
Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa Najeriya za ta karɓi rancen dala miliyan 190 daga Ƙasar Japan domin inganta wutar lantarki. Wannan na cikin wata sanarwa da ma’aikatar lantarki, yayin da ake gudanar fa taron ƙasashen Afirka da ke gudana a birnin Yokohama na Ƙasar Japan. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Tawagar Najeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta halarci taron. Rancen zai fito ne daga hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA), kuma ana sa ran zai taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ɗorewa a yankunan da ba su da isasshiyar wuta. Ma’aikatar ta kuma ce wannan lamuni ya zo ne a matsayin ƙari...
Jam’iyyar ADC a Jihar Gombe, ta sanar da korar tsohon ɗan takarar gwamnanta na shekarar 2015, Nafiu Bala, bisa zargin yi mata zagon ƙasa. Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a Gombe. An harbe masu garkuwa da mutane 3 a Kebbi Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato A cewarsa, kwamitin ladabtarwa na unguwar Nasarawo ya binciki Bala, inda ya same shi da laifukan cin amanar jam’iyyar wanda hakan ya saɓa wa dokokinta. Ya ce an gayyaci Bala domin ya kare kansa a gaban kwamitin amma ya ƙi bayyana. Barde ya ƙara da cewa kwamitin zartarwa na jihar, ya tabbatar da wannan hukunci,...
’Yan sanda sun samu nasarar kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da ƙwato bindigar AK-47 bayan musayar wuta da su a yankin Shanga na Jihar Kebbi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar. Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sanarwar ta bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru, DPO na Shanga ya gaggauta haɗa jami’an ‘yan sanda da ‘yan sa-kai waɗanda suka fafata da ‘yan bindigar, inda aka kashe uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji. Kakakin ’yan sandan ya ce wannan nasara na da nasaba da...
Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta. An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar. Aminiya ta ruwaito cewa, waɗanda...
An tsinci gawar wani saurayi mai suna Daniel Ekanen, mai kimanin shekaru 18, a gefen wani kudiddifi da ke unguwar Ikot Effanga a Ƙaramar Hukumar Kalaba, Jihar Kuros Riba. Lamarin ya jefa firgici a zukata da kuma zaman dar-dar a cikin mazauna yankin, inda aka ruwaito cewa an kawo marigayin ne wurin dangin mahaifinsa daga ƙauyen Ikot Offiong da ke ƙaramar hukumar Odukpani a jihar. Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu tsafi da sassan jikin ɗan adam ne suka yi kisan, domin kuwa an yanke kansa kafin a jefar da gawarsa a gefen kudiddifin. Wani daga...
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da cewa gobe Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025, ita ce za ta zama 1 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da harkokin addini a majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda ya bayyana cewa ba a samu labarin ganin sabon wata na Rabi’ul Awwal a ranar Asabar, 29 ga Safar ba. Dangote ya ci gaba da zama attajiri mafi arziƙi a Afirka — Forbes An haramta bukukuwan aure a Taraba Farfesa Sambo wanda kuma shi ne Wazirin Sakkwato, ya ce saboda haka, Lahadi, 24 ga watan Agustan 2025, za ta zama 30 ga watan Safar, sannan kuma bisa...
Fitaccen attajirin nan, Aliko Dangote ya ci gaba da riƙe kambinsa na mutum mafi arziƙi a nahiyar Afirka, inda dukiyarsa ta kai dala biliyan $24.4, a cewar sabuwar ƙididdigar da mujallar Forbes ta fitar a bana. Wannan ya sanya shi zama mutum na 88 a jerin masu kuɗin duniya, inda ya rike wannan matsayi da tazara mai nisa a kan sauran attajiran Najeriya. An kama matashi kan zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu An haramta bukukuwan aure a Taraba Abdulsamad Rabiu wanda ya mallaki rukunin kamfanin BUA, shi ne ya biyo bayansa da dukiyar da ta kai dala biliyan $7.2, wanda ya sa shi zama attajiri na 516 a duniya. Sai kuma Mike Adenuga da dukiya mai darajar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan yana samar da lantarki da rage asarar makamashi da kuma samar da kaso 25 na bukatun makamshi na ginin. Haka kuma zai kai ga rage fitar hayakin Carbon tan 500 a shekara. Baya ga haka, ginin na amfani da tsoffin baturan motoci masu amfani da lantarki, wajen adana makamashi. Ana amfani da irin wadannan batura guda 14 wajen adana rarar makamashin da ake samu daga bangon gilas mai zukar hasken rana da samar da makamashi mai tsafta a lokaci mafi samun hasken rana, a farashin yuan 0.22 kwatankwacin $0.031, kan kilowatt 1 a kowacce sa’a. Kuma za a yi amfani da makamashin da aka adana a lokacin da ake bukatar lantarki mai yawa ko kuma lokacin da...
Amma abin takaici, duniya ba ta san laifukan da Japan ta yi wa kasar Sin a lokacin yakin ba sosai. Har yanzu gwamnatin Japan ba ta nemi afuwar Sin da sauran kasashen Asiya da ta jefa cikin ukuba ba. Har ma, ‘yan siyasar Japan masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da gurbata wannan tarihi, a yunkurin gujewa hukunci da al’ummar duniya za su yi musu. Mace macen da aka samu a yakin duniya na 2, abun bakin ciki ne ga dukan bil’adama. Al’ummomin kasashen duniya suna da makoma da tarihi na bai daya, wanda ba za a iya mantawa da shi ba, balle a gyara shi. A bana ake cika shekaru 80 da nasarar yakin kin harin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa mafarkinn da HKI take yi dangane da ‘Isra’ila babba” wani rudu ne, wanda ba zai je ko ina ba, amma kuma zai haddasa rashin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya dama duniya gaba daya. Don haka akwa bukatar daukan mataki mai kwari don dakile shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka, a wani rubutun da yayi a jaridar Asharqul Ausat wanda ake baga ta da harshen larabaci . Ministan ya ja hankalin kasashen duniya a kan wannan tunanin na HKI, wanda ba abinda zai ci gaba da jawowa sai tashe –tashen hankula da kuma hana zaman lafiya a yankin da kuma duniya...

Juyayin Shahadar Jagoran Shiriya Na Iyalan Gidan Manzon Allah Imam Ali Arridha {a.s} A Mash’had Sun Kai 3,500,000
Birnin Mashhad na Iran ya karbi bakwancin maziyarta 3,500,000 daga kasashe 20 a yayin taron tunawa da shahadar Imam Rida (a.s) Dubban daruruwan masu Ziyara daga ciki da wajen kasar Iran ne suke gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida (a.s) a birnin Mashhad mai alfarma da ke arewa maso gabashin kasar Iran. Yayin da masu ziyarar suke ci gaba da isowa, ana gudanar da tarukan makoki a hubbaren da kuma titunan da ke kewaye da hubbaren Imam, inda taron jama’a ya kai kololuwa. Dubban al’ummar Iran ne suka ci gaba da gudanar da isa hubbare daga sassa daban daban na kasar, daga tazarar daruruwan kilomita daga garuruwan su zuwa birnin Mashhad, a cikin...
Ma’aikatar Shari’a ta Sojin Iran ta jaddada cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci barkono ne a idanun makiya Shugaban hukumar shari’a ta sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma sauran dakarun kasar sun kare juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran da kuma al’ummar yankin da ake zalunta da dukkan karfinsu tsawon shekaru 47 da suka gabata. A kodayaushe sun kasance barkono ne a idon maƙiyan Musulunci da ƙasa. Hujjatul-Islam Ahmad Pourkhagan ya gana da babban kwamandan Dakarun Juyin Juya halin Musulunci Manjo Janar Mohammad Pakpour a ranar jiya Asabar a yayin bikin tunawa da shahadar kwamandan Dakarun na ‘IRGC’, Laftanar Janar Salami. Ya ce: Duk da cewa rashin shahidi...
A yau ake gurfanar da wani majinyaci mai shekaru 40, zai gurfana a kotu, bisa zargin cin zarafin wata likita mai suna Fatima Umar Gamsa a asibitin Ƙwararru na tunawa da marigayi Janar Sani Abatch da ke Damaturu Jihar Yobe. Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Yobe, Dakta Umar Aji, ya ce kungiyar ta kai ƙara gaban ’yan sanda kuma tana jiran hukuncin da kotu za ta yanke. “A yanzu shari’ar tana gaban kotu, kuma ƙungiyar ba za ta ce komai ba har sai ta ji sakamakon hukuncin kotun,” Aji ya jaddada. Wanda ake zargin, Ahmed Usman mazaunin rukunin gidajen Abba Ibrahim da ke Damaturu an tsare shi a gidan yari na Potiskum har zuwa lokacin da za a saurari...
Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani. Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin cikin gari ba tare da sanin hatsarinsa ba, suna ɗauka ƙarfe ne da za a sayar. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayya NAJERIYA A...
Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa. Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i da dama a ranar ya mamaye kwalbatoci da magudanan ruwa a yankin. Dan-Ummah Abba, wani magidanci da lamarin ya shafa a Gandun Sarki ya bayyana cewa gidansa da yake zaune a ciki sama da shekara 30 ya rushe a sakamakon lamarin. Daga nan ya roƙi Gwamnatin Jihar Jigawa da ta kawo musu ɗaukin gaggawa. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa. Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu, a gefe guda kuma an kasa gano inda sauran da abun ya rutsa dasu suke. Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a, musamman ‘yan uwan waɗanda abin ya shafa, waɗanda yanzu ke cikin damuwa, jimami da rashin sanin makoma. NAJERIYA A YAU: Dalilan Karyewar Farashin Hatsi A Kasuwanni DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100. Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Bwala ya ce hakan zai kawo saukin rayuwa ga dubban ’yan Najeriya da ke fama da cutar, wadda ke bukatar yin jinya sau da dama a kowane mako. “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tallafin tarihi domin rage farashin jinyar ciwon koda ga ’yan Najeriya. An rage farashin kowace wankin ƙoda daga N50,000 zuwa N12,000 kacal,...
Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya. Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya sanar da rasuwar a yammacin ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025. Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyalan Gwamna da kuma al’ummar jihar baki ɗaya. Sanarwar ta kara da cewa kafin rasuwarsa, Marigayi Alhaji Ododo ya kasance mutum mai daraja wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen gina halaye da dabi’un ɗansa, Gwamna Ahmed Usman Ododo. Ta kuma miƙa ta’aziyya ga Gwamna Ododo, iyalansa da dangin Ododo gaba ɗaya, tare da addu’ar Allah ya ba su ƙarfin juriya da haƙuri.
Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas. Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa. Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a unguwar suka ce ya samo asali ne daga zargin da Doctor ke yi wa Ima, wanda ya rikide zuwa tashin hankali. Mai kula da gidan da lamarin ya faru ya kai rahoto ofishin’yan sanda na Azikiwe Division, Mile 2 Diobu, wanda hakan ya kai ga cafke wanda ake zargi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa Mutane 62 da aka sace sun tsere...
Wasu masu garkuwa da mutane sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa rabon kudin fansar mutanen da suka sace a Jihar Nasarawa. Jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku da tsabar kudi Naira miliyan 6.9 daga motar ’yan bingidar bayan hatsarin motar a yankin Garaku, daura da wani shingen bincike na Jami’an Kula da Lafiyar Ababen Hawa (VIO) Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta ce ta kwato makamai masu haɗari da kuɗi sama da naira miliyan shida, bayan wani haɗari da ya faru a kusa da Angwan Mayo. ’Yan sanda daga yankin Garaku sun ce da misalin ƙarfe 9:08 na safe, suka samu kiran gaggawa dangane da haɗarin motar kirar Opel Vectra wadda shaidu suka ce mutane biyu da ke...
Mutum 62 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sama da wata guda sun tsere bayan rundunar soji ta kai farmakin sama da ƙasa a maboyar ’yan ta’adda a Karamar Hukumar ƊanMusa, Jihar Katsina. Farmakin da aka kai a ranar Asabar da misalin ƙarfe 5:10 na yamma ya gudana ne bisa sahihan bayanan leƙen asiri, inda dakarun sojin sama da na ƙasa suka haɗa kai wajen kai hari a kauyen Jigawa Sawai, wanda ke iyaka da Jihar Zamfara. A cewar sanarwar da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Katsina ta fitar, farmakin ya tilasta ’yan bindigar guduwa, lamarin da ya ba wa mutanen da aka yi garkuwa da su damar tserewa cikin ruɗani. Wasu daga cikin waɗanda suka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Iran ba za ta amince da duk wani sauyi a kan iyakokin yankin siyasa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce gabanin ziyarar shugaba Masoud Pezeshkian zuwa kasar Armeniya cewa tabbatar da yanayin siyasar yankin bai canza ba, shi ne batun tuntubar da shugaba Pezeshkian ke gudanarwa a birnin Yerevan fadar mulkin Armeniya. A cikin wata sanarwa ta musamman ga kamfanin dillancin labaran IRNA dangane da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Jamhuriyar Azarbaijan da Armeniya, karkashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump, da jajayen layukan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gindaya, ministan harkokin wajen kasar Iran ya ce: A gobe, shugaba Pezeshkiyon zai ziyarci birnin Yerevan, inda zai zauna...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabu 16 a jihohi 12 na ƙasar nan. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaban ƙasa ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa gudanar da zaɓen lafiya ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba. A cewar sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe kujeru 12, yayin da jam’iyyar APGA ta samu biyu. Jam’iyyar PDP da jam’iyyar NNPP kowanne ya samu kujera ɗaya. Shugaba Tinubu ya taya sabon shugaban jam’iyyar APC na...
Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta bada kwangilar aikin ne akan kudi sama da Naira miliyan dubu 8 da miliyan 200 tare da wa’adin kammala aiki a watanni 18. Kazalika, Malam Umar Namadi ya kuma bude aikin gina hanyar Farin Daba, Galo Babba zuwa Galo Karama da aka ba da kwangilar su kan naira miliyan dubu shida da miliyan 300. Ya kara da cewar, aikin zai saukaka wa manoma kai...
Wani jirgin ruwa ɗauke da mutum sama da 30 da kuma babura takwas, ya nutse a garin Kojiyo da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin mai suna Nasiru Goronyo, ya ce jirgin ya yi hatsari ne a kogin garin bayan ya ɗauki mutane da kaya da suka fi ƙarfinsa. Kano: NNPP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Ghari/Tsanyawa Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025) Ya ce: “Mutane 30 da jirgin ya ɗauka ba a ga ko ɗaya daga cikinsu ba tukuna. “Sai dai an fitar da babur guda ɗaya daga cikin takwas da suka nutse, amma kayan da mutane duk sun ɓace.” Ana jiran ƙarin bayani daga hukumomi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Kudancin Caucasus cikin lura Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i, ya yi nuni da yadda Iran ke daukan abubuwan da ke faruwa a yankin arewa maso yammacin kasar da muhimmanci, yana mai jaddada cewa: “Suna sanya idanu kan abubuwan da suke faruwa, kuma ba sa sassauci ko daukarsa da rashin muhimmanci.” A wata hira da aka yi da shi ta kafar yada labarai, Baqa’i ya fayyace matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan abubuwan da suke faruwa a yankin Kudancin Caucasus na baya-bayan nan, inda ya jaddada muhimmancin siyasa, tattalin arziki da siyasa a yankin ga Iran da kasashe makwabta musamman...
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wata barazana da makarkashiyar ‘yan sahayoniyya da Amurka Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwa a ranar 16 ga watan Agusta na tunawa da dawowar fursunonin da aka ‘yantar zuwa mahaifar ta daular Musulunci. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Fursunonin da aka ‘yantar madaukaka, sune ainihin bayyanar gwagwarmaya da tsayin daka na ruhi da kuma bege na dabaru. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 16 ga watan Agusta na bikin tunawa da dawowar ‘yantattun fursunoni (fursunonin yakin shekara ta 1980-1988 a yakin da aka kakaba kan Iran), da tunawa da yakin kwanaki 12 da...

Gwamnatin DR Kongo Ta Nuna Rashin Amincewarta Da Zabin Kenya Kan Wajen Da Zata Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Kasarta
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ki amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta sanar da kin amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma da ke gabashin kasar, duba da matakin da ya saba wa ka’idojin diflomasiyya, duba da yadda Kongo ke ganin ci gaba da kasancewa a birnin na Goma ya saba ka’ida. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar din da ta gabata, mahukuntan kasar Kongo sun bayyana mamakinsu kan sanarwar da fadar shugaban kasar Kenya ta bayar na nadin Judi Kiara Nkumiri a matsayin karamin jakadanta a birnin Goma ba tare da amincewar ma’aikatar harkokin wajen Kongo ba. Sun dauki wannan a matsayin...
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan tsawon watannin da suka shafe ba tare da wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Gwamnonin Arewa sun yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Zuru Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood Sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu saboda rashin tiransufoma, lamarin da ya jefa su cikin ƙunci da wahala. Muhammad Idris Gargajiga, wanda ya yi magana da wakilinmu a madadin mazauna yankin, ya ce duk lokacin da suka kai ƙorafi sai a ce musu yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da suka kira da...
Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A. Zango ya agwance da jaruma Maimuna Musa. Marubuciya a masana’antar, Fa’iziyya D. Sulaiman ce ta sanar da auren nasu a wani rubutu da ta wallafa a Facebook. Wani mutum yanke makazutarsa a Borno Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025) Auren dai ya zo cikin bazata, domin babu wanda ya san da neman sai labari aka ji jaruman sun shiga daga ciki. Jaruma Maimuna matashiya ce wadda tauraronta ya fara haskawa a Kannywood. Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa’in, Garwashi da sauransu. A baya-bayan nan ma fitacciyar jaruma a masana’antar, Rahama Sadau, ita ma ta yi aure, lamarin da ya bai wa mutane da dama mamaki.
An ceto wani mutum mai shekara 50 ya yi yunƙurin kashe kansa a garin Bama na Jihar Borno. Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Juma’a a unguwar Hausari, inda al’ummar yankin ne suka kai masa ɗauki. Shaidu sun ce mutumin ya daɓa wa kansa wuƙa har sau uku a ciki, kafin ya yanke mazakutarsa da wuƙar. An ce ya aikata hakan ne saboda tsohuwar matarsa, daga garin Konduga, wadda ya yi wa saki uku, ta ƙi komawa gidansa. Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025) Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau ’Yan sanda sun jagoranci tawagar ’yan sintiri zuwa wurin, inda suka gano tare da ƙwace wuƙar, sa’annan suka kwashi magidancin zuwa Babban Asibitin Bama, inda...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa shuwagabannin kasashen turai kan cewa ya amince da shawara shugaba Putin na musayar kasa don samar da zaman lafiya. Majiyoyi biyu wadanda basa son a bayyana sunayensu kuma kusa da Trump a taron na Alaska ya bayyanawa jaridar ‘The guardian’ ta kasar Burtania a jiya Asabar kan cewa, Trump ya fadawa masu kan cewa Zeleski ya amince da mikawa Putin Dombasa sannan rasha kuma zata tsaya inda take, ba zata karbi sauran yankunan Donbas da suke hannun Ukraine ba. Don haka putin ya dage kan cewa dole Ukraine ta fice daga Dobas Kwata-kwata. Labarin ya ce har yanzun Ukraine tana iko da Kramatorsk da Sloviansk a yankin Donestk. Sannan yankunan kudancin Ukraine Kherson...
Dubban mutane a birnin London sun yi cincirindo a kofar shiga sansanin sojojin sama da ke arewa maso yammcin birnin London inda suke zargin gwamnatin kasar da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jiragen yakin F-35 na kasar Burtania suna shawagi a tekun medeteranin inda suke taimakawa HKI yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza. Don haka gwamnatin kasar tana da hannui a kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza. Tun cikin watan octoban shekara da 2023 mutane daga bangarori daban-daban a kasar Burtaniya suke zanga-zanga don neman a kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa a Gaza, sannan a bawa kasar falasdinu cikekken yanci bayan...
An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna. Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba. Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasara A zaɓen da aka gudanar a Zariya, Isa Haruna Ihamo na jam’iyyar APC ne ya samu nasara da ƙuri’u 26,613. Nuhu Sada Abdullahi na jam’iyyar SDP ya zo na biyu da ƙuri’u 5,721, yayin da Mahmud Abdullahi Wappa na PDP ya samu ƙuri’u 5,331. Tun watan Ramadan muke cikin duhu — Al’ummar Jauro Jatau NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a Kano Farfesa Balarabe Abdullahi, wanda ya bayyana sakamakon zaɓen, ya tabbatar da...
Al’ummar unguwar Jauro Jatau da ke kan hanyar Bypass a Ƙaramar Hukumar Akko, Jihar Gombe, sun koka kan dogon lokacin da suka shafe ba tare da samun wutar lantarki ba. Sun roƙi gwamnati, ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki cikin gaggawa. Tun a watan Ramadan Al’ummar sun bayyana cewa tun watan azumin Ramadan da ya gabata suke cikin duhu, sakamakon ƙonewar transforma da ke yankin, lamarin da ya bar su cikin ƙunci har tsawon watanni, da ke shafar rayuwar su ta yau da kullum. Wani daga cikin mazauna yankin, Muhammad Idris Gargajiga, ya bayyana cewa duk lokacin da suka kai ƙorafi ana gaya musu cewa yankin ba shi da rumfar zaɓe, abin da ya...
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar. Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa. Zaɓen cike gurbin na Babura-Garki ya fara ne da tsauraran matakan tsaro a fadin mazabar. Jami’an tsaro suka kasance a rumfunan zaɓe da wuraren da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya. A daidai ƙarfe 8:30 na safe, jami’an Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) sun isa rumfar Garki-Kofar Fada (003) inda suka fara shirye-shiryen zaɓe. Mr Ibrahim Shehu, jami’in zaɓe a rumfar, ya shaida wa...
Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne a daren Asabar a wani asibiti da ke birnin London bayan fama da jinya. Marigayin ya bar mata hudu da ‘ya’ya bakwai. A cikin sakon ta’aziyya, Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana alhinin ta kan rasuwar Sarkin, tare da mika ta’aziyya ga iyalansa, Majalisar Masarautar Zuru, al’ummar Zuru da daukacin Jihar Kebbi. “Gwamnati na roƙon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba...
Mutum sama da 600 sun rasa matsuguni sanadiyyar wata mummunar ambaliya da ta afku a garin Potiskum da ke Jihar Yobe. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta bayyana cewa kimanin mutane 612 ne ta samarwa matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta mamaye sama da gidaje 102 a garin Potiskum. Wannan ambaliya ta afku ne a ranar Juma’a 15 ga watan Agusta shekara 2025. NEMA tare da haɗin guiwar ma’aikatar ba da agaji ta jihar SEMA, sun killace mutanen a wani sansanin wucin gadi da aka kafa a makarantar firamare ta Sabon Gari, yayin da wasu ke samun mafaka a wurin ‘yan uwa da abokan arziki. Ya zuwa yanzu, jami’an hukumomin NEMA da SEMA tare da haɗin guiwar Ƙungiyar...
Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda ita ma Iran din take Kallon wannan alaka tsakaninta da Saudiyya. Inda ya kara da cewa “Mun ga irin goyon bayan da Saudiyya ta bayar kan shawarwarin nukiliyar da aka yi a baya-bayan nan, wanda hakan abin yabawa ne.” Har ila yau, ya yi ishara da cewa, magance da kuma kula da al’amurran da suka shafi yankin gabas ta tsakiya abu ne mai yiyuwa idan...
Jami’an tsaro sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru, ciki har da shugaban ƙungiyar, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Baraa. An daɗe ana zarginsa da kitsa hare-hare masu yawa a Najeriya. ’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13 Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne, ya tabbatar da kamen a wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, a ranar Asabar. Ya bayyana cewa an cafke Abu Baraa a watan Yuli bayan shafe tsawon watanni ana bin diddiginsa. Haka kuma an kama wani shugaban ƙungiyar, mai suna Abubakar Abba. Ribadu, ya...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa. Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa ya ƙi ba shi kuɗin da ya nema don yin kasuwanci. Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13 Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya A ranar 11 ga watan Agusta, Bello ya shaida wa iyayensa cewa zai tafi Ibadan, amma maimakon haka ya ɓoye kansa a Ipele. Daga nan ya riƙa kiran iyayensa da abokansa yana...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s} Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}. A yayin da yake halartar shirin na musamman na “muryar ku a ko’ina” da ake watsawa a gidan rediyon Saba, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna batutuwan da suka shafi gagarumin tattakin Arbaeen da tasirinsa ga duniyar musulmi. A farkon hirar, minista Araqchi ya mika sakon gaisuwarsa ga masu ziyarar Arba’een a birnin Karbala, inda ya bayyana farin cikinsa da halartar wannan gagarumin taron juyayi. Yana...

Kungiyar Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin Majalisar Dinkin Duniya
Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta mayar da martani da cewa: Shigar da ƙungiyar cikin jerin “baƙin littafi’ na Majalisar Dinkin Duniya ba shi da inganci Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana rashin amincewarta da kakkausar suka ga rahoton da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya fitar kan cin zarafin mata da ke da alaka da rikice-rikicen makamai, wanda ya hada da kungiyar ta Hamas a cikin jerin bakin littafin wato “blacklist”, yayin da Guterres ya yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yari. Kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Juma’a cewa: Wannan matakin bai dace ba a bisa doka, ta kuma yi gargadin...
Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye. Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba. APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Wakilinmu ya zagaya rumfunan zaɓe, inda ya gane wa idonsa yadda aikin zaɓen ke tafiya a hankali saboda matsalar na’urar tantancewa. Malam Halliru Hamza, ya ce shi ma bai samu damar kaɗa ƙuri’a ba saboda na’urar taƙi ta tantance shi. Ya ƙara da cewa mutane da dama ba su fito ba saboda yadda siyasa ke tafiya ba tare da ci gaba ba, sai tsadar rayuwa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen. Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu. Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano. Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro suna aikin tabbatar da zaman lafiya domin a gudanar da zaɓen cikin lafiya. HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna “Dukkanin mutanen da muka gani suna kawo matsala an kama su, kuma zaɓen yana tafiya lafiya. “Na gamsu sosai da yadda komai ke tafiya. Kayan zaɓe sun isa a kan lokaci,...
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a cikin al-amuran sharia da kuma na harkokin kasashen waje, yana tir da da allawadai da mataimakiyar shugaban hukumar ICJ mai hukunta manya-manyan laifuka ta duniya, Julia Sebutinde wacce ta bayyana a fili tana goyon bayan HKI a yakinn Gaza. Labarin ya kara da cewa, mataimakin ministan Kazem Gharibabadi ya bayyana kidemewarsa da abibda alkalar ta fada, ya kuma bayyana cewa hakan wani ci baya ne a cikin aikin alkalanci a wannan babban kotun, A ranar 10 ga watan Augustan da muke ciki ne Sebutinde ta bayyana a fili kan cewa Ubangijinta ya umurceta da ta tsaya a bangaren HKI , Sanna alamun tashin kiyama...
Mutane kimani 60 ne zasu gurfana a gaban kotu a kasar Burtaniya, saboda goyin bayan kungiyar mai goyon bayan Falasdinu, wata :frre Palastine’ wacce kuma gwamnatin ta bayyanata a matsayin kungiyar yar ta’adda. Labarin ya kara da cewa wannan shi ne zanga zangar da aka fi kama mutane tun lokacinda aka fara zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a shekara ta 2023. Masu goyon bayan Falasdinawa 3 wadanda aka kama a cikin watan Julin da ya gabata, an rika na gabatar da su a gaban kotu kuma kuma za’a tuhumesu karkashin doka da “Yan ta’adda na kasar. Yansanda sun bayyana cewa kotu tana iya yanke hukuncin zaman gidan kaso har na tsawon watanni 6 a kan ko wanne daga cikinsu. A...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su shiga yaki a ko dauce, amma yana ganin yiyuwar a sake shiga yaki da HKI nan kusa yana da wuya. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Abbas Argchi yana fadar haka, a daren Ashamis da ta gabata, a lokacinda ya kai ziyarar Karbala don ziyarar 40 na Imam Hussain,(a) Ministan ya bayyana cewa, a halin yanzu, mutanen kasar Iran suna da hadin kai a tsakaninsu da kuma gwamnatin kasar , yace makiya zasu so raba kan mutanen kasar da shuwagabanninsu da kuma sojojin kasar wadanda suke bada rayukansu don kare kasar da kuma kare mutanen kasar. Ministan ya kammala da cewa a yakin...
Ga hotunan yadda ake gudanar da zaɓen cike gurbi a sassan Najeriya.
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kama mutumin a wani otel da ke hanyar Turunku a cikin birnin Kaduna. A cewar rundunar ’yan sandan binciken farko da aka gudanar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya shirya yin amfani da kuɗaɗen ne wajen sayen kuri’u A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ke ya amsa laifinsa kuma ya roki a yi masa sassauci. A wata sanarwa da kakaki rundunar,...
A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin kwanciyar hankali Ƙananan hukumomin Batsari, Jibiya da Ɗanmusa na daga cikin wuraren da aka samu wannan ci gaba. Wasu manoma da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana farin cikinsu da yadda rayuwa ke dawowa dai-dai. Malam Rabe, manomi daga Nasarawa a Ƙaramar Hukumar Jibiya, ya ce: “Mu kam yanzu sai mu ce Alhamdulillahi. Lallai sulhu alheri ne a tsakanin al’umma. Ni rabon da na...
Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli. “Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu...
Shugaban majaliasar gudanarwa na kasar Sudan kuma babban hafsan hafsan sojojin kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alkawarin fatattakar dkarun RSF, tare da kawar da “duk wata dama ta yin sulhu.” Kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyyay a bayar da rahoton cewa, al-Burhan ya ce sojojin za su ci gaba da yaki ko ta halin kaka, kuma ba za su ci amanar sadaukarwar wadanda aka kashe a rikicin ba. Al-Burhan ya yaba da irin tsayin dakan da sojojin suka yi a manyan garuruwa irinsu El Fasher, Babanusa, da Kadugli, yana mai cewa suna ci gaba da kare kasar ta kowace fuska. Majiyar Al-Mayadeen ta bayar da rahoton cewa, Al-Burhan ya gabatar da wani fayil na tsaro da ke...
Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi. Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana hakan ta gidan talabijin na kasar a yammacin jiya Alhamis, inda ya ce an shawo kan lamarin gaba daya, kuma an fara gudanar da bincike. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula na siyasa, kuma ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ‘yan kwanakin nan kan tsare jami’an soji. Hukumomi sun bayyana dan kasar Faransa...

Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
“Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun. “Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da...
Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa. Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin domin jajantawa iyayensa da ‘yan uwansa . “kwamishinan ya Kara da cewa ‘Mai girma gwamna Uba Sani Yaso yazo da kansa amma bisa wasu abubuwa da suka bijiro hakan ya sanya ya wakilto mu saboda haka gwamna ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Abubakar”. Maiyaki, yace domin ganin an dakile matsalar yawaitar tu’ammali da muyagun kwayoyi, gwamnatin jihar Kaduna ta Kafa wani...
Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye. 2. Kula da walwalar sojoji da karfafa musu gwiwa Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta...
A jiya Alhamis ne aka kaddamar da gasar wasanni ta mutum mutumin inji ta duniya a birnin Beijing na kasar Sin, wadda ke gabatar da sabbin ci gaban da aka samu a bangaren aiki da basira da motsi, wajen kera mutum mutumin inji. Kungiyoyi 280 daga kasashe 16, ciki har da Amurka, da Jamus, da Italia ne za su fafata a gasar da za a yi daga Juma’a zuwa Lahadi, a dakin wasan gudun kankara na kasa. Mutum mutumin injin za su fafata ne cikin wasanni 26 na motsa jiki, kamar gudu, da dogon tsalle, da sarrafa jiki, da kwallon kafa, da ma wasu ayyukan da suka shafi basira a fannoni daban-daban kamar jigilar kayayyaki, da ware magunguna, da aikin...
Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu. Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani. “Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance. “’Yan kasuwa da ke habaka...
Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara bukatun al’umma, da tabbatar da dorewar samar da aikin yi da daidaiton farashin kaya, da kuma raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, inda aka cimma sabbin nasarori kan neman ci gaba mai inganci. A fannin masana’antu kuma, yawan kayayyakin da aka samar ya karu da sauri, kana, aikin kera na’urori da aikin samar da kayayyaki da fasahohin zamani suna bunkasuwa kamar...
An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar HKI da yaren Hebru mai suna Yedioth Ahronoth yana fadar cewa an gano gawar sojan dan shekara 28 wanda ba’a bayyana sunansa ba a dajin dajin sweezland kusa da yankin tiberias a yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, idan ya tabbata sojan ya kashe kansa ne to kuwa shi ne 17 da suka kashe kansu tun bayan fara yaki a gaza a shekara ta 2023. Ahronoth ya cewa sojan ya yi aiki da runduna ta 99 a gaza a cikin yan makonnin da suka gabata. Sannan a halin yanzu...
Ita ma da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai bukatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa. Hakazalika Maryam ta jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya babu yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani. “Ba maganar talauci idan zaman lafiya da adalci sun tabbata.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Sin Ta Soki Lamirin Amurka Dangane Da Wanke Japan Daga Laifukan Da Ta Tafka Yayin Yakin Duniya Na Biyu
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya soki lamirin kasar Amurka, dangane da yadda ta wanke Japan daga laifukan da ta tafka, yayin yakin duniya na biyu. Jiang Bin, wanda ya yi sukan a Juma’ar nan, ya kira hakan a matsayin mummunan karan-tsaye ga ainihin abun da ya auku a tarihi, kana tozarta damuwar wadanda mamayar dakarun Japan ta cutar. Jami’in ya yi tsokacin ne a matsayin martani ga sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, inda ta ce, bana shekaru 80 ke nan, bayan da Amurka da Japan suka kawo karshen yaki a yankin tekun Pacific. To sai dai kuma a ta bakin Jiang Bin, yayin yakin duniya na biyu, dakarun Japan ‘yan mamaya sun aikata muggan...
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin. Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar daren Alhamis ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje da dama, inda wasu gine-gine suka ruguje ƙarƙashin ruwan. An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil Sakamakon ambaliyar ruwan ya sa mazauna wasu unguwanni da dama suka rasa matsugunansu inda suke hijira ya zuwa gidajen ‘yan uwa da makarantu, inda suke kokawa kan yadda iftala’in ta afku....
“Sama da yara miliyan 10.1 ne ba su kai makaranta, kashi 70 masu zuwa makarantar kuma ba su da dabarun koyo, kuma fiye da kashi 60 na malaman firamare na gwamnati ba su da ilimin dijital,” in ji ta Da take yaba wa gwamnatin Koriya ta Arewa bisa tallafin da ta samu ta hannun hukumar raya kasashe ta KOICA, Garba ta ce wannan hadin gwiwa ya taimaka wa kasar wajen sake tunanin koyo, tare da dakile rarrabuwar kawuna, da bai wa makarantu da malamai kwarin gwiwa domin samar da sauyi mai dorewa. Mataimakin Babban Sakatare na UBEC (Technical), Mista Razak Akinyemi Olajuwon, ya bayyana cewa, wannan shiri ya kara wa malamai kwarin gwiwar yin amfani da su da bunkasa abubuwan...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu saurarozasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au. ////…Madallah, masu sauraro shirimmu nay au zai dubi “ranar 40 na Imam Hussain(a) wanda ya fado a ranakun Alhamis ko jumman da suka gabata, a nan Iran da kuma Iraki, kowa da yadda suke yi lissan watan Safar a wajensu. Ranar 40 na Imam Hussain (a) ita ce ranar 20...
Jami’an tsaro sun kuɓutar da wasu fasinjoji 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Itobe – zuwa Ochadamu – Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu a Jihar Kogi. Fasinjojin da aka kuɓutar an yi garkuwa da su ne a ranar 11 ga watan Agusta a ƙauyen Ugbakpedo da ke kan titin, lokacin da wata mota ta yi wa fasinjojin kwanton ɓauna. Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da Brazil Matsalar ƙofa ta hana fasinjoji 58 hawa jirgin Abuja zuwa Landan Jami’an tsaron da suka haɗa da: ’yan sanda da ’yan banga da mafarautan yankin sun bayyana cewa sun afkawa dajin da ke yankin kafin ceto matafiyan. “A ranar 13 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 4:30 na Asubahi ne...