2025-11-24@14:36:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 505
«Kawu Sumaila»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci. Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin. Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin. Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
Sama da ’yan Najeriya 5,000 da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, na fuskantar barazanar dawo da su gida. Daga cikinsu, kusan 1,500 ne ake tsare da su, wanda hakan na daga cikin matakin da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka na korar baƙin haure da masu neman mafaka ba bisa ƙa’ida ba. Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Alƙaluman da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE), ta fitar a watan Nuwamban 2024, sun nuna cewa akwai mutum miliyan 1.445 baƙin haure da ke zaune a ƙasar ba tare da takardun izini ba, ciki har da mutum 3,690...
Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.
Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar. Labarin ya kara da cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
