Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha
Published: 7th, March 2025 GMT
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci.
An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu.
Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan.
Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba.
Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za ta ci gaba da wakiltar al’ummarta.
A cikin wani rubutu da ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta ce: “Dakatar da ni ba bisa ƙa’ida ba ya saɓa wa adalci da gaskiya.
“Ba zai karɓe min matsayin da ’yan Kogi suka ba ni ba. Zan ci gaba da yi wa mutanena da ƙasata hidima har zuwa 2027—da ma bayan hakan.”
Majalisar ta dakatar da ita na tsawon watanni shida bayan karɓar shawarar kwamitin Ladabtarwa.
Matakin dai ya haifar da zazzafar muhawara s tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke ganin an tauye mata haƙƙinta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi dakatarwa zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda ta yi nasara a kan Arsenal 1-0 a Premier League cikin Agusta da wanda ta ci Burnley 1-0 a cikin watan Satumba a Premier League.
Sababbnin ‘Yanwasan da Liberpool ta saya a kakar banamages Giorgi Mamardashbili daga Balencia Jeremie Frimpong daga Bayern Leberkusen, Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen,
Milos Kerkez daga Bournemouth, Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt, Aledander Isak daga Newcastle United, Armin Pecsi daga Puskas Akademia. Giobanni Leoni daga Parma Freddie Woodman daga Preston North, Will Wright daga Salford.
Wasu daga cikin matsalolin Liberpool A Yanzu
Matsalar masu buga mata tsakiya Liberpool ta samu sauye-sauye da yawa a fannin masu taka mata wasa daga tsakiya, bayan da wasu daga ciki suka bar kungiyar, ya dace a ce ta hadafitattun da za ta fuskanci kakar bana.
Liberpool ta dauki Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen, amma har yanzu dan wasan bai nuna kansa ba, inda yake ta shan suka daga magoya bayan da suke ganin kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.
Raunin ‘yanwasa da ke jinyaRaunin da wasu ‘yanwasan Liberpool suka ji sun taka rawar gani da kungiyar Liberpool ke kasa kokari a kakar nan. Daga ciki mai tsaron baya, Giobanni Leoni ya ji rauni a wasansa na farko a kungiyar, wanda ake cewa yana doguwar jinya. Mai tsaron raga Alisson Becker ya ji rauni a lokacin gasar zakarun turai wanda ake cewar zai yi jinya har karshen watan Oktoba, watakila ya wuce hakan.
Bayan Liberpool na yoyoA kakar bara bayan Liberpool ya yi yoyo, duk da cewar kungiyar ce ta lashe kofin, amma dai an samu matsaloli da yawa a bayan. Kungiyoyi da dama sun amfana da kurakuren Liberpool a bara daga ciki har da Nottingham Forest da Brighton da kuma Brentford.
Wasu lokutan da zarar Liberpool ta kai kora sai kaga wagegen gibi tsakanin masu tsare baya da ‘yan tsakiya. Haka kuma tun kafin fara kakar bana, Liberpool ta buga wasannin atisaye, kuma tun a lokacin gurbin masu tsare baya ya nuna matasalar da kungiyar za ta iya fuskanta da fara
kakar nan.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA