Adadin Wayoyin Salula Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 22.1 A Disamban Bara
Published: 15th, February 2025 GMT
Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53.
Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA