Gwamnan Filato ya kori kwamishinoni 5
Published: 30th, January 2025 GMT
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kori kwamishinoni guda biyar daga muƙamansu.
Wannan ma cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Architect Samuel Jatau, ya fitar da yammacin ranar Alhamis.
Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-RufaiSanarwar ta bayyana cewa sauke kwamishinonin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka, sai dai ba a bayyana dalilin korarsu ba.
Sanarwar ta bayyana cewa korar kwamishinonin ba zai rasa nasaba da gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba, musamman ganin yadda suka kwashe shekara guda wajen gudanar da ayyukansu.
A cewar wata majiya, gaza yin aiki yadda ya kamata ne ya sa aka cire su daga muƙamansu.
Kwamishinonin da aka sauke sun haɗa da: Chrysanthus Dawam, wanda ke riƙe da ma’aikatar kasafin ku6di da tsara tattalin arziƙi, Noel Nkup, wanda ke jagorantar ma’aikatar matasa da wasanni.
Ragowar sun haɗa da Jamila Tukur, Kwamishinar ma’aikatar yawon buɗe ido, Obed Goselle, wanda ke kula da ma’aikatar kimiyya da ƙere-ƙere, da Sule Musa, wanda ke jagorantar ma’aikatar ciniki da masana’antu.
Wannan mataki ya ɗauki hankalin al’umma, musamman mazauna jihar, inda ake ta hasashe kan yadda sauke kwamishinoni guda biyar zai shafi gudanar da ayyukan gwamnatin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Calen Kwamishinoni
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Gwamnan Neja Ya Ki Halartar Bikin Ranar Ma’aikata, Ana Zargin Akwai Takun Saka
Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai taɓa kin halartar bikin Ranar Ma’aikata ba tun bayan da ya zama mataimakin gwamna.
Sabanin shekarar da ta gabata, Kwamred Garba bai bayyana a wannan shekarar ba duk da cewa Gwamna Bago da Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas, Sani Musa, sun halarta, lamarin da ya ƙara zafafa zargin rikici tsakaninsa da gwamnan.
Wasu majiyoyi sun ce yana wajen gari, yayin da wasu ke ganin ya ƙi halartar taron ne da gangan don guje wa ƙara dagula yanayi mai cike da rashin jituwa a siyasar jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp