2025-12-13@13:31:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 938

«rashin Hawan»:

    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da naira biliyan 2 da miliyan 651 domin ayyukan Hajjin 2026, biyo bayan gabatar da bukatar da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya yi. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce za a yi amfani da kudaden ne a bangarorin sufuri da jijigilaAlhazai, jin dadinsu, ayyukan lafiya da kuma shirye-shiryen gudanarwa. Sauran bangarorin...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta ce za ta kashe fiye da naira miliyan dubu 18 domin gudanar da harkokinta a sabuwar shekara. Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Lawal Yunusa Danzomo ne ya bayyana haka lokacin da yake kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa. Dr. Lawan Yunusa Danzomo ya ce zasu mayar da hankali ga aikin gina ajujuwa da gyaran wadanda suka lalace. Za kuma a samar da littatafan darussa da tebura da kujeru domin inganta harkokin koyo da koyarwa. Hakazalika za a  gina bandakuna da samar da ruwan sha da wutar lantarki da tsaro. Danzomo, ya ce aiwatar da haka zai yi matukar tabbatar da...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe naira miliyan dubu 3 domin gudanar da aikace-aikacenta a lokacin aikin Hajjin 2026. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin sabuwar shekara a gaban kwamatin harkokin addini na majalisar dokokin jihar Jigawa. Alhaji Ahmed Umar Labbo yace hukumar za ta sayi motar daukar marasa lafia wato ambulance domin dawainiya da mahajjatan da za su gamu da rashin lafiya a lokacin hajji a kasa mai tsarki. Yana mai bayyana cewar za a yi amfani da wasu daga cikin kudaden wajen kaiwa da komowa yayin aikin hajji. Sai kama masauki ga ma’aikatan hukumar da ma’aikatan...
    Mai horar da Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Liverpool, Arne Slot ya ce zai sanya Mohammed Salah cikin jerin ’yan wasan da za su bugawa Liverpool wasa da Brighton a ranar Asabar. Slot wanda ya samu saɓani da Salah kan ajiye shi a benci a wasanni uku a jere, ya ce yana da yaƙinin cewa, Salah zai ci gaba da bugawa ƙungiyar wasa. 2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya Ya kuma ƙara da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan domin ya ci gaba da taka leda a Anfield. Salah mai shekara 33, baya cikin jerin ‘yan wasan da suka doke Inter Milan a Italiya...
    Shugaban kasar Iran Masud pezeshkiyan a wajen taron zaman  lafiya na turkmanistan ya bayyana cewa siyasar kasashe masu karfin fada aji a yammacin Asiya ne suka bawa isra’ila wata dama ta musamman  ta kai hare-hare gaba gadi, da hakan ya bata damar kai harin soji kan kasashen yankin ciki har da kasar iran ba tare da fuskantar wani sakamako ba. Har ila yau shugaba peszeshkiyan da yake bayani a wajen taron zaman lafiya a garin Ashgabat na kasar Turkministan ya kara da cewa harin da Isra’ila ta kai wa iran a watan yuni da  ya kai ga shahadar mutane da dama da basu san hawa ba balle sauka ya samu kyakkawar tarba ne ma mai makon yin Allah wadai Yace...
    Wata rana, Abu Huraira (RA) yunwa ta kama shi matuka, har yazu wurin mimbarin Annabi SAW da ke cikin masallacin Annabi, sai ya fadi a wurin, duk wadanda suka zo wurin suka ganshi, sai suce Allah Sarki, wane ba shi da lafiya har sai da Annabi ya zo ya ganshi, sai yace masa, Abu Hurairah kana jin yunwa ko? Sai ya amsa da eh. Take Annabi SAW ya ce masa, biyo ni zuwa daki na. Annabi yasa aka kawo masa nono a dan koko kamar yadda aka saba, Abu Hurairah yana jira a ce masa ya sha, sai Annabi SAW ya ce masa ya kira ‘yan uwansa Ahlul suffati, kuma jama’a ne masu yawa, da isowarsu, Annabi SAW ya sa...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026. Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa. Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce hukumar za ta yi amfani da kudaden wajen inganta shirye shiryen koyon karatu da rubutu ga manya maza da mata da na ci gaba da karatu don kammala karatun sakandare da na masu son sake jarrabawar sakandire da koyon karatu ta Rediyo da cibiyoyi daban daban da ke fadin jihar. Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumarsa...
    Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga kasashen duniya wadanda suka rage yawan kudaden da suke bayarwa don tallafawa yan gudun hijira daga kasar Afganisatan a cikin kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jakadan kasar Iran a MDD Amir Saeed Iravani yana fadar haka a jawabinda ya gabatar a taron kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar ta Afganistan a jiya Laraba. Iravani ya kara da cewa a halin yanzun Iran tana ci gaba da daukar bakwncin yan gudun hijiran Afganisatan fiye da miliyon 6 wanda ya hada da da shi da shansu da karatun yayansu da kuma tallafin da gwamnatin kasar take bayarwa na gidajen zamansu da ruwa da wutan lanatarki. Wanda a...
    Hukumar ICPC ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Najeriya na ɗaure a gidan yari. Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi. Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025 Ya ce cin hanci ya yi tasiri sosai a rayuwar ’yan Najeriya, kuma yana haifar da talauci, rikice-rikice, da jinkirta ci gaban ƙasa. Ya ƙara da cewa yawancin dukiyar da wasu ke taƙama da ita a Najeriya ma da alaƙa da...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai kan nasarorin da hukumar ta samu da ƙalubalen da ta fuskanta a shekarar Taron manema labaran wani ɓangare ne na shirye-shiryen hukumar na bikin Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya. Barista Salisu Abdul ya ƙara da cewa, cin hanci babban abin da ke janyo koma-baya ne ga Najeriya a fannoni daban-daban na rayuwar jama’a...
    Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi Allah wadai da sabbin gine-ginen mastugunnan yahudawa yan share wuri zauna guda 764 da isra’ila take ginawa a gabar yammacin kogin jodan , kuma ta bayyana shi a matsayin wani shiri na mayar da yankin ya koma na yahudawa. Wannan matakin yana nuna irin yadda isra’ila ta ke ci gaba da fadada gine-ginenta a yankun da aka dauki dogon lokaci ana takaddama akai, kuma babbar barazana ce ga yankunan dake ciki yankunan falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan, Siyasar ci gaba  da Gine gine na isra’ila ya kara sauri a yan shekarun nan duk da nuna rashin amincewa da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya nuna, kuma ya bukaci ta dakatar da dukkan...
    Daga Aliyu Lawal  Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, wadda ya rabawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja. Alhaji Iliyasu Zakari, wanda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne ginshikin mulkinsa, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, hukumomin tsaro da Gwamna Mohammed Umar Bago bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da sakin dalibai ɗari da aka...
    Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan daliban sun gama jarabawar ƙarshe. Sai dai ba a bayyana sunan dalibin ba. DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka Majiyar ta ce motar ta yi ƙoƙarin wuce wata mota kafin ta kwace ta kuma...
    Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto ganawar da aka yi a tsakanin mataimakan ministocin harkokin waje na kasashen Saudiyya, Walid Khariji, da na China  Miao Deo da kuma ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci. A yayin wannan taron, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana gamsuwarsa da yadda kasar China take daukar matakai na gina kyakkyawar alaka a cikin yannacin Asiya, sannan kuma ya bayyana matsayar Iran na bunkasa alakarta da kasashe makwabta. Ministan harkokin wajen na Iran ya yi Ishara da yadda alaka a tsakanin Tehran da Riaydh take bunkasa a cikin fagage mabanbanta, haka nan kuma yadda suke tuntubar juna akan batutuwan da kasashen biyu suke bai wa muhimmanci. Haka nan kuma ya yi Ishara da rawar...
    Babban magatakardar MDD Antonio Gutress ya yi suka da kakkausar murya akan kutsen da ‘yan sandan Haramtacciyar Isra’ila su ka yi a cikin cibiyar kungiyar Agaji ta “Unrwa” a gabashin birnin Kudus. A bayanin da babban magatakardar MDD ya fitar ya ambaci cewa; Har yanzu ginin na “Unrwa” mallakin Majalisar Dinkin Duniya ne, yana da kariya da bai kamata a taba shi ko shiga cikinsa ba. Haka nan kuma ya yi kira ga “Isra’ilan” da ta yi gaggauta dawo da hurumin ginin na MDD da ba shi kariya,sannan kuma da hana daukar wasu Karin matakai akan gine-ginen MDD. A nashi gefen, shugaban hukumar Agajin ta “Unrwa” Phillipe Lazarani ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Abinda Isra’ilan ta yi,...
    Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar. Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar. Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta Bukatar dai na kunshe ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisa yayin zamanta. Tinubu ya umarci tura sojojin makon da ya gabata domin dakile yunƙurin karɓar mulki ba bisa ka’ida ba a Jamhuriyar Benin da kuma kaucewa rikicewar tsaro a yankin yammacin Afirka....
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi watis da kasashen turai a tattaunawar dawo da zaman lafiya a Ukraine, wanda hakain ya sa kasashen rauni a cikin al-amuran kasar ta Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wani taro mai muhimmanci wanda Volodimir Zelesky shugaban kasar Ukraine ya yi da Firai ministan kasar Burtania Keir Starmer, da Emmanuel Macron na kasar Faransa da kuma Friedrich Merz chancellor na kasar Jamus Zelesky ya kasa fada masu gaskiyar abinda Amurka take shiri na zaman lafiya a kasar ta Ukraine. Labarin ya kara da cewa, kasashen turai sun kashe biliyoyin Euro a yakin Ukraine kuma suna ci gaba da kashewa yakin Ukraine da Rasha kudade, amm Donal Trump na...
    Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baghaie ya yi tir da kashe fararen hula a garin Kalogi dake Jahar Kurdufan na Sudan. Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo karshen abinda yake faruwa a wannan kasar. Kusan mutane 80 ne fararen hula da rabinsu kananan yara ne aka kashe a wasu jerin hare-hare da jiragen sama marasa matuki. Wuraren da aka kai wa harin dai sun hada makarantu na kananan yara da asibitoci. Ana zargin kungiyar nan ta kai daukin gaggawa ( RSF) da kai wannan harin. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to...
    Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu na kasar Rasha, Olga Lyubimova, mataimakin shugaban kasar Rasha, Vladmir Medinsky sai kuma jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Rasha Kazem Jalali. Shugaban Tsangayar FIna-finai ta Eurasia,  Nikita Mikhalov ya jinjina wa Majid Majidi saboda fina-finan da ya yi da hakan ya sa aka ba shi kyauta ta musamma da ita ce lambar yabo ta “ Dimond Butterfly”. A jawabin da ya gabatar, Majid Majidi...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta bayyana cewa za ta mika makamanta ne kawai ” idan Isra’ila ta kawo karshen mamaya, tana mai jaddada cewa ba za a iya kwance damarar makamai ba a cikin yanayin da ake ciki na zaluncin soja da siyasa. Babban jami’i a ofishin siyasa na Hamas kuma babban mai shiga tsakani na kungiyar, Khalil al-Hayya, ne ya bayyana hakan inda yake cewa idan mamayar ta kare, za a sanya wadannan makaman a karkashin ikon gwamnatin kasar Falasdinu.” Ofishinsa ya fayyace cewa kalmar “ƙasa” tana nufin “ƙasar Falasɗinawa mai zaman kanta” mai cikaken iko. “Har yanzu ana ci gaba da tattaunawa game da kwance makamai tsakanin kungiyoyi daban-daban da masu shiga tsakani, kuma yarjejeniyar tana cikin farkon...
    Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu a baya bayan nan suka allawadai da kuma nuna goyon bayansu ga kasar UAE kan mallakar tsibiran Tumb babba da tumb karami da Abu Musa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana cewa bayan duk wani taron da suka gudanar sai kaji cewa wadan nan kasashen Larabawa suna allawadai da Iran kan mallakar wadanan tsibiran, tare da wannan kuma suna kokarin bata dangantaka mai kyau dake tsakanin kasashen yankin da Iran. Yace yana da tabbaci wasu kasashen duniya ne suke ingiza wadan nan kasashen larabawa su rika tada hankali don a...
    Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin ayyuka da sufuri na majalisar dokokin jihar Jigawa. Babban Sakataren ya yi bayanin cewar, za a yi amfani da mafi yawan kudaden ne wajen gudanar da ayyukan hanyoyin mota tsakanin gariruwa da hanyoyin burji da kuma titunan cikin gari. Yana mai cewar, haka kuma za a gudanar da ayyukan hanyoyi a manyan makarantun jihar ciki har Jami’ar Sule Lamido da ke...
    Yanzu ƴan Najeriya za su iya cire naira 100,000 ta na’urar cire kuɗi ta ATM a rana, haka ma abin yake a ɓangaren cire kuɗi ta na’urar POS. A ɓangaren ma’aikatu kuma, za su iya cire kuɗi har naira miliyan biyar ne a duk mako. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabbin tsare-tsaren da Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar bayan garambawul da ya yi kan dokokin cire kuɗi ta na’urar ATM da POS a Najeriya. Bankin ya ce wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2026. A cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare na bankin, Dr Rita Sike ta fitar a ranar Talata 2 ga watan Disamba, ta ce babban bankin...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da su ka rika fitowa a hukumance na fada ganin an daina kawo wa Lebanon hari sannan ayi hakan. Jawabin na Sheikh Na’im ya yi shi ne adaidai lokacin da ake tunawa da kuma girmama malaman addini da su ka yi shahada, yana mai cewa abinda aka yi na tura wakilin Lebanon farar hula a cikin wannan kwamitin tsagaita wutar, tamkar bai wa Isra’ila kyauta ne...
    Microsoft na fuskantar matsin lamba da kuma matakin shari’a saboda samar wa Isra’ila fasahar da ake amfani da ita wajen take hakkin Falasdinawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan. A cikin wata budaddiyar wasika da aka aike wa kamfanin a ranar 2 ga wannan watan, wata kungiyar lauyoyi ta kasa da kasa ta yi gargadin cewa Microsoft da shugabanninta za su iya fuskantar hukunci na shari’a kan taimakawa da kuma tallafawa laifukan da aka aikata wa fararen hula Falasdinawa. Eric Saib, mai kula da harkokin ci gaban kafofin watsa labarun kasa da kasa na Cibiyar Larabawa don Ci gaban Kafafen Yada Labarai, ya  jaddada cewa watannin baya-bayan nan sun nuna karara cewa ana amfani da ayyukan kamfanin wajen take hakkin...
    Hassan Fadlallah wanda dan majalisar kasar Lebanon ne daga kungiyar Hizbullahy a bayyana cewa; gwargwadon yadda ake ja da baya a gaban makiya, suke kara samun karfin gwiwa,don haka da akwai bukatar hadin kai a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi domin fuskantar kalubalen dake gaba.  Shi dai Hassan Fadlalalah yana halartar taron majalisun kasashe  nahiyar Asiya da ake yi a birnin Mashhad na Iran, ya bayyana cewa: Laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi, yana nuni ne da yadda su ka kai koli wajen nuna keta a kan kasashen da suke da cin gashin kai da ‘yanci, da hakan yake a matsayin karya zaman lafiya da sulhu na duniya. Fadlallah ya kuma yi jinjina ga jamhuriyar musulunci ta Iran akan...
    Rahotanni sun bayyana cwa kungiyar Hamas tace za ta mikawa isra’ila sabon samfurin jikin dan Adama da ta samu a arewacin gaza, bayan da isra’ila ta yi ikirarin cewa gawarwakin da kungiyar gwagwarmaya ta basu ba su daga cikin gawarwaki guda biyu da su ke rike da su da har yanzu ba’a dawo da su ba, Kungiyar ta hamas ta bayyana cewa dakarunta da hadin guiwa dakarun kungiyar jihadil Islami suna aiki tare kuma sun gano wani burbushin jikin dan adam da suke ganin yana da alaka da bayahuden da suka kama ne beneath a karkashin burabutsai a yankin beit lahia, Kuma za ta mika samfurin zuwa isra’la ta hannun babban kwamitin kungiyar bada agaji ta red cross ta ksa...
    Kamfanonin jiragen sama kasashen yamma sun bukaci Amurka ta basu izinin ratsawa ko zuwa kasar Iran bayan dakatarwa saboda yakin kwanaki 12 a cikin watan yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wasu majiyoyin gwamnatin Amurka na fadar cewa a halin yanzu babu wata barazana ta sake komawa yaki da kasar Iran. Sannan jita-jitan da wasu kafafen yada labarai suke yadawa dange da sake komawa yaki da kasar Iran ba gaskiya bane. A cikin yan makonnin da suka gabata ne wasu kamfanonin jiragen saman fasinja na kasashen yamma suka farfado da zirga-zirga zuwa kasar Iran bayan bayan fara yakin watan yuni Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments...
    Kasar Masar ta sanar da tattaunawa da Amurka kan batun shirya sake gina zirin Gaza bayan yakin kisan kare dangi na shekaru biyu da Isra’ila ta kaddamar kan yankin. “Yanayin da ke faruwa a Yammacin Kogin Jordan bai yi muni kamar na Gaza ba,” in ji Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Jamus. M. Abdelatty ya sanar da cewa Alkahira tana tattaunawa da Amurka game da wani taron kasa da kasa da nufin sake gina yankin Gaza, bayan yakin. A wani taron manema labarai na hadin gwiwa a Berlin ranar Talata da takwaransa na Jamus, Johann Wadephul, Abdelatty ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa da Washington don...
    Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya  yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai  gabatar da kuduri  don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela. Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana  cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai. A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri...
    Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa. A cewar ofishin, sojojin Isra’ila na kuma tsare da mutane 38 ba bisa ka’ida ba.   ofishin ya ce ya lissafa laifukan tsagaita wuta guda 591, ciki har da harbi kai tsaye kan fararen hula, gidajensu, da tantuna, da kuma bama-bamai da rushe gidaje. Sanarwar ta ce, wadannan laifukan, suna “nufin mamayar na wargaza yarjejeniyar da kuma haifar da mummunan yanayi wanda ke barazana ga...
    Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi. Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da wanna mataki kuma suka bayyana shi a matsayin keta doka , suna ta daga ganyen Ayaba da aciki aka rubuta afuwa, wanda ke kwatanta wani shiri ne na jamhuriyar ayaba. Natanyaho mai shekaru 76 da haihuwa ya nemi afuwar shugaba Herzog a hukumance yana kokarin tsrewa daga gidan kaso idan aka yanke masa hukumci, shekaru da yawa ke nan natanyaho yake neman afuwa kamar yadda...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ya zuwa yanzu ta mayar da sama da naira miliyan 50 ga maniyyatan jihar na shekarar 2026, biyo bayan rage kudin kujerar aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar. Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an mayar da kudaden ga maniyyatan da suka riga suka biya kudin kujerunsu ga hukumar kafin a rage farashin. Ahmed Labbo ya ce NAHCON ta sake fasalin kudin Hajj na Yankin Arewa wanda yanzu ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600 yana mai jaddada cewa mayar da kudin umarni ne...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana halin da Falasdinu ke ciki da rauni mafi muni da aka aikata kan bil adama a doron kasa. A yayin bikin Ranar Falasdinu ta Duniya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sake nanata goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bai wa Falasdinawa, tana mai bayyana halin da suke ciki a matsayin “mafi munin rauni ga lamirin dan adam, Kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya bayyana. Kisan kare dangi, wanda ya fara a watan Oktoba na 2023, ya kashe Falasdinawa sama da 70,000, galibi mata da yara, kuma ya mayar da yankin kufai. Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon watan Oktoba tare da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa...
    An yi gangami a fadin duniya domin nuna goyan baya ga al’ummar Falasdinu a daidai lokacin da aka gudanar da bikin ranar Falasdinu a ranar 29 ga watan Nuwamba da MDD ta kebe. A faransa a gudanar da irin wannan gangamin, inda suka yi Allah wadai da mamayar da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza da Yammacin Kogin Jordan, tare da bayyana goyon bayansu ga adawar Falasdinu. Baya ga Faransa, Birtaniya, Jordan, Kuwait, Slovenia, Sweden, da Morocco an shirya zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da mamayar Isra’ila, ayyukan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan, korarsu, da kuma kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza da kuma cin zarafin fararen hula. Daga cikin taken da aka yi da...
    A ranar nuna goyon baya ga alummar falasdinu shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari ya jinjinawa Alummar falasdinu game da juriya da tsayin Dakar da suka nuna, yace jarumtar da suka nuna ta bude sabon shafin tarihi, don haka gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka yana da muhimmanci sosai. Kasar Pakistan tana da tarihin nuna goyon bayan alummar falasdinu , inda suka nuna goyon bayan alummar falasdinu na hakkin fayyacewa kansu makoma, a kudurin Lahore na shekara ta 1940,don haka wannan kiran na zardari ya kara jaddada tsohon matsayin Pakistan da ya doru kan nuna goyon baya, kwatar yanci da daidaito da kuma adalci. Kiran da zardari yayi na gudanar da bincike kan laifukan yakin Israila...
    Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita wajen kare hakkin falasdinawa da kuma matsa kaimi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa, adaidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da labanon da kuma kasar siriya, Wannan bayanin yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman dar-dar da cin zarafin dan adam ke kara Kamari a yankin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jodan, inda hankalin duniya ya tashi...
    Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila. Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon. A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga...
    Ofishin Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike bayan kisan gillar da sojojin Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a ranar Alhamis a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, bayan sun daga hannayensu suka mika wuya. “Mun firgita da kisan gillar da ‘yan sandan kan iyaka na Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a Jenin, a Yammacin Kogin Jordan ” in ji mai magana da yawun Babban Kwamishinan Jeremy Laurence ga manema labarai. “Babban Kwamishinan (Volker Türk) ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaggawa, kuma ya bukaci a hukunta wadanda suka aikata wadannan laifukan,” Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghai ya jadda game da hakkin kasashe a yammacin asiya na kare martabar su da yankunansu game da wuce gona da irin Isra’ila. Har ila yau yayi suka game da kasa tabuka komai da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan hare haren da isra’ila ke kai wa kan wasu kasashe kamar labanon da siriya wanda...
    A bayanin da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar a yau, ta yi tir da harin da sojojin na “Isra’ila” su ka kai wa kauyen Beit-Jin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13. Bayanin ya kara da cewa; Harin, yana a matsayin keta hurumin shugabancin kasar Syrai da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar ya kuma ce, abinda “Isra’ila” take yi a wannan yankin yana kara yawan zaman dar-dar din da ake ciki a wannan yankin. Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin garin Beit-Jin a gefen birnin Damascuss, inda ta bude wuta akan mutanen kauyen da ya kai ga kashe 13 daga cikinsu da jikkata wasu. Ita...
    Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci. Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye. Daga karshe...
    Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,” “Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis. Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya. Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
    Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.” Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi. Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen...
    Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar. Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan. Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun...
    Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne da babu sulhu a kansu, don haka duk wata tattaunawa da Amurka dole ne ta zama cikin yanci da daidaito, za’a iya tattaunawa amma ta gudana ba tare da nuna fifiko ba. Amurka tana kokarin nuna kanta a matsayin wadda za ta kawo sauyi a kowanne lamari na duniya, amma wannan wani nau’i ne na yaudarar kai, don haka mun yarda da tattaunawa ta gaskiya...
    Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata.  Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar  Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik. A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan...
    Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701. “Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701...
    Adadin Falasdinawan da aka kashe a yakin kisan kare dangi na Isra’ila a Gaza na iya zama mafi girma fiye da yadda aka kiyasta a baya, in ji rahoton jaridar Die Zeit ta Jamus ta mako-mako. A bisa ga kiyasin masu binciken, tsakanin Falasdinawa 99,997 da 125,915 ne aka kashe a Gaza a cikin shekaru biyu na farko na yakin. Masana kimiyya a Cibiyar Max Planck sun tattara bayanai daga majiyoyi da yawa kafin su bayyana kididdigar. Baya ga alkaluman da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta fitar, sun hada wani bincike mai zaman kansa na gida da rahotannin mace-mace da aka buga a shafukan sada zumunta. Duk da haka, asibitoci da yawa sun daina aiki yadda ya kamata a lokacin...
    Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda  shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi. Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa  yana gabatar da jawabi bayan taron shuwagabannin na G20 na kwanaki 2. Ramanposa yace kungiyar G20 ba zata taba manta da sauyin yanayi ba, kuma ba zata kyala sauran kasashen duniyaba ba, kuma kungiyar zata yi kokarin ganin ta daga sauran kasashe raunan a duniya zuwa matsayin da ya dace na tattalin arziki. Kakakin Ramanposa ya ce dukkan kasashen da suka halarci taron sun amince da jawabin bayan taron. Amma shugaban...
    Rahotanni sun bayyana cewa daliban jami’ar St Gorges dake London sun yi zanga-zangar nuna adawa da daukar wani farfesa a fanni tattalin arziki kuma tsohon sojan Amurka aiki a makarantar, inda suka nuna kasancewarsa babban barazana ne ga dalibai musamman ga falsdinawa da kuma masu nuna goyon bayansu. Masu zanga-zangar sun bayyana cewa daukar tsohon sojan isra’ila aiki yana Isar da wani mummunan sako ne ga dalibai kai tsaye musamman wadanda suka shafi rikicin dake faruwa a yankin gaza, kuma matakin da jamiar ta dauka yayi karo da alkawuran da ta dauka na bada ilimi  da kuma kare hakkin dan adam. Akalla dalibai magoya bayan falasdinawa fiye da 100 ne da magoya bayansu suka yi gangami a wajen jami’ar da...
    Sojojin Isra’ila sun kashe wasu yara falasdinawa guda biyu a yankin gaza duk da yajejejeniyar dakatar da bude wuta da a sanya hannu akai, da ta fara aiki a farkon watan oktoba kamar yadda hukumar unicef tayi gargadi akai. Tun da aka rattaba hannun kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a ranar 11 ga watan oktoba, akall yara dubu 67 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren isra’ila a yankin Gaza,  yayin da wasu da dama kuma suka jikkata, wannan shi ne kididdigar da aka fitar dake nuna cewa kullum isra’ila na kashe yara biyu a kullum Kakakin hukumar kula da kana nan yara na majalisar dinkin duniya yayi gargadi game da matsanancin halin dubban daruruwan yara falasdinawa za su shiga...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin  ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya  domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da kara a hukumance ga majalisar dinkin duniya. Wannan bukata ta zo ne adaidai lokacin da sojojin Isra’ila suke kai hare hare kan fararen hula dake jawo asarar rayuka, kuma yake jawo fargaba game da ci gaba da hara-haren israila na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai lamba 1701, Isra’ila ta kai hare hare a lokuta daban daban a kudancin labanon kuma yayi sanadiyar mutuwar...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda Isra’ila ta yi wa kisan gilla. Sojojin Isra’ila sun kuma tabbatar da kai hari kan al-Mawasi a Khan Younis, kudancin Gaza. Isra’ila ta kai hare-hare uku daban-daban a birnin Gaza da ke arewacin yankin Falasdinawa da kuma kudancin Khan Younis, a cewar hukumar Falasdinawa. Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila sun kai hare-hare 393, inda suka kashe akalla Falasdinawa 290 tare da raunata...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne.    Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga wannan daftarin, wanda aka yi shi bisa dalilai na siyasa, son rai, da kuma na neman haddasa barna.” Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a ranar Laraba, a lokacin zaman Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Uku kan kudurin kare hakkin dan adam na Canada kan Iran: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: “Mun yi...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin. Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana...
    Matsayar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta dauka kan tattaunawa da Amurka Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da Amurka. Ya yi nuni da cewa: Babu wata hujja mai ma’ana ta tattaunawa da wani bangare da ke neman ta tsara sharuddansa kan Iran, yana mai cewa wasikar Shugaba Pezeshkian ga Yariman Saudiyya ta kasance ta biyu kawai kuma ba ta da alaƙa da ziyarar da ya kai Amurka. Da yake amsa tambaya a ranar Laraba game da ikirarin Shugaban Amurka na ranar da ta gabata game da tattaunawa da Iran, Baqa’i ya ce, “A halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakanin Iran da...
    Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10. Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52. Da labarin...
    Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta yi suke kudurin Amurka da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da shi na tilasta aikewa da dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza domin tabbatar da zaman lafiya,  ta yi gargadin kada ayi amfani da shi wajen take hakkokin alummar falasdinu na kafa kasarsu mai cin gashin kai A wani bayani daya fitar tun a ranar talata ma’aikatar harkokin wajen iran ta ce  kudurin da aka amince da shi ya manta da ainihin rawar da majalisar dinkin duniya za ta taka da kuma kudurinta na baya da ya shafi yankin falasdinu. Kuduri mai lamba 2803 an amince da shi ne a ranar litinin da ta gabata inda ya bukaci kafa dakarun...
    Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a sansanin yan gudun hijira na Ainul Hilwa dake kusa da Sidon yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, kana sun soki kasar Labanon game da rashin daukar matakin soji da na siyasa akai. Harin an kai shi ne kan sansanin yan gudun hijira mafi girma dake kasar Labanon  yanzu dai dubban gidaje ne suka shiga cikin fargaba saboda da hare haren da isra’ila ke kaiwa ba kakkautawa, Gwamnatin kasar labanon na fuskantar mummunar suka na rashin daukar matakan da suka dace da haka yasa isra’ila ke yawan kai hare-hare a kudancin kasar, yayain da jami’an gwamnatin ke cewa yanzu haka suna shirin mika wani korafi  ga...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin Tsaro ya yi da daftarin kudirin Shugaba Donald Trump na Amurka game da Gaza. Iran ta yi gargadi akan amfani da wannan kuduri a hanyar da za ta keta ko ta wargaza hakkokin al’ummar Falasdinawa ba, musamman ‘yancin cin gashin kai da kuma kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta. A Kudurin da aka amince dashi jiya Litinin, Iran ta jaddada damuwar da wasu membobin...
    Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon. An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA).   Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin, kan abin suka kira, membobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a sansanin. Saidai kungiyar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne. https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
    Tsohon zakaran damben duniya a ajin masu nauyi, Anthony Joshua, zai fafata da tauraron YouTube, Jake Paul, a wani damben ƙwararru da za a yi a watan Disamba mai zuwa. Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36, wanda ya lashe kambun duniya ajin masu nauyi sau biyu, zai kara da Paul a cibiyar Kaseya Center da ke Miami. ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya Ana sa ran za a watsa damben kai tsaye a tashar Netflix a ranar 19 ga Disamba. Wadda za ta kasance fafatawa mai turmi takwas, kowanne na mintuna uku. Joshua, wanda ya yi fafatawa uku a baya da nauyin sama da kilogram 113,...
    Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinu sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun kai hari a sansanin yan gudun hijira dake gabar yammacin kogin Jodan kuma sun kashe wasu matasa guda biyu,da suka hada da jadalla jihar jumaa dan shekara 15 dake sansanin yan gudun hijira na fara’a a yammacin  garin Tubas. Hukumar bada agaji ta yankin falasdinu ta bayyana cewa jami’anta sun kula da wasu mutane biyu da aka jikkata wato wani yaro dan shekara 16 da haihuwa da ya samu rauni a kugunsa, da kuma wani dan shekara 18  da shi ma ya ji rauni a lokacin da suke dauki ba dadi da sojojin Isra’aila a sansanin na fara’a, sai dai an hana ma’aikatansu zuwa daukar mutum...
    Tawagar wasannin Wushu na kasar Iran ta nuna rawar gani sosai a gasar hadin kan kasashen musulmi da ake yi a kasar saudiya  inda ta samu lambobin yabo guda 4 wato Azurfa 1 tagulla 1 da kuma zinariya 2 a ranar karshe na gasa a wannan bangaren. A bangaren mata kuma Sara shafi’I wacce ta fara fitowa a  gasar kasa da kasa ta doke abokiyar hamayyarta daga kasashen kargyzstan da Turikiya ta kai ga wasan karshe , daga nan kuma ta yi galaba a kan abokiyar hammayarta ta kasar masar da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagayen farko don samu lambar zinariya Haka zalika a bangaren mata masu nauyin kilograme 60  Sohaila Mansurian ta...
    Rahotanni sun bayyana cewa bangarorin falasdinawa sun yi watsi da kudurin da aka kaddamar ga kwamitin sulhu na majalsar dinkin duniya na shirin aikewa da sojojin ketare zuwa yankin Gaza sun yi kira ga kasar Aljeriya da sauran mambobin da ba na dindin ba a kwamitin sulhu da su kalubalance shi. Daftarin kudurin an tsara za’a kada kuri’a akan shi  a yau litinin na yiyuwar akewa da dakarun kasashen waje 20,000 domin kulawa da iyakokin Gaza, da kuma bada huro ga yan sandan falasdinu . A Sanarwar hadin guiwar dukkan bangarorin falasdinawan sun yi tir da wannan shiri, inda suka bayyana shi a matsayin wani sabon salo na kara mamaye yankin dama alummarsa,   domin bada halacci ga zaman dakarun kasashen...
    Jakadan kasar Sin a Japan Wu Jianghao, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen Japan Takehiro Funakoshi a jiya Juma’a, inda ya bayyana matukar adawar kasarsa, da korafi a hukumance, dangane da kalamai marasa dacewa da firaministar Japan Sanea Takaichi ta furta dangane da kasar Sin. Jakada Wu, ya ce munanan kalamai masu tayar da husuma na Takaichi, dangane da yankin Taiwan na Sin, wadanda aka jiyota tana yi kwanan baya, a majalissar dokokin kasarta sun sabawa hankali, sun tsallaka jan-layin kasar Sin, kana barazanar nuna karfi ne da neman takalar yaki. Kazalika, firaministar ta Japan ta ki amincewa da kuskurenta, ta ki janye kalaman, ko sassauta mummunan tasirinsu. Don haka matakin nata ya shaida matukar kaucewa gaskiya, da fankamar...
    Shugaban kasar iran Msud pezeshkiyan ya kira prime ministan Iraqi mohammad shia al-sudani ta wayar tarho domin taya shi murnar kammala zaben yan majalisar dokoki da aka yi a kasar cikin gagarumar nasara da kuma kwanciyar hankali da tsaro.  Kasashen iran da Iraqi kasashe ne masu makwabtaka da juna kuma sakamakon  da aka fitar na zaben yan majalisa da aka gudanar zai taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Ana sa bangaren Al-sudani ya jaddada cewa zaben ya nuna irin yadda alummar iraki suka yi riko da demukuradiya, kuma sakamakon zaben zai taimakawa kasar wajen gudanar da ayyukan ci gaba  da gina kasar da gwamnatin tasa a gaba, Shi ma shugaban iran pezeshkiyan  ya jinjina game...
    Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis. WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar. HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci. Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin. Babu rahoton rauni...
    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
    Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na karɓo rancen Naira tiriliyan 1.15 domin cike giɓin kasafin kuɗin 2025. Amincewar ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Lamunin Cikin Gida da na Ƙasashen Waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Manu Haruna, ya gabatar. Matasa 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20 Ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 na Naira tiriliyan 59.99 ya bar giɓin naira tiriliyan 1.15 wanda dole ne a cike ta hanyar nemo rancen a cikin gida. Sanatoci sun amince cewa rancen ya zama dole domin ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati da tabbatar da nasarar kasafin kuɗin 2025,...
    Daga Bashir Meyere Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na neman rancen Naira Tiriliyan 1.15 domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2025. Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da lamuran bashi na cikin gida da na waje. Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, wanda mataimakinsa Sanata Haruna Manu ya wakilta, ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2025 na Naira tiriliyan 59.99 da Majalisar ta amince da shi, ya karu da Naira tiriliyan 5.25 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 54.74 da gwamnatin tarayya ta fara gabatarwa. Ya ce an riga an amince da Naira tiriliyan 12.95 a cikin kasafin, wanda hakan ya...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na ci gaba da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al`ummar jihar. Babban sakataren ma’aikatar lafiya na jihar, Dr. Kabiru Ibrahim ya bada wannan tabbacin a dakin taro na ma’aikatar lafiya ta jihar a Dutse. Yace ayyukan da za’a gudanar a asibitocin sun hada da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ruwan sha. Sauran sun hada da kewaye asibitocin domin inganta yanayin aiki da al’amuran tsaro. Dakta Kabiru Ibrahim ya kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa kokarinta na tallafawa harkokin kiwon lafiya a jihar.  
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
    Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baghaei yayi tir da Amurka game da rashin kyakkawar nufi ko muhimmantar da tattunawa da ake Magana akai, yace sanarwar da shugaban Amurka trump ya fitar a baya bayan nan na amicewa da hannu Amurka wajen kai mata hari ya nuna cewa ta ma shiga cikin harin soji da aka kai mata. Kakakin yayi suka mai tsananin ga kamalan da shugaban Amurka  yayi dake tabbatar da hujjoji dake nuna cewa yana da hannun dumu dumu wajen kai mata harin soji,  wannan yana daya daga cinkin bayyanannun hujoji  dake tabbata da taka rawar Amurka wajen kai mata hari. Haka zalika ya nuna cewa iran ta mikawa kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya wadannan kalaman...
    Pars Today – Jakadan Iran a Rasha ya sanar da cewa Tehran da Moscow sun amince su kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Kazem Jalali, jakadan Iran a Rasha, ya rubuta a ranar Lahadi a dandalin sada zumunta na X cewa an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Rasha don kafa kawancen sufurin jiragen ruwa na farko. Ya kara da cewa wannan yarjejeniya ta samo asali ne daga tarurrukan da aka gudanar a ranakun 6-7 ga Nuwamba a Makhachkala tsakanin shugabannin tashoshin jiragen ruwa da na ruwa, manyan jami’an gwamnati, da daraktocin manyan kamfanonin kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen biyu. A cewar Pars Today, ya kara da cewa a lokacin wannan taron, an amince da tsarin da tsarin hadin...
    Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93. Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya. Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Ana sa ran gudanar da Sallar jana’izarta a safiyar Litinin daina nan da misalin ƙarfe 11, a gidan nata da ke Bambale, Birnin Zariya.
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025
    Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Hajiya Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya, ta jagoranci wani yunƙuri na ganin an tsawaita hutun haihuwa na mata ma’aikata daga watanni uku zuwa shida. Ta jagoranci manyan jami’an lafiya zuwa majalisar dokokin jihar domin neman goyon bayan doka kan wannan shiri. Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu — Tinubu A yayin taron wayar da kai a majalisar, Hajiya Asma’u ta bayyana cewa shayar da jarirai nono har watanni shida yana da matuƙar amfani wajen rage mace-macen jarirai, inganta garkuwar jikinsu, da bunƙasa ƙwaƙwalwarsu. Uwargidan ta roƙi majalisar, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo, da su samar da doka da za ta...
    Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi.   Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.”   Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa. Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse. Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana. Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a...
    Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 ​​a cikin  masai. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a. Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800 Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai. “Hukumar kashe gobara ta...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza. Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bukaci Amurka da Turai su nuna gaskiya idan suna son sake gina aminci da Iran. A wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Shugaba Emmanuel Macron na Faransa,  da takwaransa na Iran Mas’ud Pezeshkian, shugaban na Iran ya ce dole ne turai su mutunta ‘yancin Iran kuma su daina gabtar da bukatu da Iran ba za ta taba amincewa da su ba. Iran ta yi maraba da tattaunawa amma Pezeshkian ya sake nanata cewa, a yanzu ba Iran ce za ta tabbatar da gaskyarta ba, domin ta riga ta yi haka, ya rage kan kasashen turai ne su tabbatar wa duniya cewa da gaske suke yi a cikin abin da suke furtawa. Duk da haka, ya...
      “Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.   Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.   A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.   An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
      Firaministan kasar Georgia Irakli Kobakhidze da firaministan kasar Serbia Duro Macu da shugaban majalisar wakilan kasar Najeriya Tajudeen Abbas, sun halarci taron bude bikin tare da ba da jawabai. Haka kuma wakilai kimanin 1500 daga sassan siyasa, kasuwanci da ilmi na kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 155 su ma sun halarci taron.(Tasallah Yuan)   ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka November 5, 2025 Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika November 4, 2025
    Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi tsokaci game da matakin Amurka na sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake da damuwa a kansu, inda ta jaddada matsayin Sin na matukar goyon bayan gwamnatin Najeriya, wajen jagorantar al’ummarta zuwa turbar neman ci gaba bisa yanayin da kasar ke ciki. A ’yan kwanakin nan ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da sanya Najeriya cikin jerin kasashen da kasarsa ke kara mayar da hankali a kansu, bisa zargin barazanar da ya ce mabiya addinin Kirista na fuskanta a kasar. Trump ya kara da cewa, idan har gwamnatin Najeriyar ta gaza shawo kan kisan Kiristoci, to Amurka za ta hanzarta dakatar da dukkanin tallafin da take baiwa kasar, kana...
    Kasashen Musulmi bakwai, da suka yi taro a Istanbul a ranar Litinin don tattauna makomar Gaza, sun dage kan cewa Falasdinawa ne kawai ke da hakkin mulkin kansu, inda sukayi fatali da sabon tsarin kafa wata wani kwamitin gudanarwa na kasa da kasa a yankin bayan makonni biyu na tsagaita wutar da akayi wacce ke tangal-tangal. “Dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa, kuma Falasdinawa dole ne su tabbatar da tsaron kansu,” in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, ga manema labarai bayan ganawa da takwarorinsa daga Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Jordan, Pakistan, da Indonesia. “Akwai bukatar sake gina Gaza, kuma mutanenta suna bukatar komawa gida inji shi. Ya bayyana fatansa na “sulhu tsakanin Falasdinawa” cikin sauri tsakanin Hamas...
    A Iran dubban ‘yan kasar ne suka taru a Tehran da kuma birane sama da 900 a fadin kasar don tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a 1979, bikin da ake wa lakabi da ‘’Ranar Yaki da Girman Kai ta Duniya’’ A kasar. Dalibai, matasa, malamai, da iyalai ne suka halarci tarurrukan na yau Talata suna masu Allah wadai da ayyukan Amurka da Isra’ila, gami da harin da suka kai wa Iran a watan Yuni. Mahalarta tarukan dauke da tutocin Iran da hotunan wadanda suka yi shahada a hare-haren Isra’ila da Amurka yayin da suke rera taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila.” Jami’ai daga cibiyoyin gwamnati da na soji, iyalan shahidai, da tsoffin sojoji yakin da Irak na...
    A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36.   Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024.   BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon...
    A wata hira da kafar watsa labarai ta iran press ta yi da jagoran harkar musulunci a najeriya shaikh Ibrahim zakzaki yayi tir da ci gaba da kashe mutane da ake yi a kasar sudan inda kungiyar RSF ta kasashe sama da mutane 2000 a garin el-fishar, ya zargi kasar hadaddiyar daular larabawa da ruruta wutar yaki a madadin kasashen masu girma na duniya. Yakin basasar dake ci gaba da gudana a kasar sudan ya dauki mummunan yanayi yayin  da kungiyoyin masu samun goyon bayan kasashen waje ke kara kai hare-hare kan fararen hula da basu ji ba basu gani ba, bayanan na shaikh zakzaki sun kara haskaka yanayin siyasar da ke mayar da kasashen afrika fagen yaki don rarrabasu,...
    Kakakin gwamnatin kasar iran fateme muhajirani ta bayyana cewa ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta tabbar da karbar sakon da ya kunshi batun fara tattaunawar diplomasiya tsakaninsu da Amurka, sai dai za’a bayyana yadda za ta kasance da kuma abubuwa da ta kunsa a nan gaba. Wannana mataki ya nuna cewa ana iya ci gaba da kokarin ganin an koma teburin tattaunawa da ta tsaya cak ,sai dai duka da haka matsayin iran na kin amincewa da tattaunawa kai tsaye yana nan daram kuma yana nuna irin sarkakiyar diplomasiya da kuma bukatar masu shiga tsakani amintattu da za su jagoranci tattaunawar. Sanarwa ta fito ne a daidai lokacin da ake yayata batun ci gaba da tattaunawa ba kai tsaye ba...