2025-09-18@08:32:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 517
«bikin Ranar Hausa ta Duniya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana cewa banda wadanda suka rasa rayukansu mutane 11 ne suka ji rauni. Sannan mutane 3018 suka kauracewa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan ruwan sama na sa’oii masu yawa. Arah yace gidaje 503 ne suka rushe a jihar sannan wasu 265 suka lalace. Banda haka akwai gadoji biyu da hanyoyi biyu wadanda ruwan ya sharesu.
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar cewa a bana za a gabatar wa mahajjata huɗubar Ranar a cikin harsuna uku na Najeriya. Harsunan Najeriya guda uku da za a gabatar da Huɗubar Ranar Arfa da su sun ne Hausa da Fulatanci da kuma Yarbaci. Harsunan huda uku na daga cikin karin harsunan duniya guda 34 da hukumomin Saudiyya suka sanar cewa za a gabatar da Huɗubar a cikinsu.
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta bayyana baƙin ciki da alhini kan mummunan haɗarin mota da ya yi ajalin wasu ‘yan wasa daga jihar Kano, yayin da suke dawowa daga gasar wasanni ta ƙasa da aka kammala a jihar Ogun. Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya fitar da wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar, yana mai miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Kano. Mutane 21 Sun Mutu A Tawagar Ƴan Wasannin Kano A Hatsarin Mota Ahmed Musa Ya Angwance Da Matarsa Ta 4 A Kano “Muna miƙa ta’aziyyar ga iyalan ‘yan wasan, gwamnatin jihar Kano da kuma ɗaukacin ma’abota wasanni a faɗin kasar nan,” in ji sanarwar. Gwamna AbdulRazaq ya...
Aƙalla ‘yan wasa 20 daga tawagar jihar Kano ne suka rasu, yayin da da dama suka jikkata, sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a gadar Dakatsalle, sa’ilin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Kasa da aka kammala kwanan nan a Abeokuta. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Umar Bala Fagge, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa motar da ke ɗauke da ‘yan wasan, wadda ke ɗauke da mutane 30, ta faɗa gadar ta Dakatsalle da ke jihar ta Kano. “Yayin da nake magana da ku yanzu, mun kirga gawarwaki 19,” ya fada cikin tashin hankali. Ado Salisu, tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida da ke kula da lamuran Wasanni ta Najeriya (SWAN), ya ce an kai...
Hukumomi na roƙon mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haɗari tare da haɗa kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa. A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da jaddada cewa al’ummar ƙasar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi ƙasa a gwiwa wajen tallafa masu ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka zalika, ya kara da cewa; gwamnatinsa ta bayar da kimanin Naira biliyan biyu, domin noma hekta 1,000 na gonaki ta hanyar amfani da na’urar noman rani mai amfani da hasken rana a garin Baga. Gwamna Zulum ya ci gaba da cewa, kwanan nan ya tura wata tawagar bincike, don yin bincike tare da gano gaskiya zuwa Gamborun Ngala, sannan kuma tawagar ta tabbatar mana da samun albarkatun ruwan karkashin kasa, wadanda za mu iya amfani da su wajen noman rani ta hanyar ban-ruwa. Kazalika, ya sanar da cewa, an kuma kebe karin wasu Naira biliyan 1.5, domin gudanar da irin wadannan ayyuka a garuruwan Gamborun Ngala da Marte, wadanda a halin yanzu an kusa kammala su baki-daya. Bugu da...
A jawabinsa a wajen rabbata hannun yarjejeniyar, jami’in shirin na jihar ta Gwambe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya danganta wannan aiki a matsayin wani babban ci gaba a jihar. Ya kara da cewa, aikin ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, akwai kuma batun zuba hannun jari ga ci gaban kiwon su kansu dabbobin. A cewarsa, za su tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka da kuma sarrafa nama. Jami’in ya kuma yaba wa gwamnan na Jihar Gombe, Inuwa Yahaya bisa hangen nesansa na kokarin kyautata samar da kayan more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Shi kuwa a nasa jawabin, shugaban gudanarwa na kamfanin Arch. Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci, sannan...
Kwararran likita tiyata, Farfesa Sani Ali Aji ya bayyana cewa kwarrun likitocin tiyata guda 6 ne kacal suka rage a Jihar Kano, wanda ake has ashen tana da al’umma fiye da miliyan 20. Farfesa Sani ya kara da cewa wannan karanci na likitoci ya faru ne sakamakon karancin albashi, karanci kayan aiki na zamani da sauransu, wanda hakan ya sa kwararrun likitoci suka koma kasashen Turai da na Larabawa domin samun alfashi mai tsoka. ‘Yansanda Sun Kama Mutane 41 Da Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kano Ya bayyana cewa maganin wadannan matsaloli shi ne, samar da kayan aiki wadatace da albashi ga ma’aikata mai tsoka da sauransu. Farfesa Sani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu, yana mai jaddada cewa: makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin koyarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ziyarar da ya kai masarautar Oman, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata hira da gidan talabijin na kasar, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma muradun yankin da na kasa da kasa na Iran da Oman, da kuma muhimman batutuwan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin tsaro na cikin matsalolin da suke ci gaba da ci wa ’yan Najeriya da dama tuwo a kwarya, har a wannan lokaci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yake cika shekara biyu a kan mulki. Wasu rahotanni da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar dai sun koka da yadda suke ganin matsalar ta kara kamari a wadannan shekarun. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan matsala ta rashin tsaro. Domin sauke shirin, latsa...
Ambaliyar dai, ta afku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama yana sauka a daren Laraba. Wani mazaunin garin, Mohammed Usman ya ce tuni aka fara tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwan, amma wasu da dama ba a iya ganin su ba musamman a wuraren da gidaje suka nutse. Daraktan yada labarai da ayyuka na musamman a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Dakta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shima a nasa jawabin Janar Martin Luther Agwai cewa ya yi, “Aikin wanzar da zaman lafiya na daya daga cikin muhimman aikin Majalisar Dinkin Duniya da ake iya gani, inda sama da sojoji 87,000 ke sanye da rigar wanzar da zaman lafiya da farar hula suka taka rawa a cikin wasu ayyuka 12, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Lebanon, daga Sudan zuwa Mali. Nijeriya kuma na wakiltar ayyuka guda 8.” Wadannan jajirtattun maza da mata suna taimakawa wajen daidaita yankuna, ba wa fararen hula kariya, tallafawa tsagaita wuta, da sake gina da amana inda ta lalace. Mahimmanci lamari shi ne, tun lokacin da aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta farko a shekara ta 1948,...
A ranar 23 ga Mayu, 2025, jam’iyyar APC ta bayyana Tinubu a hukumance a matsayin dan takararta guda daya tilo don zaben 2027, duk da fuskantar sauyin ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban. Buhari ya jinjina wa kokarin Tinubu wajen rage talauci da hauhawar farashin kayayyaki, yana mai kira ga fannoni masu zaman kansu da daukacin ‘yan ƙasa da su ba da gudunmawarsu. Ya kammala da cewa: “Ina taya Shugaba Tinubu murnar cikar shekaru biyu a ofishi. Allah ya ci gaba da ba ka hikima da tausayi wajen jagoranci. Mu kuma mu rage tsammaninmu daga gwamnati.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
Bayan an bari Amer, ya shiga jirgin, suka kama hanyarsu ta tafiya har suka sauka lafiya wanda hakan ya sa ma’aikatan jirgin suka ɗauki hoton da shi don tarihi, inda a ɗayan ɓangaren mutane da dama ke suffanta lamarin a matsayin hujjar ƙarfin niyya da ikon Allah. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani wasa da masana ke ganin zai matuƙar ƙayatarwa a gasar kofin Unity, yau Laraba za a buga wasa tsakanin manyan ƙasashen Afrika biyu Nijeriya da Ghana, ba kawai wasan ƙwallon ƙafa bane yau, kare mutunci, da ɗaukaka martabar ƙasa da kuma ramuwar gayya duk suka haɗe a wasan da za a buga a filin wasa na Gtech dake birnin Landan. Babu kanwar lasa a cikin ƙasashen biyu in dai batu ake na taka leda a nahiyar Afrika duba da cewa dukkansu sun lashe manyan kofuna na cikin gida kuma sun nuna abinda zasu iya a fagen ƙwallon ƙafa a Duniya, Ghana ta lashe gasar AFCON ta ƙasashen Afrika sau huɗu a tarihi yayin da Nijeriya ta lashe sau...
Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42. Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane 10 a kauyukan Tyolaha, Tse-Ubiam, kamar yadda shugaban karamar hukuma Gwer ta yamma Victor Omnin ya bayyana. Shugaban karamar hukumar ya bayyana wa ‘yan jarida abinda ya faru da cewa; na takaici ne, domin a wannan lokacin da muke Magana ana ci gaba da gano gawawwaki.” Jahar Benue tana tsakiyar kasar Nigeria ne a yankin da ake kira : Middle-Belt”. An kuma dauki shekaru masu...
Ya ce, mahajjaciyar ta kamu da rashin lafiya ne jim kadan bayan kammala Tawafi – zagaye dakin Ka’aba, inda daga nan aka kai ta asibiti a ranar Lahadi, a ranar Litinin kuma Allah ya yi mata cikawa. “Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, an yi jana’izar ta a Makkah a wannan rana, kuma an sanar da danginta a Jattu Uzairue a hukumance,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duk tare da yakin da suke fafatawa a Gaza, dimbin yahudawan sahyoniyya masu bauta sun kutsa cikin masallacin Al-aksa da ke birnin Qudus inda suka gudanar da bukukuwan addinu a jiya Litinin. Shafin yanar Gizo na labarai ‘Arab News’ ya bayyana cewa, bakin na addini, farin ciki ne da kwace gabacin birnin Qudus daga hannun falasdinawa a yakin shekara 1967 tsakanin yahudawan da kuma larabawa. Birnin Qudus ta gabas dai nan ne masallacin Al-aksa yake, kuma nan ne Falasdinawa suke da dama. Yahudawan dai su na ganin dukkan birnin Qudus wanda ya hada har da inda masallacin Al-aksa yake mallakinsu ne kuma su na da shirin rusa masallacin don gina wurin bautansu a inda masallacin yake.
Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama. Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su da masaniyar irin wahalar da iyayensu ke sha wajen ganin sun samar musu da rayuwa mai inganci. Lallai ya kamata ƴan majalisa su matsala ƙaimi a samar da wani yanayi ga yara musamman wajen kare su daga faɗawa ƙangin talla ko bautar aikatau ko kuma zama ƴan jagorar masu bara, hakan kuwa zai faruwa ne idan aka aiwatar da dokar kare ƴancin yara. Daga...
Mutanen garin Rano ake Jihar Kano sun kashe DPO na Babban Ofishin ’Yan Sandan garin tare da banka wa ofishin wuta Fitattun jama’ar gari sun kai wa Hedikwatar ’Yan Sanda da ke Rabin hari ne a sakamakon mutuwar matashin a hannun ’yan sandan. Wasu sanarwar da kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kano, S.P. Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta bayyana cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga mutuwar wani wanda ake zargi da aka tsare. Ya bayyana cewa an kama matashin ne bisa laifin tuka babur ba cikin danganci kuma zargin yana yin haka ne bayan shaye-shayen ƙwayoyi. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su Wani abu ya fashe...
A jiya Asabar ce kasashen Rasha da Ukraine suka yi musayar Fursinoni a tsakanin, karon farko irinsa tun bayan fara yaki a tsakaninsu fiye da shekaru 3 da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai Arabs News ya bayyana cewa an yi musayar furisnonin ne a jiya Asabar kuma ko wace kasa ta sake fursinonin yaki har 390. Labarin ya kara da cewa a dai dai lokacinda aka yi musayar fursinonin sojojin Rasha sun yi loguden wuta a kan birnin Kiyev babban birnin kasar ta Ukraine. Majiyar gwamnatin kasar Ukraine ta bada sanarwan cewa akalla mutane 10 sun ji rauni saboda luguden watan. A makon da ya gabata ne kasashen biyu suka tattauna a tsakaninsu a birnin Istambul na kasar...
Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki. Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da cewa; yadda al’ummar Iran su ka yi gwagwarmayar ‘yanto da garin Khurramshahr, bayan tsawon shekaru 8 na yaki, ya sa Amurka ta fahimci cewa yaki da Iran yana da tsada da kuma hatsari; kuma da ace sun san za su yi nasara ta hanyar karfin soja da ba su zauna akan teburin tattaunawa ba. Janar Sanaei ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su...
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa. Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki na kai farmaki da ba su da matuki, jiragen sama marasa matuki, da kuma albarusai. Haka nan kuma harin ya shafi manyan dakunan ajiye makamai a cikin tashar jiragen ruwan na Odessa. Sanadiyyar wannan harin harshen wuta ya tashi wanda ya dauki lokaci yana ci. A gefe daya an yi musayar fursunoni a tsakanin sojojin Rasha da kuma na Ukiraniya wanda shi ne mafi girma...

Afirka Ta Kudu Ta Zargi Shugaban Kasar Amurka Da Rashin Dalili Akan Zargin Yi Wa Fararen Fatar Kasar Kisan Kiyashi
Ministan ‘yan sandan kasar Afirka ta kudu, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na cewa an yi wa fararen fatar kasar kisan kiyashi a yayin ziyarar da shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya kai. A yayin ganawar da ya yi da shugaban kasar Afirka ta kudu, shugaban kasar Amurka ya kunna wani faifen bidiyo da a ciki aka nuna gicciye a gefen hanya domin tunawa da fararen fata manoma da aka yi wa ksian gilla. Ministan ‘yan sandan kasar ta Afirka ta kuku Senzo Mchunu ta cewa; Wadannan gicciyen ba su nuni da cewa suna akan kabarurruka ne, ko wani wuri na tunawa da matatu, an Sanya su ne a 2020 domin tunawa da dukkanin...
Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
A jawabinsa yayin Kaddamar rabon kayan Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya bayyana cewa “Komawar mu jam’iyyar APC ya nufin kawar da adawa don samar da ci gaba a jihar Kebbi, kuma zamu yi hadin gwiwa da gwamnatin, Gwamna Nasir Idris don amfanin mutanenmu ga irin ayyukan da ya gudanar a dukkan kananan hukumomin 21 na jihar, Wanda shi ne muke kira a ko da yaushe cewa a samar da cigaba ga jama’ar da muke shugabanta,” Inji Sanata Muhammadu Adamu Aliero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Shuwagabannin Amurka da Afirka ta Kudu sun yi arangama kan zargin kisan kare dangi a Afirka ta Kudu Fadar White House ta shaida wata zazzafar musayar wuta tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, wanda ya musanta zargin da ake masa na cewa Pretoria na cin zarafin ‘yan kasar fararen fata. An yi ganawar ne mako guda bayan da Trump ya yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na yin kisan kiyashi ga ‘yan kasarta ‘yan asalin Turai. A yayin tattaunawar da ta samu halartar jami’ai daga bangarorin biyu, shugaban na Amurka ya bukaci ma’aikatansa da su nuna masa faifan bidiyo da ke da alaka da zargin kisan kiyashin, sannan Ramaphosa ya kuma mika...
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni. Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban Kamfanin na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya jaddada bukatar sauya ra’ayi game da lamuni, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauke shi a matsayin wani makami na bunkasa maimakon akasin haka. “CREDICORP, wacce aka kafa a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wata cibiya ce ta kasa da ke aiki don tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar samun lamuni ga duk ‘yan...
Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Sanata Muhammad Adamu Aleiro, ya raba wa al’ummar mazabar sa kayan tallafi da nufin ba su damar dogaro da kai. Kayayyakin sun hada da babura 150 (Keke NAPEP), babura 114, firiza mai zafin rana guda 302, injin nika 750, famfunan ruwa mai amfani da hasken rana 500, injin dinki 800 da kuma buhunan taki 3,400. Da yake jawabi a wajen bikin raba kayayyakin a karamar hukumar Aleiro ta jihar Kebbi, Sanata Adamu Aleiro, ya ce hakan na daga cikin romon dimokuradiyya ga al’ummar mazabarsa kadai, har ma da jihar. Sanata Aleiro, ya lissafo wasu ayyukan da ya aiwatar a matsayin aikin mazabu a kananan hukumomi takwas na mazabarsa da suka hada...
Zanga-zangar ta haifar da cunkoso a kan hanyar yayin da matafiya da suka hada da manyan motoci a kan titin suka tsaya cak na tsawon sa’o’i. Matasan sun kuma koka da yadda har yanzu ba a sako wani jigo a jam’iyyar LP ba, Okasime Olowojoba da aka yi garkuwa da shi kusan wata guda duk da biyan sama da Naira miliyan 5 kudin fansa. Daya daga cikin masu zanga-zangar Paul Lawani ya ce, “Ba za mu iya ci gaba da zama bayi a kasarmu ba, ya kamata gwamnati ta fada mana abin da take yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya. Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa. “Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala. Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin.. ...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin na cewa tattaunawar ta yi amfani.” Rasha a shirye take ta yi aiki tare da Ukraine a kan wata yarjejeniya “game da samar da zaman lafiya a nan gaba.” “Rasha da Ukraine za su fara tattaunawa nan take domin tsagaita bude wuta,” in ji Trump. A cewar wata majiya kusa da tattaunawar da ke gudana, shugaban fadar White House ya tuntubi Volodymyr Zelensky “na ‘yan...
Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da kullum, ciki har da sojoji da ‘yan sanda,” Dbeibah, ya fadi haka ne biyo bayan al’amuran tsaro da suka faru a babban birnin kasar, Tripoli, a ranar litinin bayan kisan Abdul Ghani al-Kikli, wanda aka fi sani da “Ghaniwa,” kwamandan kungiyar da ake kira “Stability Support Apparatus”. Bayanin na Dbeibah ya zo ne a yayin wani taron tsaro da aka gudanar a makon da ya...
Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida kuma wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurika (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa a ranar Lahadi a Maiduguri. Marigayin, wanda ya kuma kasance tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida (Correspondents Chapel) na jihar Borno, ya rasu ne bayan doguwar jinya. Na Dauki Karramawar Jaridar LEADERSHIP Da Matukar Muhimmanci – Gwamna Abba Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa An shirya gudanar da sallar jana’izarsa yau Litinin a ƙofar gidansa da ke unguwar State Low-Cost, Maiduguri. Abokan aiki da ‘yan uwa sun bayyana baƙin ciki game da rasuwar, suna yaba masa da halayensa na kirki da ƙwarewarsa a fannin jarida. Daga kanmu, magana ta...
Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta biya wa maniyyatan jihar 2,047 kuɗin hadaya domin sauƙaƙa musu wajen hidimomin aikin Hajji na shekarar 2025. Amirul Hajji kuma Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake yi wa mahajjatan jirgin farko bankwana kafin tashin zuwa ƙasa mai tsarki. An tafka asara bayan gobara ta ƙone Kwalejin Sheikh Dahiru Bauchi Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Ya ce an biya wa kowane maniyyaci Riyal 600. Mahajjatan da za su fara tafiya sun fito ne daga ƙananan hukumomin kudancin jihar, kuma za su tashi a jirgin kamfanin Max Air. Gwamna Radda ya...
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200. Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki. Ko...
A cewarsa, ba ga wannan akwai shirin kawo sauyi kan manyan kalubale da suka hada da lalata na’urorin wutar lantarki, gudanarwa, matsalolin yankuna da suke janyo cikas ga gudanar da ayyuka. Ya umarci hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) da ta tabbatar kamfanonin rabar da wutar lantarki sun bayar da hadin kan da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun kashe wasu karin mutane 21 wato a safiyar yau Jumma’a, a sansanin yan gudun hijira na Jabaliya. wato sa’o’ii 5 bayan tsakiyar dare a kuma lokacin bada wannan labarin. Labarin ya kara da cewa a wasu hare haren guda biyu a Khan Yunus sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 5 wasu daga cikinsu yara. Gwamnatin Hamas a Gaza, ta bayyana cewa, tun lokacinda sojojin yahudawan suka...
Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...
A yau ne za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya kan yaƙin da ke tsakanin Ukraine da Rasha a birnin Istanbul da ke ƙasar Turkiyya, – amma fadar Kremlin ta bayyana cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin, ba ya cikin jerin jami’an da za su halarci tattaunawar. Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban Amurka Donald Trump shima ba zai halarci taron ba – duk da cewa ya nuna sha’awar halarta jiya idan har Putin zai je. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, zai kuma kasance a babban birnin Turkiyya, Ankara a yau don ganawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan inda ya ce zai je taron tattaunawar da Rasha a Istanbul ne kawai idan Putin ya halarta. Tun daga watan Disamba na...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya wadanda suka hana da nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da...
Ya ce, aikin wannan cibiya ta “Saudi Noor” yana gudana ne a karkashin jagorancin Hadimin wurare biyu masu tsarki; Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mohammed bin Salman. Hakan ya nuna manufar Saudiyya wajen gudanar da ayyukan jinkai a fadin duniya—wanda KSrelief ke tallafawa al’umma—domin inganta kiwon lafiya tare da magance cututtukan dake addabar al’umma masu karamin karfi. Ya ce, “tun lokacin da cibiyar ta fara ayyukan jinkai don yaki da cutar makanta a Nijeriya, cikin watan Oktobar 2019, KSrelief ta gudanar da gwaje-gwajen idanu sama da 218,000, da gudanar da tiyatar idanu sama da 21,000, kuma da bayar da tallafin tabarau sama da 45,000 ga al’umma. “KSrelief ta samu karbuwa a matsayin daya daga...
Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu. Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya ‘Yan ta’addan sun kuma sake kai wani hari da sanyin safiyar Talata a Gajiram...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta ba abu ne da za a amince da shi ba. A yammacin jiya Lahadi ne jami’an gwamnatin kasar Iran suka gudanar da wani taro karkashin jagorancin shugaban kasar Masoud Pezeshkian, inda ya jaddada aniyar gwamnatin kasar na kare nasarorin da Iran ta a fagen ayyukanta na zaman lafiya, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba neman mallakar makamin...
Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar ma’aikatan jiniya ta duniya, Daraktan riƙo na Hukumar ta WHO a Afirka, Chikwe Ihekweazu, ya ce ficewar tasu za ta nakasa harkokin kiwon lafiyar da ake riritawa a nahiyar. Ihekweazu ya cigaba da cewa wannan ɓangare na masu aikin jinyar na da matuƙar muhimmanci ga ɗaukacin al’umma, don haka bashi kulawa, abu ne da ya dace, domin zai ba da gudunmawa ga cigaban ɓangaren lafiya,...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin. Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata...
“Babu shakka cewa INEC na fuskantar matsin lamba mai tsanani, daga mambobin APC da sauran abokan huldarsu wadanda ke tsoron TNN, domin sun shirya yin magudi a zaben 2027 wajen samun nasararsu. “Amma muna kira ga INEC da ka da ta bayar da kai bori ya hau a matsayinta na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tare da kare mutuncnta ta hanyar kin yin abin da ya saba wa doka. “Muna tunatar da hukumar INEC cewa ‘yan Nijeriya suna sa ido sosai kan yadda za ta magance wannan batun na TNN, kuma duk abin da za ta yi zai tantance ko ‘yan Nijeriya za su iya dogaro da ita don shirya sahihin zabbe mai cike da adalci a 2027,”...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco. Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu tana bunkasa inda a shekarar da ta gabata ya kai dalar Amurka biliyon $9. Har’ila yau kowa ya san yadda kasar Masar ta zama sansanin sojojin kasar Rasha a lokacin yakin duniya na biyu. Da kuma yadda kasar ta taimakawa kasar Rasha a yakin da ta fafata da sojojin Nazi na kasar Jamus. Har’ila yau shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya godewa shugaban kasar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani
Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugabannin kasashen Rasha da China Sun yi alkawalin fuskantar siyasar Amurka akansu,a yayin wani taro da su ka yi a birnin Moscow a daidai lokacin bikin tunawa da zagayowar cikar shekaru 80 da samun galaba akan ‘yan Nazi na kasar Jamus. Shugaba Vladmir Putin na Rasha da takwaransa na China Xi Jing Ping sun yi tattaunawa ta fiye da sa’oi 3, sun rattaba hannu akan yarjeniyoyi a tsakaninsu da su ka kunshi kara yawan hannunu jarin da su ka zuba a cikin kasashen junansu, haka nan kuma yin aiki a tsakaninsu domin tabbatar da zaman lafiya a duniya sannan kuma da zurfafa girman alaka a tsakaninsu. Bayanin bayan taron kasashen biyu ya kunshi nuna damuwa akan yadda Amurka take kara...
A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana tare da manema labarai bayan tattaunawa a fadar Kremlin dake birnin Moscow. Inda Xi ya jaddada cewa, a yayin da yanayin kasa da kasa ke fuskantar sauye-sauye da hargitsi, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su yi riko da ruhin kyakkyawar makwaftaka kuma na dindindin, da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da hadin gwiwar samun moriyar juna da nasara tare, da habaka girma, fadi da juriyar dangantakar Sin da Rasha daga dukkan fannoni, da sanya karin kwanciyar hankali ga zaman lafiya da tsaro a duniya, da samar da kuzari ga ci gaban duniya da wadata. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, da sanya kwanciyar hankali da kyakkyawan kuzari a duniyar mai fuskantar sauyi da tashe-tashen hankula. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin ziyarar da ya kai kasar ta Rasha. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba mai dorewa, cikin koshin lafiya kuma a babban mataki, sakamakon...

Aragchi: Muna Bukatar Rage Zaman Daradar Da Kuma Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Pakisatan Da Indiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Indiya da Pakisatan su daure su daina musayar wuta a tsakaninsu saboda tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Alhamis bayan isarsa birnin News Delhi. A jiya larabace sojojin kasar Indiya suka cilla makamai masu linzami kan kasar Pakisatan da kuma yankin Kashamir da ke karkashinn ikon Pakisatn. Inda mutane 31n sauka rasa rayukansu a yayinda wasu 46 suka suka ji Rauni. Shehbaz Sharif firai ministan kasarPakisatan ya bayyana cewa kasar Pakisatan zata rama, kuma ya sha alwashin maida martani kan duk wani jinin mutanen Pakisatan da sojojin Indiya suka zubar....
Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ta tokwaransa na kasar China Xi Jinping sun tattauna a birnin Mosco a yau Alhamis, inda kasashen biyu suka kara dankon zuminci a tsakaninsu, da fatan zasu bukasa harkokin kasuwanci da ci gaba a tsakaninsu nan da shekara ta 2030. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa shugaba Xi Jinping ya je birnin Mosco ne don halattan bikin nasara da kasar Rasha ta samu kan sojojin Nazi a yankin duniya na biyu shekaru 80 da suka gabata. Haduwar shugabannin kasashen biyu yana zuwa ne a dai-dai lojkacinda ake kara tada jijiyoyin wuta tsakanin su da kasashen yamma musamman Amurka. Shuwagabannin biyu sun kara jaddada manufar su da samar da duniya mai kudubobi...
An gabatar da shirin talabijin na kasa da kasa mai taken “Kalaman Magabata dake Jan Hankalin Xi Jinping” jiya Laraba a kasar Rasha, yayin da shugaban Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow domin ziyarar aiki a kasar da kuma halartar bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasarar yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. Sama da mutane 200 daga Sin da Rasha ne suka halarci bikin kaddamar da shirin a Moscow. Da yake bayyana kaddamar da shirin a matsayin irinsa na 4 da aka yi a Rasha, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce shirin na wannan karo ba amfani da dadaddun labarai wajen gabatar da falsafar shugabanci na gari na Xi Jinping da dabi’un dan adam ga duniya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta don yada tsoro, yada labaran karya, domin samun sabbin mabiya. A saboda haka, ya bukaci ‘yan jarida da editoci da su rungumi dabi’ar kishin kasa wajen bayar da rahoto ta hanyar guje wa kanun labarai masu daukar hankali ga farfagandar ta’addanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje. Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba. Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa suna ƙoƙarin rura wutar ƙabilanci ne a Arewacin Nijeriya Najeriya, musamman a daidai lokacin da yankin ke buƙatar haɗin kai domin magance matsalolinsa. Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus To sai dai ƙungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a ƙalubalanci yunƙurin nasu ba, tun da dai ’yan ƙabilar Yarabawa suna da ƙungiyar Afenifere,...
Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, tare da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, kwanciyar hankali da kuma tsari. A yau, yawan fasinjojin da ke kan hanyarsu ta dawowa daga hutun ta jiragen kasa na ci gaba da karuwa, inda a yau ake sa ran za a yi jigilar fasinjoji miliyan 21.1 ta hanyar jirgin kasa na kasar, yayin da ake shirin kara jiragen kasan fasinja 1896 a kan adadin jiragen da...
A jajibirin bikin cika shekaru 80 da samun nasarar babban yakin ceton kasa a kasar Rasha, rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, tare da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin, za su gudanar da bikin tallata fim din “Red Silk” wanda Sinawa da ‘yan Rasha suka shirya a birnin Moscow. A wannan lokacin, mashirya fim din Sinawa da ‘yan Rasha, za su yi musayar ra’ayoyinsu kan yadda suka shirya fim din, tare da sanar da cewa, za a fitar da fim din a kasar Sin a watan Satumba na wannan shekara a lokacin da kasar Sin ke bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin juriya na jama’ar kasar Sin kan zaluncin Jafanawa da...
Gwamnatin HKI ta bada sanarwan halakar sojojinta biyu da kuma jikatan wasu alokacinda suke bincike da kuma kokarin shiga wani rami na karkashin kasa a inda wani bom ya tashi ya kashe su ya kuma raunata wasu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakafen yana labaran yahudawan na fadar haka a safiyar yau kuma wadanda aka rutsa da su sun hada da Captain Noam Ravid, dan shekara 23 a duniya da kuma Staff Sergeant Yaly Seror, dan shekara 20 a duniya. Labarin ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a jiya asabar, sannan wasu sojoji biyu daga rundunar Yahalom sun ji rauni. Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne aka fara yakin tufanul...
Gudu ya zamto wani bangare na rayuwar Antonio Rao tsawo dan kasar Italiya da yake da shekara 80, wanda yanzu yake da shekara 92, inda ba shi da shirin daina shiga gasar tsere. A bana, ya kammala gasar gudun fanfalaƙi na Rome karo na 30 a jere cikin kasa da sa’o’i bakwai. Ɗan shekara 19 da ya ƙirƙiro na’urar gano bam cikin daƙiƙa ɗaya Sojoji sun kama jami’an tsaro da ke haɗa baki da ’yan ta’adda Idan mutum yana bukatar samun karin kuzari to ya shiga gasar gudu, wanda a kwanan nan wani dattijo mai shekara 92 ya kammala gudun fanfalaƙi na Roma na tsawon kilomita 42 a karo na 30 a jere, inda ya kara a kan bara da...
Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya. Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo na 35 a Ilorin. A cewarsa, magance rashin tsaro bai kamata ya zama matsala ga kasar da ta hada karfi da karfe a ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa domin murkushe ‘yan tawaye ba. Ya kuma shawarci gwamnati da kada ta rinka yi masu tada kayar baya ta hanyar yi musu afuwa, ya kara da cewa kada gwamnati ta tausayawa...
A daya bangaren kuma, sashen sufurin jiragen kasa na Sin, ya gudanar da zirga-zirga kusan miliyan 23.12, adadin da ya karu da kaso 11.7 bisa dari, kamar dai yadda alkaluman kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin suka nuna. Har ila yau, idan an kwatanta da tafiye-tafiye masu cin gajeren zango da Sinawa suka fi gudanarwa cikin kwanaki 3 na bikin sharar kaburbura na Qingming, an gudanar da zirga-zirga zuwa wurare masu nisa, tare da lekawa wuraren dake kusa da kan iyakokin kasar a ranakun hutun murnar ranar ‘yan kwadago ta duniya a bana. Wasu alkaluma na daban, daga shafin hidimar tafiye-tafiye na Qunar.com, sun nuna cewa, a ranar Alhamis, adadin wuraren da masu yawon bude ido suka ziyarta...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya. Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar. Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya. Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar. Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana. A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa, duba mara lafiya guda daya tak da ke dauke da cutar Maleriyar da ba ta yi karfi sosai ba a asibitin gwamnati, na lashe kimanin Naira 17,000, tsakanin ganin likita, yin gwaje-gwaje da kuma magunguna. Wadannan kudade sun kai kimanin Naira tiriliyan 1.156 da ake kashewa a kan wannan cuta, amma asalin kudaden sun zarta haka, musamman idan Maleriyar ta yi kamari, za a iya kashe ninki uku ko sama da haka na wannan kudi. Yayin da duniya ke yin wannan biki na ranar Maleriya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nanata cewa, cutar na ci gaba da zama barazana, musamman a yankuna masu fama da zafi, duk da cewa; cuta ce da...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho. A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar. Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu. Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000...
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wayar da kan al’umma kan kare lafiyar ruwa tare da raba riguna a wasu zababbun Jihohin Najeriya. Ministan Tattalin Arzikin Ruwa, Adegboyega Oyetola wanda ya kaddamar da taron a gidan gwamnati, Minna ya ce wannan ra’ayin ya yi daidai da jajircewar Gwamnatin Tarayya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da rayuwar ’yan Najeriya da ke dogaro a kullum kan hanyoyin ruwa na cikin kasa wajen sufuri da kasuwanci. Ya amince da dimbin karfin tattalin arzikin magudanan ruwa a kasar nan da ke fama da tashe-tashen hankula sakamakon yawaitar hadurra na kwale-kwalen da ke bukatar hada kai, da kuma daukar matakai bisa dabaru don haka aka fara raba riguna 3,500 a matakin farko ga...
Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa yawan kudaden da Amurka ta tallafawa Ukraine a yakin dai ya kai dalar Amurka biliyon $175, kuma wannan ita ce hanya tilo wacce Ukraine zata iya biyan wadannan basussuka. Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjeniyar. Wannan na faruwa ne al-hali ana ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine. Wannan yarjeniyar dai ta tabbatarwa...
Gwamnatin Nijeriya ta ayyana gobe Alhamis 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar albarkacin bikin murnar Ranar Ma’aikata ta Duniya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a yammacin wannan Larabar. AU ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Gabon Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu Sanarwar ta ambato ministan yana yaba wa ma’aikatan ƙasar kan sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen gudanar da ayyukansu. Ministan ya kuma yaba musu kan gudunmawar da suke bayarwa wajen ciyar da Nijeriya gaba. Ana dai gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara a sassan duniya.
Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. . Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee. Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu...
Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da motar da ke ɗauke da wadanda abin ya shafa zuwa Gambarou Ngala ta taka abin fashewar. Wata majiya ta ce, “Ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni na farko sun nuna cewa mata huɗu da yara shida da maza 16 ne suka mutu a wannan fashewar.” Ta ci gaba da cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Furunduma, kimanin kilomita...
Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja. Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani. Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da...
Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a tsagaita wutar ne Rasha ke bikin karshen da yakinta da kasar Jamus a shekarun 1941 zuwa 1945, wanda aka fi sani da Yakin Duniya na Biyu a yawancin duniya. A Rasha ana kiran yakin na Duniya na biyu da sunan Babban Yaƙin Ceton Kasa. Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji laifi...
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Ridha Zafarqandi ya tattauna hanyoyin bunkasa aiki tare a fagen kiwon lafiya da mataimakin ministan kiwon lafiya na tarayyar kasar Rasha. Ministan na Iran dai ya yi wannan trattaunar ne a jiya Lahadi inda su ka tabo fagage da dama da su ka yi tarayya akansu a cikin harkar kiwon lafiya. Ministan na Iran ya kuma ce, a baya kasashen biyu sun cimma yarjejeniya wacce a wannan lokacin ake son bunkasa ta. Muhammmad Ridha Ya kuma bayyana yadda kasashen biyu suke da kayan aiki masu yawa a fagagen magance cutuka masu yaduwa da wdanda ba su yaduwa haka nan kuma fagen yin magunguna. Shi kuwa mataimakin ministan kiwon lafiyar na tarayyar...
Kasar Rasha ta fara tura iskar gasa zuwa kasar Iran ta kasar Azarbaijan, wanda daga karshe zai shiga kasuwan ga kasar ta rasah. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar ta na fadar haka a yau Asabar. Labarin ya kara da cewa tun taron kwamin hadin guiwa na kasuwanci da tattalin arziki na kasashen biyu ya gudanar da taronsa na hadin guiwa karo na 18 a birnin Mosco, Rasha ta bada sanarwan fara tura iskar gas zuwa kasar ta Iran ta kasar Azirbajan, wanda kuma hakan zai zama kasuwa ga kasar Rasha amma a kasar Iran.. Kasashen biyu dai sun dade suna kokarin karfafa dangantaka a tsakaninsu, musamman bayan da kasashen yamma suka dora masu takunkuman...
Wannan dai, wani bangare ne na shirin kara habaka hada-hadar kawance tsakanin kasar da China. Kazalika, hakan na daga cikin yunkurin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, na jawo masu zuba jari da yawansa ya kai kimanin dala biliyan daya a fannin habaka samar da Sikari a kasar. Bisa tsarin wannan yarjejeniya, kamfanin zai kafa masana’antar Sikari da kuma gonar Rake da za su fara samar da tan 100,000 na Sikari a duk shekara. Kazalika, Hukumar NSDC ita kuma, za ta taimaka wajen samar da duk takardu da kuma sahalewar gwamnati da ake bukata, domin fara aikin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gargaɗi sabbin masu yin hidimar ƙasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da su guji shiga ƙungiyoyin sirri, da ayyukan siyasa, da kuma nuna kiyayyar addini a duk tsawon lokacin hidimarsu. A cikin jawabin gwamnan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Abdulkadir Mamman Nasir, ya gabatar a yayin shirin gabatar da ƴan hidimar na rukunin A, na tsari na ɗaya, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan horon na farko wani muhimmin mataki ne a tafiyar hidimar ƙasa da mambobin NYSC ke yi. Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga Minista Ya Nemi A Mayar Da NYSC Shekaru 2 Ya kara da cewa suna buƙatar...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar tarho a ranar Lahadi, sakataren yada labarai na ACF na kasa, Farfesa T.A. Muhammad Baba, wanda aka nemi ya yi tsokaci kan kalaman Baba-Ahmed, ya ce a matsayinsa na dattijo, Baba-Ahmed yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa. Mai magana da yawun ACF, duk da haka, kungiyar za ta bincika dukkan batutuwan tare da gabatar da su ga masu jefa kuri’a don su iya yin zabi...

A Karon Farko A Tarihi Adadin Lantarki Da Sin Ke Iya Samarwa Ta Karfin Iska Da Hasken Rana Ya Zarce Wanda Ake Iya Samarwa Ta Amfani Da Dumi
Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba. Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga karfin iska da aka kafa a Sin sun ninka har sau 6, yayin da na samar da lantarki daga karfin rana suka ninka sama da sau 180. Ya zuwa yanzu, sabbin kayayyakin samar da lantarki ta wannan hanya da ake kafawa duk shekara a kasar Sin, sun kai kaso sama da 40 bisa dari kan na daukacin kasashen duniya, adadin da ya yi matukar ba...
Bugu da kari, game da amincewar da gwamnatin shugaba Trump ta yi da aikin hako ma’adinan karkashin teku, Guo Jiakun ya ce ba wata kasa dake da ikon karya dokokin kasa da kasa a wannan fanni, ta yadda za ta iya keta dokokin bincike, da bunkasa ayyukan hako ma’adinan karkashin teku ba bisa ka’ida ba, domin kuwa hakan zai haifar da illa ga moriyar daukacin al’ummun kasa da kasa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An sako limamin cocin Katolika, Rabaran Fada Ibrahim Amos wanda ’yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da rana a Kurmin Risga da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Fada Amos, wanda ke aiki a Cocin St. Gerald Ƙuasi Parish ya dawo gida lafiya lau ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare, kwana ɗaya bayan sace shi. An kama mutum 2 ɗauke da ƙwayar tramadol ta N150m a Kano Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe Bayani kan sakin nasa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Cocin Diocese na Kafanchan, Rabaran Fada, Dakta Jacob Shanet ya fitar, inda ya gode wa Allah tare da nuna godiya ga...
Sashin ma’adinai da ba na karfe ba ta kashe kudin makamashi da kashi 33.7 zuwa naira biliyan 118.49, kuma masana’antar yadi, tufafi da takalmi kudin da ya kashe ya karu sau hudu, wanda ya kai naira biliyan 26.45 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da naira biliyan 6.97 a shekarar 2023. Rahoton ya ce duk da an samu karin wutar lantarki a cikin masana’antu a shekarar 2024, da adadin karin wuta na awa 13.3 a kwace ranar da ya karu daga awa 10.6 a shekarar 2023. Kazalika karin kudin wuta ya karu da kaso 200 ga wadanda suke amfani da rukunin A, don haka kudaden da masana’antun ke kashewa wajen biyan kudin wuta nan ma ya karu sosai....

Amurka Ta Yi Barazana Ga Ukraine A Dai-dai Lokacinda Ta Fitar Da Shirin Zaman Lafiya Da Rasha Na Karshe
Gwamnatin kasar Amurka ta gargadi kasar Ukraine a dai dai lokacinda ta gabatar da shirin zaman lafiya da kasar Rasha na karshe. Shirin da shugaban kasar Donal Trump ya bayyana shi ne karshe dai, ya bukaci gwamnatin shugaba Volodimir Zelesky ta amince da yankin Cremea da kuma sauran yankunan hudu wadanda Rasha ta mamaye da karfi shekaru uku da suka gabata su zama mallakin kasar Rasha har’ abada. Sannan ta amince a daukewa kasar Rasha takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata tun bayan fara yakin. Sannan daga karshe ta amince ba zata shiga kungiyar tsaro ta NATO ba. Shawara bata yi maganar wani abu banada wadannan hudu ba, duk da cewa Ukraine tana da wasu bukatu a yarjeniyar tsagaita...
–Ya Kamata Malamai Su Karfafa Zamantakewa Ta Wayewar Musulunci A Duk Inda Musulmi Suke Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh, ya Shehunmu da sauran daukacin Bayin Allah, muna mika sakon gaisuwa da kuma ziyara ta ‘yan’uwantaka ta Musulunci a dukkanin matakai da Annabi (SAW) ya zo mana da shi na Musulunci da Imani da kuma Ihsani. Bayan haka, muna godiya da irin bayanin da aka yi mana a karatunka na Tafsiri na rana ta 11 a game da muhimmancin karfafa zamantakewa ta wayewar Musulunci a tsakanin Musulmi a duk inda suke. Tabbas, lokaci ya yi da masu wa’azin Musulunci ya kamata su daina kafa hujjar yaki da ayoyin Surar Bara’a a wuraren da ba su dace ba, domin akwai...
Rashford ya yi watsi da yiwuwar komawa Landan, inda yace ba lallai bane ya cigaba da wasa a karkashin Ruben, inda yake da burin zama a kungiyar da zata buga gasar Zakarun Turai a badi, majiyoyi na kusa da dan wasan sun tabbatar Rashford har yanzu bai tattauna kan makomarsa ba kuma baya shirin yin hakan har zuwa tsakiyar watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
Hukumar lafiya ta duniya (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci. Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan. Haka nan kuma ta yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar. A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar...
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci. Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan