Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
Published: 15th, September 2025 GMT
Gwamnan Jihar Neja, Umar Mohammed Bago, ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya bayan da ya sake jaddada cewa duk wani malamin addini da ke shirin yin wa’azi dole ne ya gabatar da rubutaccen wa’azinsa domin tantancewa kafin ya gabatar da shi ga jama’a.
A cewar gwamnatin jihar, wannan mataki na da nufin daƙile kalaman ƙiyayya, tsattsauran ra’ayi da barazanar tsaro da ke tasowa daga wa’azin da ba a tantance ba.
Da yake jawabi a shirin Politics on Sunday na gidan talabijin na TVC, Gwamna Bago ya musanta zargin cewa dokar ta hana wa’azi gaba ɗaya, yana mai cewa matakin na da nufin tabbatar da zaman lafiya da hana tayar da fitina.
Gwamnan ya ce:
“Ban hana wa’azi ba. Duk wanda zai yi wa’azi a ranar Juma’a, ya kawo rubutaccen wa’azinsa domin tantancewa. Wannan ba sabon abu ba ne. A Saudiyya ma haka ake yi. Ba za a bar malami ya yi wa’azi da ke cin mutuncin jama’a ko gwamnati ba, yana mai cewa ba da damar yin wa’azi ba yana nufin a yi amfani da damar wajen tayar da hankali.”
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro kamar DSS, ’yan Sanda, Sibil Difens da sojoji domin sa ido kan wa’azin da ka iya tayar da hankali.
Matakin ya fara jawo ce-ce-ku-ce ne bayan da Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Addini ta Jihar Neja, Umar Farooq, ya sanar da cewa duk wani malami dole ne ya nemi lasisin wa’azi cikin watanni biyu ko ya fuskanci hukunci.
“Abin da ake bukata shi ne su zo ofishinmu, su cike fom, sannan su fuskanci kwamitin tantancewa kafin su fara wa’azi,” in ji Farooq.
Wannan sanarwa ta haifar da martani iri-iri daga shugabannin addini da ƙungiyoyin fararen hula, inda da dama ke nuna fargabar cewa dokar za ta iya zama hanyar danne ’yancin faɗin albarkacin baki.
Babban Limamin Jami’ar Fasaha ta Minna, Sheikh Bashir Yankuzo, ya bayyana ra’ayi mai sassauci, yana mai cewa duk da cewa gwamnati na da haƙƙin daƙile kalaman ƙiyayya, ba za ta hana wa’azi na gaskiya ba.
Sheikh Yankuzo ya ce:
“Wa’azi umarni ne daga Allah, kuma gwamnati ba ta biya kowa albashi don yin wa’azi. Amma idan akwai masu tayar da hankali ko amfani da kalaman batanci, to gwamnati na da ikon dakile hakan don tabbatar da zaman lafiya.”
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja ta bakin Sakataren ta, Raphael Opawoye, ta ce ba a sanar da su hukuncin ba.
“CAN ba ta da masaniya kan dokar. Za mu fitar da sanarwa idan an sanar da mu a hukumance,” in ji Opawoye.
Sai dai wani malamin addinin Musulunci, Ustaz Uthman Siraja, ya soki dokar kwata-kwata, yana mai cewa ta take ‘yancin addini da ibada.
Ya bayyana cewa:
“Hana wa’azi cin zarafin ’yancin addini ne. Mafi alheri shi ne gwamnati ta gayyato malamin da ya tayar da hankali ta hukunta shi, ba wai a tantance wa’azi gaba ɗaya ba.”
Gwamna Bago ya kare dokar da cewa matakin tsaro ne na rigakafi, musamman ganin tarihin jihar na fuskantar hare-haren ’yan bindiga, rikicin addini da tsattsauran ra’ayi.
Yayin da wa’adin cike fom da samun lasisi ke ƙara matsowa, idanu sun karkata zuwa Jihar Neja don ganin ko dokar za ta kawo zaman lafiya ko kuma ta ƙara dagula al’amura tsakanin gwamnati da al’ummar addini.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Wa azi tayar da hankali yana mai cewa hana wa azi
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria