HausaTv:
2025-11-02@11:21:40 GMT

Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta

Published: 14th, September 2025 GMT

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da sanarwar ta G7, tana mai cewa ba ta da tushe balle makama

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah-wadai da zarge-zargen da mambobin kungiyar G7 da kawayenta suka yi dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, tana mai kallon hakan ba gaskiya ba ne.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ta bayyana zargin da ke kunshe a cikin sanarwar hadin gwiwa na kasashen G7 da kawayenta dangane da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cewa ba gaskiya ba ne.

Sanarwar ta kara da cewa: Yin zargin karya kan wadanda ke da alhakin kare tsaron kasar Iran wani lamari ne karara na murguda gaskiya da kuma hasashe na yaudara da masu fitar da wadannan bayanai suka yi, wadanda kokari ne na tada zaune tsaye a yankuna daban-daban na duniya, musamman a yammacin Asiya, sun taimaka wajen yaduwar hargitsi da rashin tsaro.

Ko shakka babu, dole ne Amurka da sauran kasashen duniya da suke kawance da ita su yi taka-tsan-tsan wajen daukar matakan da basu dace ba wadanda suke barazana ga tsaron yankin da na duniya, musamman irin hadin kai da shiga al’amuran take manya-manya da hakkin dokokin kasa da kasa, da suka hada da dokokin kare hakkin bil adama da na kare hakkin bil adama, da gwamnatin sahayoniyya take tafkawa a Falasdinu da ta mamaye a Palastinu, ballantana goyon bayansu ga gogaggun ‘yan ta’adda.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu   September 14, 2025 Tsananin Masifar Da Falasdinawa Ke Ciki A Gaza Saboda Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 14, 2025 Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba September 14, 2025 Tsohon Kwamandan IRGC Ya Ce Boma-Boman HKI Na Zuwa Kanku Idan Kunki Samar da Kawance September 14, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Rusa Dogayen Gine-Gine A Gaza A September 14, 2025 Dubban Mutanen New Zealanda Sun Fito Jerin Gwanon Goyon Bayan Falasdinawa September 14, 2025 Velayati: Taron Malaman Yahudu A Azerbaijan Tsokana Ce Ga Musulmi Shia September 14, 2025 Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Wajen Kawo Karshen Rashin Hankalin Isra’ila. September 13, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Masu Neman Agaji 4 Tare Da Jikkata Da Dama A Gaza. September 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Musulunci ta Iran

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar  suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.

Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.

Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta
  • Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher